Taɓa Kimar Sahabban Annabi SAW: Malaman Musuluci Sun Gargadi Shehi kan Wa’azinsa
- Kungiyar Malaman Musulmi na Yarbawa ta gargadi Sheikh Habeeb Adam Al-Ilory kan kalaman da ake zargin sun saba wa Sahabbai
- Shugaban kungiyar Dr Khidr Mustafa ya ce irin wadannan maganganu na iya kai mutum ga sabawa akida
- Kungiyar ta bukaci Al-Ilory ya dauki hanyar mahaifinsa marigayi Sheikh Adam Al-Ilory wanda ya yi fice wajen hadin kai da hidima
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Agege, Lagos - Kungiyar Malaman Musulmi na Yarbawa (YMSA) ta gargadi malamin Musulunci kan kalamansa.
Kungiyar ta bukaci Daraktan Markaz At-Ta’lim Al-‘Arabi wal-Islami, Agege, Sheikh Habeeb Adam Al-Ilory, ya guji kalaman batanci ga Sahabban Annabi Muhammad (SAW).

Source: Facebook
Kungiya ta ja kunnen malamin Musulunci
A cikin wata sanarwa daga Ibadan, shugaban kungiyar, Dr Khidr Mustafa, ya nuna damuwa kan kalaman da ake danganta masa, cewar Tribune.
YMSA ta ce irin wadannan kalamai, idan an furta su, ba wai kawai za su rage darajar sahabbai ba, har ma suna iya kaiwa ga ridda.
Kungiyar ta jaddada cewa a cikin koyarwar addinin Musulunci, cin mutuncin sahabban Annabi ana daukarsa babban laifi da kaucewa daga koyarwa sahihiya.
Sanarwar ta ce:
“Su ne wadanda suka tsaya tare da Manzon Allah a lokutan tsananin wahala wajen yada addini."
Ya ambaci manyan sahabbai kamar Abu Bakr ibn Abi Quhafah, Umar ibn al-Khattab, Abu Hurayrah, Abu Musa al-Ash’ari, da Amr ibn al-‘As.
Dr Mustafa ya jaddada alkawarin Aljanna ga Abu Bakr da Umar, yana mai cewa wannan abu an tabbatar da shi a Alkur’ani da Hadisi.
“Babu Musulmi mai akida sahihiya da zai yi shakka kan yabo da darajar wadannan mazaje nagari."
- Cewar sanarwar

Source: Original
An bayyana darajar sahabban Annabi SAW
Shugaban YMSA ya bayyana Abu Bakr As-Siddiq a matsayin ginshikin gaskiya, adalci, tausayi da kauna ga Annabi Muhammad.
Mustapha ya ce:
“Alkur’ani da sahihan hadisan Annabi suna tabbatar da gaskiyar zuciyarsa da shugabancinsa wajen kare sakon Musulunci."
Kungiyar ta kuma soki abin da ta kira "labaran karya" da wasu a Yammacin duniya ke yada wa kan tarihin sahabbai.
Ta bukaci Musulmi su rike ra’ayin malamai gaskiya, su nuna kauna da girmamawa ga sahabbai, tare da nisantar da ra’ayoyin bata.
Kungiyar ta kuma shawarci Sheikh Habeeb Adam Al-Ilory ya daidaita da’awarsa kamar mahaifinsa Sheikh Adam Abdullah Al-Ilory na hadin kai da hidima.
Shehi ya yi fatawa kan satilait a gida
Kun ji cewa Sheikh Habeebullah Adam El-Ilory ya ce ya kamata a sake duba wasu koyarwar addini da suka sabawa ci gaban al’umma na yau da kullum.
Ya soki malaman da ke hana amfani da na'urorin zamani, ya ce yin haka ba ya hana shiga Aljanna domin tabbas aikata hakan ba laifi ba ne a addini.
Malamin ya tuna yadda aka soki ra’ayinsa a 2010 kan shiga siyasar mata, amma yanzu Saudiya ma ta amince da hakan a dukan matakai na kasar.
Asali: Legit.ng

