Maza Sun Gaza Ne?, ‘Dalilin da Ya Sa Ya Kamata Mace Ta Mulki Najeriya a Yanzu’
- Yar takarar shugaban ƙasa, Ada Kate Uchegbu, ta ce Najeriya na buƙatar mace shugaba don kawo sabon salo da ci gaban ƙasa
- Ta jaddada cewa sake-sake shugabanni ya gaza, mace shugaba za ta kawo sauyi, inganci, da ƙarfin matasa wajen gyaran ƙasa
- Uchegbu ta ce za ta yaƙi cin hanci da rashin tsaro, ta kuma kafa shirin samar da aikin yi ga matasa da sauya siyasar ƙasa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Yayin da ake shirye-shirye musamman kan zaben 2027 da ke tafe, wasu sun fara kiran ba mace damar zama shugabar kasa.
Yar takarar shugaban ƙasa, Ada Kate Uchegbu, ta bayyana cewa Najeriya na bukatar mace shugaba domin kawo sabon salo na shugabanci.

Source: Facebook
2027: Yar takara ta bukaci ba mata dama
Uchegbu ta jaddada cewa Najeriya ta gaji shugabanni iri ɗaya da ake maimaitawa, abin da bai haifar da ci gaba ba, cewar Tribune.
Ta ce lokaci ya yi da ya kamata a samu sauyi a Najeriya inda ta tabbatar da cewa mace shugaba za ta kawo sauyi a Najeriya.
A cewar ta, mata na daga cikin shugabanni mafi ƙarfi a Afirka, sun cancanci jagoranci ba wai kawai don nuna bambancin jinsi ba, amma saboda ƙwarewa.
Ta ce idan mace ta zama shugaban ƙasa, za a ga sabon salo a tsarin siyasar ƙasa da Afirka baki ɗaya, wannan zai wargaza tsohon tunanin da ake yi.
Yar takarar shugaban kasa ta bayyana cewa burinta shi ne kawo sauyi na ƙarni, duba da shekaru da tunani, ta ce ƙasa na bukatar sababbin ra’ayoyi da shugabanni.

Source: Facebook
Yar takara ta fadi jajircewar mata a shugabanci
Uchegbu ta ce gogewarta a aikin jarida ta koya mata yadda manufofi ke shafar rayuwar mutane, hakan ya ƙarfafa mata hangen nesa na gaskiya da riƙon amana.
Ta kuma gargadi al’ummar Anambra da su zaɓi cancanta ba kuɗi ko manyan masu goyon baya ba, ta ce cancanta ce mabuɗin ci gaban ƙasa.
Uchegbu ta bayyana cewa matsalar mata ba ta ƙwarewa ba ce, illa tsarin siyasa mai cike da wariya.
Alkawuran da yar takarar shugaban kasa ta yi
Haka kuma, ta yi alƙawarin yaƙi da tsaro ta hanyar sake fasalin hukumomi, amfani da fasaha, da samar da rukunin mata a cikin jami’an tsaro.
Ta kuma ce za ta ƙaddamar da shirin samar da aikin yi ga matasa da asusun tallafi, inda ta jaddada cewa matasa su ne makomar ƙasa.
'Tinubu zai laseh zaben 2027' - Jigon APC
Mun ba ku labarin cewa wani babban jigon APC, Farfesa Haruna Yerima, ya bayyana cewa Bola Tinubu zai yi nasarar 2027 idan ya cigaba da tafiya da Kashim Shettima.
Kungiyar Northern Ethnic Nationality Forum ta bukaci Tinubu ya sauya Shettima, inda ya ce ikirarin tsoron Musuluntarwa karya ne.
Yerima ya kara da cewa Shettima ya cancanta, kuma Tinubu ba karamin ɗan siyasa ba ne da za a tilasta masa mataimaki.
Asali: Legit.ng

