Sababbin Bayanai Sun Fito, an Gano Albashin Tinubu, Kashim da Gwamnoni

Sababbin Bayanai Sun Fito, an Gano Albashin Tinubu, Kashim da Gwamnoni

  • Sababbin bayanai sun nuna yawan albashi da Shugaba Bola Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima ke karba
  • Bayanai sun ce Tinubu na karɓar N1.4m a wata a matsayin albashi, tare da alawusai da suka kai N106m a shekara
  • Mataimakinsa, Kashim Shettima yana samun N1.2m a wata, yayin da Sanatoci ke karɓar albashi ƙasa da N1m

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Ana ci gaba da maganganu kan yawan albashin shugaban kasa, Bola Tinubu mataimakinsa da kuma sauran masu mukaman siyasa.

Sababbin bayanai sun fito kan albashin manyan jami’an gwamnati na Najeriya, bisa ga bayanan hukumar RMAFC.

An bayyana albashin Tinubu da Kashim Shettima a wata
Hukumar RMAFC na duba yiwuwar kara albashin Tinubu, Kashim. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Twitter

Yawan albashin Tinubu da Kashim Shettima

Rahoton Leadership ya ce wasu majiyoyin gwamnati sun tabbatar da yawan albashin Bola Tinubu da mataimakinsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaba Bola Tinubu yana karɓar albashi a wata na N1,405,882, baya ga alawusai da suka kai fiye da N7.5m, jimillar shekara N106,870,584.

Kara karanta wannan

Kungiyar APC ta gargadi Tinubu kan sauya Shettima, ta fadi barazanar da ke tafe

Baya ga albashi, yana da hakkin samun alawus iri-iri kamar na wahalhalu, hutu, tsaro, gidaje, kayan daki, ma’aikata, da gyaran motoci.

Mataimakinsa, Kashim Shettima yana samun N1,212,629 a wata, wanda ya kai N14,551,548 a shekara, da alawusai irin na tsaro, aiki da hidima.

Shugaban RMAFC, Mohammed Bello ya ce hukumar na shirin ƙara albashi saboda na yanzu tun 2008 aka kafa su, ba su yi daidai da halin tattalin arziki ba.

Ya ce:

“Ba za ka biya Shugaban Ƙasa N1.5m a wata ba, kana son ya yi aiki ga mutane miliyan 200.”
Albashin Tinubu da Kashim da kuma wasu yan majalisu
Hukumar RMAFC tana son kara albashin Tinubu, yan majalisu. Hoto: The Nigeria Senate.
Source: Twitter

Yawan albashin gwamnoni, yan majalisu

Sanatoci suna samun N1,063,860 a wata, ciki har da albashin N168,866, gyaran gida, wasanni, ma’aikata, takardu, tufafi, da alawus ɗin wakilai N422,166.

Alawusai na musamman kamar kayan daki N6m da tashi aiki suna biya sau ɗaya a zangon mulki, yayin da alawus motoci na zama lamuni ne.

Kakakin Majalisa yana samun albashin shekara N2.48m, amma alawus suna kai N18.3m, Mataimakin Kakakin Majalisa kuma yana samun N17.1m na alawus a shekara.

Gwamnoni na jihohi suna karɓar albashin wata-wata na N185,308, wanda ya kai N2.2m a shekara, kafin ƙarin alawus daban-daban da suka ninka kuɗin.

Kara karanta wannan

'An bar Arewa a baya,' Remi Tinubu za ta bude kamfani a Legas, an fara korafi

Alawusai sun haɗa da kuɗin mota, lafiya, gidaje, kayan daki, tafiya da izinin hutu, wanda ya sa kuɗin shekara ya kai N11.5m ga gwamnonin jihohi.

Mataimakan gwamnonin jihohi kuma suna karɓar N2.1m albashi a shekara, amma alawusai sun ƙara su kai N10.7m, cewar Vanguard.

An gargadi Tinubu kan sauya Shettima

Mun ba ku labarin cewa Kungiyar APC North Central Forum ta shiga sahun masu ba shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, shawara kan Kashim Shettima.

Shugaban kungiyar ya shawarci Bola Tinubu da ka da ya sauya Shettima don tsoron rasa kuri'un yankin Arewa ta Tsakiya.

Saleh Zazzaga ya nuna cewa ajiye Kashim Shettima na iya jawowa shugaban kasan matsala idan ya tashi neman tazarce a shekarar 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.