'Ka Dawo Gida da Gaggawa: An Buƙaci Tinubu Ya Sanya Dokar Ta Baci a Jihohin Arewa 2
- Jam’iyyar ADC ta yi kira ga Shugaba Bola Tinubu ya soke tafiyarsa kasashen waje ya kuma ayyana dokar ta-baci
- ADC ta ce kashe-kashen al’umma a Malumfashi a Katsina da hare-haren Zamfara na nuni da rushewar tsarin tsaron Najeriya baki ɗaya
- Jam’iyyar ta kuma caccaki shugabannin PDP da suka gudanar da taron siyasa a Zamfara jim kaɗan bayan harin, tana kiran hakan rashin tausayi
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Jam’iyyar ADC mai adawa a Najeriya ta la’anci kisan da aka yi a garin Malumfashi da ke jihar Katsina, inda aka kashe fiye da mutane 30 a masallaci.
Rahoton baya-bayan nan ya nuna cewa sama da mutane 144 aka sace, 24 aka kashe, da 16 suka jikkata a sassan Zamfara a farkon watan.

Source: Twitter
ADC ta koka kan karuwar rashin tsaro
A cikin sanarwar da Bolaji Abdullahi, kakakin jam’iyyar ya sa hannu, ADC ta bukaci Tinubu ya dakatar da tafiye-tafiyensa a ƙasashen waje ya ayyana dokar ta-baci, cewar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
ADC ta bayyana yawaitar hare-haren a matsayin shaida cewa tsarin tsaron Najeriya ya rushe, tana cewa “rayuka fiye da 140” sun salwanta a watanni biyu.
Jam’iyyar ta kuma soki gwamnoni na jam’iyyar PDP da suka shirya taron siyasa a jihar Zamfara bayan kisan, tana cewa hakan rashin tausayi ne ga mutanen da abin ya shafa.
Sanarwar ta ce:
“Kashe-kashen da ke Katsina da Zamfara hujja ce babba ta rushewar tsarin tsaro a Najeriya gaba ɗaya.
“Gazawar Shugaba Tinubu wajen yin jawabi ga ƙasa ko ta’aziyya ga iyalan mamata ba abin amicewa ba ne.”

Source: Twitter
ADC ta bukaci Tinubu ya daow gida Najeriya
ADC ta ce abin takaici ne ganin shugaban kasa ya ci gaba da yawo a duniya yana daukar hoto, alhalin jama’a suna mutuwa a gida.
“Diplomasiyyar kasashen waje ba ta da ma’ana idan tsaron cikin gida ba a iya tabbatar da shi ga ’yan ƙasa,”
- Cewar sanarwar
ADC ta kara da caccakar Tinubu kan rashin yin jawabi na kai tsaye ga iyalan mamatan ko kuma tabbatar da tsaron wadanda suka rage a yankunan.
Jam’iyyar ta kuma yi kira ga gwamnati ta sake duba tsarin tsaron ƙasar nan, tana cewa shawarar CDS ga jama’a ya nuna tsanani, The Guardian ta ruwaito.
Sanarwar ta kara da cewa:
“Kiran CDS da ’yan ƙasa su koya dabarun kare kai, alama ce gaskiya da bukatar sake tunanin tsarin tsaron cikin gida.”
Zamfara: An roki Tinubu ya sanya dokar ta-baci
Kun ji cewa wata ƙungiyar Arewa ta bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya ayyana dokar ta-baci a jihar Zamfara saboda tabarbarewar tsaro.
Kungiyar NCAJ ta zargi gwamnatin Zamfara da yin salon mulkin 'kama karya' yayin da ta ce jihar ba ta samun wani ci gaba a yanzu.
NCAJ ta ce garuruwa sun koma biyan haraji ga ‘yan bindiga, jami’an gwamnatin jihar na amfana da haramtacciyar hakar ma’adinai.
Asali: Legit.ng

