‘Ku Ƙaura,’ Gwamnati Ta Gargaɗi Mazauna Gombe da Jihohi 6 kan Mummunar Ambaliya

‘Ku Ƙaura,’ Gwamnati Ta Gargaɗi Mazauna Gombe da Jihohi 6 kan Mummunar Ambaliya

  • Gwamnati ta yi hasashen ambaliya a jihohi bakwai da garuruwa 25, inda ta gargadi mazauna bakin kogin Jebba zuwa Lokoja
  • Sanarwar ta bayyana cewa jihohin da abin zai shafa sun hada da Benue, Borno, Gombe, Kebbi, Nasarawa, Neja da kuma Yobe
  • Hukumar NEMA ta yi kira ga mazauna wasu garuruwan Kebbi, Neja da Kwara da su kaura daga gidajensu don kare kai daga ambaliya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - A ranar Asabar, ma’aikatar muhalli ta tarayya ta yi hasashen yiwuwar ambaliya a jihohi bakwai da garuruwa 25 a fadin Najeriya.

Ma'aikatar ta ce ruwan sama mai yawa da ake sa ran zai sauka tsakanin 23 zuwa 24 ga Agusta, 2025 na iya janyo ambaliya a jihohin bakwai.

Gwamnatin tarayya ta ce za a fuskanci ambaliyar ruwa daga ranar 23 zuwa 24 ga Agusta, 2025, a jihohi 7
Yadda ambaliyar ruwa ta mamaye gidaje a Maiduguri, jihar Borno a 2024. Hoto: Audu Marte
Source: Getty Images

Gargadin ambaliya ga mazauna bakin kogi

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ma'aikatar ta fitar, ta hannun daraktan sashen kula da ambaliya da yankunan teku, Usman Bokani, inji rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Da gaske an yi wa Sheikh Jingir ihu a Abuja? Izala ta fadi abin da ya faru

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ma'aikatar ta umurci mazauna garuruwan bakin kogin Jebba zuwa Lokoja da su gaggauta yin hijira, saboda ruwan kogin Neja na ƙara yawa, wanda zai iya yin ambaliya kowane lokaci.

Sanarwar ta ce:

“Saboda karuwar ruwa a kogin Neja, ana shawartar mazauna yankunan bakin kogi daga Jebba zuwa Lokoja da su gaggauta barin garuruwansu."

Jihohi da garuruwan da za su fuskanci ambaliya

Jihohi da garuruwan da ake sa ran za su fuskanci wannan ambaliya sun haɗa da:

  1. Jihar Benue (Garuruwan Abinsi, Agyo, Gbajimba, Gogo, Makurdi, Mbapa, Otobi, Otukpo, Udoma, Ukpiam);
  2. Jihar Borno (Garuruwan Briyel, Dikwa, MaiduKamba);
  3. Jihar Gombe (Garuruwan Bajoga, Dogon Ruwa, Gombe, Nafada);
  4. Jihar Kebbi (Garuruwan Gwandu, Jega, Kamba);
  5. Jihar Nasarawa (Garuruwan Agima, Keana, Keffi, Odogbo, Rukubi);
  6. Jihar Neja (Garin Lapai);
  7. Jihar Yobe (Garuruwan Gashua, Gasma, Potiskum).

Ambaliya: NEMA ta aika sako ga jihohi

A ranar Juma’a, hukumar ba da agajin gaggawa ta kasa (NEMA) ta bukaci mazauna yankunan da ke cikin haɗarin ambaliya da su gaggauta yin kaura zuwa garuruwa masu aminci.

Kara karanta wannan

'An bar Arewa a baya,' Remi Tinubu za ta bude kamfani a Legas, an fara korafi

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa jihohin da ke cikin haɗarin ambaliya sosai, a cewar NEMAs, sun haɗa da Kebbi, Neja da Kwara, waɗanda ke da iyaka da ƙasar Benin.

Hukumar NEMA ta gargadi mazauna jihohin Arewa 3 da su kaura daga gidajensu don tsira daga ambaliya
Jami'an hukumar ba da agajin gaggawa ta kasa (NEMA) a bakin aiki. Hoto: @nemanigeria/X
Source: Twitter

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban sashen hulɗa da manema labarai na hukumar, Manzo Ezekiel, ya fitar.

Daraktar Janar ta NEMA, Hajiya Zubaida Umar, ta kuma umurci dukkan ofisoshin NEMA da ke kula da garuruwan bakin kogin Neja da su ƙara wayar da kan al'umma game da ambaliya.

Ta kuma roƙi gwamnatocin jihohin da aka lissafa a rahoton da su tallafa wa hukumomin agajin gaggawa na jihohi (SEMA) da kuma kwamitocin agajin gaggawa na ƙananan hukumomi (LEMC) wajen daukar matakan gaggawa domin rage illar ambaliyar bana.

Ambaliya ta cinye gidaje da gonaki a Arewa

A wani labarin, mun ruwaito cewa, mamakon ruwan sama ya jawo rushewar gidaje da cinye gonaki a jihohin Bauchi, Filato da kuma Neja.

A Filato, sama da gidaje 50 da makarantu da majami’a sun rushe yayin da guguwar ta kakkarya bishiyoyi, ta fasa turakun wuta.

A Bauchi da Neja, ambaliya ta cinye gonaki da dama, inda hukumar SEMA ta sanar da shirin fara kai tallafi ga wadanda abin ya shafa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com