Da Gaske an Yi wa Sheikh Jingir Ihu a Abuja? Izala Ta Fadi abin da Ya Faru
- Izala ta yi karin haske kan zargin cewa an yi wa shugaban malaman ta, Sheikh Sani Yahya Jingir, ihu a Abuja
- A bayani da wani jagora a Izala ya fitar, kungiyar ta ce labarin karya ne kuma sharrin masu neman bata suna ne
- Ta yi kira ga musulmai su rika binciken kowane labari kafin yada shi, kamar yadda Alkur’ani ya yi umarni da hakan
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja, Najeriya – An samu karin bayani kan jita-jitar cewa an yi wa jagoran kungiyar Izala, Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir, ihu a masallacin Guzape, Abuja.
Bayan yada labarin a yammacin ranar Juma'a, kungiyar ta fito ta karyata rade radin da ke yawo a kafafen sada zumunta.

Source: Facebook
A wata sanarwa da shugaban kwamitin yanar gizo na JIBWIS a jihar Filato, Ibrahim Maina Muhammad, ya fitar a Facebook, ya ce babu gaskiya a cikin labarin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ibrahim Maina ya ce an sanya wa’azin kai tsaye a kafafen sadarwa kuma babu wani alamu da ke nuna cewa an sami ihu ko tarzoma.
Karin bayani daga kungiyar Izala
Kungiyar ta bayyana cewa waɗanda suka yada wannan labari sun yi hakan ne don bata suna da kuma karkatar da hankalin al’umma.
A cewar sanarwar, Sheikh Jingir ya kasance malami da ya saba yin wa’azi cikin nutsuwa ba tare da damuwa da kalaman masu saurare ba.
Ibrahim Maina ya jaddada cewa gaskiya ba ta bukatar ado, kuma ya kira al’umma da su rika tantance kowane labari kafin yada shi, bisa ga koyarwar Kur'ani.
Ya ce Allah ya umarci musulmai da su tabbatar da gaskiyar kowanne bayani kafin su yada shi don kada su jefa kansu cikin nadama.
Izala ta bukaci a yi gaskiya da adalci
Sanarwar ta yi amfani da wasu ayoyin Alkur’ani daga Suratun Nisa’i (4:135) da Suratul Ma’ida (5:8), inda aka yi kira ga masu imani da su tsaya da gaskiya da adalci.
Ta kuma jaddada cewa musulmi na hakika ba sa yada jita-jita don kawai su faranta wa wasu rai ko su cutar da wanda suke gaba da shi.
Kungiyar ta yi nuni da cewa irin wadannan labaran da ake yadawa na iya zama silar shiga cikin zunubi.

Source: Facebook
Da gaske an yi wa Sheikh Jingir ihu?
A cewar Izala, yayin wa’azin da Sheikh Jingir ya gabatar a Abuja, ya yi magana kan bukatar gwamnati ta samar da taki mai inganci ga manoma.
Sai wani daga cikin jama’a ya yi magana da karfi kan batun kashe-kashen da ake fama da su a kasar.
Kungiyar ta ce hakan ba ihu bane, illa dai bayyana damuwa ne daga cikin masu sauraro, kuma Shehin bai dauki hakan a matsayin kalubale ko barazana ba.
Malaman Darika sun gana da gwamna Buni
A wani rahoton, kun ji cewa shugabannin Darikar Tijjaniyya sun gana da gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni.
Gwamna Buni ya bukaci shugabannin da su yi wa Bola Tinubu addu'a da sauran dukkan masu rike da madafun iko.
Jagoran tawagar, Sheikh Ibrahim Shehu Dahiru Usman Bauchi ya ce sun je jihar Yobe ne domin gudanar da bikin Mauludi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

