Benue: Ɗan Majalisar da Aka Dakatar Ranar Juma'a Ya Zama Sabon Shugaban Majalisa
- Majalisar dokokin Benue ta zaɓi Alfred Emberger a matsayin sabon shugaban majalisar bayan murabus ɗin tsohon Aondona Dajoh
- Emberger na daya daga cikin ‘yan majalisa huɗu da aka dakatar da su a ranar Juma'a bisa zargin yunkurin tsige shugaban majalisa
- A wani taron gaggawa da majalisar ta yi ranar Lahadi, an zabi Emberger tare da rantsar da shi ba tare da wata hamayya a zauren ba
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Benue - A ranar Lahadi, 24 ga Agusta, 2025, majalisar dokokin Benue ta zaɓi Alfred Emberger a matsayin sabon kakakin majalisa.
Nadin Alfred Emberger ya zo ne jim kaɗan bayan murabus ɗin tsohon kakakin majalisar, Aondona Dajoh.

Source: Facebook
An janye dakatarwar 'yan majalisar Benue
Sabon kakakin majalisar na daga cikin ‘yan majalisa huɗu da aka dakatar da su a ranar Juma’ar da ta gabata, bayan ƙoƙarinsu na tsige tsohon kakaki, Aondona Dajoh.

Kara karanta wannan
Bayan zargin gwamna da ƙoƙarin tsige shi, kakakin majalisa ya yi murabus da kansa
A zaman gaggawa da aka gudanar a ranar Lahadi karkashin jagorancin mataimakiyar shugabar majalisa, Lami Danaldi-Ogenyi, majalisar ta cimma matsayar janye dakatarwar da aka yi wa waɗannan 'yan majalisa huɗu.
Shugaban masu rinjaye na majalisar, Saater Tiseer, ya gabatar da kudirin a janye dakatarwar, inda Samuel Jiji na mazabar Logo ya mara masa baya.
Mataimakiyar kakakin majalisar ta ce:
“Biyo bayan kudirin da shugaban masu rinjaye na majalisa ya gabatar da kuma amincewar sauran mambobi, majalisa ta amince da janye dakatarwar da aka yi wa mambobin majalisar huɗu.”
An zabi sabon shugaban majalisar Benue
Bayan janye dakatarwar, sai aka shigar da mambobin huɗu cikin zauren majalisa, aka sanar da takarar sabon shugaban majalisa.
Douglas Akyaa na mazabar Makurdi ta Kudu ya gabatar da kudiri tare da tsaida Emberger a matsayin sabon kakaki, inda Abu Umoru na mazabar Apa ya mara masa baya.
Babu wani ɗan takara daban da ya nemi kujerar ko kuma jayayya kan zaben Emberger, wanda ya sa nan take sabon kakakin ya karbi rantsuwar kama aiki daga sakataren majalisa, John Hwande.

Kara karanta wannan
'Yan Majalisa da Sanatoci 50 da suka dumama kujera, ba su da gudumuwa a shekara 1

Source: Twitter
Jawabin sabon shugaban majalisar Benue
A jawabinsa na karɓar rantsuwar aiki, sabon kakakin majalisar Benue ya yaba wa tsohon shugaban majalisar bisa jajircewarsa wajen cigaban majalisa da al’ummar jihar.
Emberger ya ƙara da cewa:
“Zan tabbatar da jagoranci na adalci, haɗin kai da girmama ra’ayoyi daban-daban. Wannan majalisa a ƙarƙashina za ta yi aiki da gwamnati da fannin shari'a cikin haɗin kai, tare da kiyaye ‘yancin kai bisa tsarin doka.”
Benue: Shugaban majalisa ya yi murabus
A wani labarin, mun ruwaito cewa, shugaban majalisar jihar Benue, Aondona Dajoh, ya ajiye mukaminsa a ranar Lahadi 24 ga watan Agustan 2026.
Hon. Aondona Dajoh ya tabbatar da murabus din nasa inda ya ce ya yi hakan ne domin mafita ga ci gaban Benue da kuma majalisar dokokin jihar.
Dama dai majalisar ta dakatar da wasu ‘yan majalisa hudu saboda yunkurin tsige shi, amma Gwamna Hyacinth Alia ya musanta hannu a lamarin.
Asali: Legit.ng