Duniyar Musulunci Ta Yi Rashi: Babban Malamin Addini Ya Rasu a Gombe

Duniyar Musulunci Ta Yi Rashi: Babban Malamin Addini Ya Rasu a Gombe

  • Duniyar Musulunci ta yi babban rashi na fitaccen malamin addini wanda ya rasu a yau Lahadi a jihar Gombe
  • Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya bayyana jimami kan rasuwar babban malami Sheikh Umar Bojude, babban limamin masallacin AG Dalibi a Gombe
  • Ya ce Sheikh Bojude ya rayu cikin ibada da jagoranci na addini, inda ya zama ginshiƙi ga darikar Tijjaniyya da al’umma baki ɗaya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gombe - Ana cikin jimami bayan sanar da rasuwar fitaccen limamin masallacin Juma'a a Gombe a yau Lahadi.

Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya yi jimami kan rasuwar Sheikh Umar Bojude.

Malamin musulunci ya rasu a Gombe
Gwamna Inuwa Yahaya ya yi jimamin mutuwar shehi a Gombe. Hoto: Isma'ila Uba Misilli.
Source: Facebook

Hakan na cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran gwamnan jihar Gombe, Isma'ila Uba Misilli ya tabbatar a Facebook.

An yi rashin shugaban Izala a Gombe

Kara karanta wannan

Gwamnatin Katsina ta dauki matakin fuskantar matsalar 'yan bindiga

Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan sanar da rasuwar daya daga cikin shugabannin Izalah a unguwar Jekadafari a jihar Gombe.

Rahotanni sun nuna cewa malamin Izala, Malam Shu’aibu A Ahmad ya rasu a Gombe bayan doguwar jinya da ya yi a asibiti.

Bayanan sun nuna cewa marigayin yana daga cikin fitattun malaman Izala da suka yi karatu a kasashen waje a jihar Gombe.

Kungiyar Izala ta tabbatar da ranar Litinin, 28 ga Yuli, 2025 za a yi jana’izarsa da misalin karfe 5:00 na yamma a unguwar Jekadafari.

Babban limamin masallacin Juma'a ya rasu

Sanarwar da Gwamna ya fitar ta ce jihar ta yi rashin babban malamin addini kuma limamin masallacin AG Dalibi da ke Gombe.

A cikin sakon ta’aziyyarsa, gwamnan ya bayyana Sheikh Umar Bojude a matsayin fitaccen malami kuma ginshiƙi na darikar Tijjaniyya.

Gwamnan ya ce marigayin ya sadaukar da rayuwarsa gaba ɗaya wajen ibada da jagoranci wanda ya kara nuna irin jajircewar da ya yi.

Gwamna Inuwa ya yi jimamin rasuwar malami a Gombe
Gwamna Inuwa Yahaya yayin wani taro a jihar Gombe. Hoto: Muhammadu Inuwa Yahaya.
Source: UGC

Gombe: Gwamna ya yaba da gudunmawars marigayin

Inuwa ya ce marigayin ya bar gagarumin tasiri a zukatan jama’arsa, al’ummar Jankai da kuma jihar gaba ɗaya, inda za a yi kewar koyarwarsa.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya kadu da Allah ya yiwa tsohon gwamna kuma jigon APC rasuwa a Abuja

Gwamna Inuwa ya mika ta’aziyya ga iyalan Sheikh Bojude, mabiya Fiyanul Islam, darikar Tijjaniyya da musulmi a fadin jihar da wajen ta.

Ya yi addu’ar Allah Madaukaki ya saukar da rahamarsa marar iyaka a kan Sheikh Umar Bojude, ya gafarta masa, ya kuma ba shi Aljannatul Firdaus.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa an gudanar da jana'izar marigayin da misalin ƙarfe 5:00 na yammacin yau Lahadi 24 ga watan Agustan 2025.

Legit Hausa ta yi magana da masoyin marigayin

Musa Muhammad Ibrahim ya ce tabbas an yi babban rashin wanda cike gurbinsa zai yi wahala.

Ya ce:

"Gaskiya marigayin mutum ne mai hakuri da kuma haba-haba da mutane, ya ba da gudunmawa sosai ga addinin Musulunci."

Daga karshe ya yi addu'ar Allah ya jikansa ya kuma gafarta masa, ya saka masa da gidan aljanna firdausi.

Gwamna ya yi jimamin mutuwar hadiminsa

Mun ba ku labarin cewa Gwamna Inuwa Yahaya na Gombe ya bayyana jimaminsa kan rasuwar hadiminsa na musamman a jihar da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.

Marigayi Mamman Alkali ya rasu a ranar Laraba 23 ga watan Yulin 2025 a Gombe bayan gajeriyar rashin lafiya da ya sha fama da ita.

Inuwa ya ce Mamman Alkali mutum ne mai amana, hazikin dan siyasa kuma dan dimokuradiyya na gaskiya da ya sadaukar da kansa wajen hidimar jama’a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.