Dakarun Sojoji Sun Ragargaji 'Yan Ta'addan Lakurawa, an Kashe Miyagu

Dakarun Sojoji Sun Ragargaji 'Yan Ta'addan Lakurawa, an Kashe Miyagu

  • Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar hallaka wasu 'yan ta'adda na kungiyar Lakurawa a jihar Sokoto
  • Sojojin sun yi wa 'yan ta'addan kwanton bauna ne a karamar hukumar Tangaza lokacin da suka je sayen kayan abincin da za su yi amfani da su
  • Karamar hukumar Tangaza na daga cikin wuraren da 'yan ta'addan Lakurawa suke addaba da kai hare-haren ta'addanci a jihohin Sokoto da Kebbi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Sokoto - Sojojin Najeriya sun kashe wasu mutane biyu da ake zargin mambobin kungiyar ta’addanci ta Lakurawa ne a jihar Sokoto.

Dakarun sojojin sun kashe 'yan ta'addan ne a ranar Asabar, 23 ga watan Agustan 2025 a kauyen Mano, karamar hukumar Tangaza.

Sojoji sun kashe 'yan ta'addan Lakurawa a Sokoto
Hoton dakarun sojojin Najeriya a bakin aiki Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Jaridar The Punch ta rahoto cewa ’yan ta’addan sun je sayen kayan abinci ne kafin sojoji su yi musu kwanton ɓauna.

Kara karanta wannan

Sojojin sama sun yi ruwan wuta kan 'yan bindigan da suka kashe masallata a Katsina

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji sun kashe 'yan ta'addan Lakurawa

Jami’in rundunar sojoji da ke kula da Tangaza, Gudu, Binji da Silame, Manjo Chukuma, ya tabbatar da wannan farmaki, rahoton jaridar Leadership ya tabbatar.

"Sojojinmu sun tare ’yan ta’addan a kasuwa. Bayan ɗan musayar wuta, mun kashe biyu daga cikinsu, muka kwato bindigogi uku da babura guda biyar. Sauran sun gudu cikin daji, kuma dakarunmu na ci gaba da binsu.”

- Manjo Chukwuma

Wani ganau ya bayyana cewa aikin gaggawa da sojojin suka yi ya kawo saukin zuciya ga mazauna yankin.

"Mun ga su suna kokarin sayen abinci lokacin da sojoji suka iso. Bayan harbe-harbe, mun ga mutane biyu daga cikinsu sun faɗi matattu. Wannan ya ba mu ɗan kwarin gwiwa saboda mun sha wahala a hannunsu.”

- Wani ganau

Al’ummomin kan iyaka na Tangaza, Gudu da kuma Argungu a jihar Kebbi sun dade suna fama da hare-haren Lakurawa, waɗanda ke amfani da iyaka da Jamhuriyar Nijar wajen shigowa.

Kara karanta wannan

'An bar Arewa a baya,' Remi Tinubu za ta bude kamfani a Legas, an fara korafi

Mutane sun ji dadin kashe 'yan ta'adda

Wani dattijo a yankin, Alhaji Umar Bello, ya bayyana lamarin a matsayin abin karfafa gwiwa.

"Waɗannan ’yan ta’adda suna shigowa su fita yadda suka ga dama, suna kashe jama’armu da satar shanunmu."
"Wannan aikin sojoji ya nuna cewa gwamnati tana sauraronmu. Muna addu’a su ci gaba da haka har sai sun kawar da su gaba ɗaya."

- Alhaji Umar Bello

Sai dai mazauna yankin sun roƙi dakarun sojojin su ci gaba da matsa musu lamba domin samun dawwamammen zaman lafiya.

Sojoji sun kashe kwamandojin Boko Haram

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya na rundunar Operation Hadin Kai sun ragargaji 'yan ta'addan Boko Haram a jihar Borno da ke yankin Arewa maso Gabas.

Dakarun sojojin sun kashe kwamandojin kungiyar guda biyu tare da mayaka 11 bayan sun yi yunkurin kai wani harin ta'addanci a karamar hukumar Gwoza ta jihar.

Hakazalika, sojojin sun kwato makamai da dama da suka hada da bindigogi da alburusai tare da babura daga hannun miyagun 'yan ta'addan na Boko Haram.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng