'Yan Sanda Sun Ritsa Masu Garkuwa da Mutanen cikin Daji, an Tura Miyagu Barzahu

'Yan Sanda Sun Ritsa Masu Garkuwa da Mutanen cikin Daji, an Tura Miyagu Barzahu

  • Jami'an rundunar 'yan sandan jihar Kebbi sun samu nasara kan masu garkuwa da mutane bayan sun gwabza fada
  • Lamarin ya auku ne bayan an samu bayanan sirri kan shirin masu garkuwa da mutanen na tare matafiya a karamar hukumar Shanga
  • Jami'an 'yan sandan sun yi gaggawar kai dauki, inda suka kashe wasu daga cikin miyagun tare da kwato bindiga

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kebbi - Rundunar 'yan sandan jihar Kebbi ta bayyana cewa jami’anta sun kashe wasu mutane uku da ake zargin masu garkuwa da mutane ne.

Jami'an 'yan sandan sun kashe masu garkuwa da mutanen ne a karamar hukumar Shanga da safiyar ranar Lahadi, 24 ga watan Agustan 2025.

'Yan sanda sun kashe masu garkuwa da mutane a Kebbi
Hoton jami'an 'yan sanda a bakin aiki Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Jaridar The Punch ta rahoto cewa hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi, CSP Nafi’u Abubakar, ya sanyawa hannu.

Kara karanta wannan

Kwale kwale ya kife da mutanen da ke tserewa harin 'yan bindiga a Sokoto

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan sanda sun fafata da masu garkuwa da mutane

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 2:30 na dare, bayan samun bayanan sirri kan hango wata tawagar masu garkuwa da mutane a cikin daji da ke kan hanyar Tungargiwa–Saminaka, inda ake zargin suna shirin kai hari ga matafiya.

Kakakin 'yan sandan ya bayyana cewa DPO na Shanga ya hanzarta tattara jami’an ‘yan sanda tare da ‘yan sa-kai domin kai dauki wurin.

"Da isarsu, tawagar jami’an tsaro ta yi artabu mai tsanani da miyagun. A karshe, an kashe masu garkuwa da mutane guda uku, sannan aka kwato bindigar AK-47 guda ɗaya, jigida ɗaya da harsasai guda bakwai."
"Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kebbi, CP Bello M. Sani, ya jinjinawa DPO da tawagarsa saboda yadda suka nuna jarumta da gaggawa wajen kai farmaki."
"Ya bayyana nasarar a matsayin hujja ta jajircewar rundunar wajen kawar da miyagun laifuffuka daga jihar."

Kara karanta wannan

Sojojin sama sun yi ruwan wuta kan 'yan bindigan da suka kashe masallata a Katsina

"Tsaurara sintiri a Shanga da kewaye tuni ya fara samar da sakamako mai kyau. Wannan nasara ta kuma tabbatar da irin abin da za a iya cimmawa idan jami’an tsaro da al’umma suka haɗa hannu."

- CSP Nafi'u Abubakar

'Yan sanda sun kashe masu garkuwa da mutane
Taswirar jihar Kebbi, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Kwamishina ya yabawa jama'a kan hadin kai

Ya kara gode wa mazauna yankin saboda yadda suke gaggauta ba da bayanan sirri ga jami’an tsaro, yana mai jaddada cewa irin wannan haɗin kai shi ne ginshikin hana aikata laifuffuka, rahoton Vanguard ya tabbatar.

Kwamishinan ya sake yin kira ga jama’a da su kasance masu lura da duk wani motsi na zargi, tare da sanar da hukumomin tsaro mafi kusa.

Sojoji sun kashe 'yan ta'addan Lakurawa

A wani labarin kuma, kun ji cew a dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar kashe 'yan ta'addan Lakurawa a jihar Sokoto.

Dakarun sojojin sun hallaka 'yan ta'addan ne bayan sun yi musu kwanton bauna lokacin da 'yan ta'addan suka je sayo kayan abinci.

Sojojin sun kashe 'yan ta'adda guda uku tare da kwato babura guda shida bayan an kwashi lokaci ana musayar wuta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng