'An bar Arewa a Baya,' Remi Tinubu za Ta Bude Kamfani a Legas, an Fara Korafi

'An bar Arewa a Baya,' Remi Tinubu za Ta Bude Kamfani a Legas, an Fara Korafi

  • Uwargidan shugaban kasa Oluremi Tinubu za ta kaddamar da sabuwar cibiyar masana’antu a unguwar Mushin, Legas
  • Cibiyar ta kunshi sassa biyu, bangaren kera kayayyaki da kuma bangaren kasuwanci da horo ga ‘yan kasuwa
  • Tsohon hadimin Abdullahi Ganduje, ya soki gwamnatocin Arewacin Najeriya kan gazawar kafa irin wannan masana’anta

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Lagos – A yau ake sa ran Uwargidan shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu, za ta kaddamar da cibiyar masana’antu a jihar Legas.

Wannan aiki dai an fara tsara shi tun shekarar 2020, sannan aka fara gina shi a 2021 a cikin yankin Matori da ke unguwar Mushin.

Sabon kamfanin da Remi Tinubu za ta bude a Legas
Sabon kamfanin da Remi Tinubu za ta bude a Legas. Hoto: Lagos State Government|Salihu Tanko Yakasai
Source: Facebook

Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya bayyana a X cewa wannan gagarumin aiki alama ce ta himmar jihar wajen bunkasa masana’antu da samar da ayyukan yi.

Kara karanta wannan

Najeriya ta samu rancen $238m daga Japan, minista ya lissafa ayyukan da za a yi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Cikakken tsarin cibiyar da aka yi a Legas

Cibiyar ta kunshi manyan sassa guda biyu; na farko shi ne bangaren kera kayayyaki, inda aka tanadi injinan zamani da za su rika samar da takalma, jaka, bel da sauran kayayyaki.

Bangare na biyu kuwa, shi ne na kasuwanci wanda ya kunshi shaguna, dakin baje koli, dakunan horo, wuraren aiki da ofisoshi da aka tsara don inganta fasaha da kirkire-kirkire.

Sanwo-Olu ya kara da cewa wannan aiki ya nuna sadaukarwar Legas wajen karfafa ‘yan kasuwa da kananan masana’antu.

Tasirin masana’antar ga tattalin arziki

A cewar gwamnan, cibiyar za ta kasance muhimmin mataki wajen samar da ayyukan yi, karfafa kirkire-kirkire da kuma inganta tattalin arzikin jihar.

An bayyana cewa an tsara cibiyar don tallafawa masu sana’a da matasa masu hazaka wajen kara darajar kayayyaki a kasuwannin cikin gida da na waje.

Wannan zai baiwa Legas damar shiga cikin manyan cibiyoyin kasuwanci a fannin kayyakin da ake yi da fata a nahiyar Afirka.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Shugaban Boko Haram, Bakura ya karyata labarin kashe shi

Korafin tsohon hadimin Abdullahi Ganduje

Hadimin tsohon gwamnan Kano Abdullahi Ganduje, Salihu Tanko Yakasai, ya bayyana damuwa kan rashin samun irin kamfanin a Arewa.

Ya wallafa a X cewa Legas na karbe damarmakin da wasu jihohin Arewacin Najeriya ya kamata su mallaka, musamman jihohin Kano da Sakoto da ke samar da fata sosai a duniya.

Ya nuna takaici cewa duk da Arewa ke samar da fata ga kasuwannin Turai, har yanzu ba ta gina irin wannan cibiyar ba, illa dai shugabanni na karkata ga rarraba akuyoyi.

Idan aka yi dace, ana ganin hakan na iya zama wani darasi ga shugabannin Arewa wajen sauya akala daga siyasar tallafi zuwa aikin gina masana’antu.

Hadimin Ganduje da ya yi korafi kan kafa kamfanin takalma a Legas
Hadimin Ganduje da ya yi korafi kan kafa kamfanin takalma a Legas. Hoto: Salihu Tanko Yakasai
Source: Facebook

Tinubu ya kawo manhajar haraji a Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya kaddamar da na'urar lissafa harajin da kowa zai rika biya a Najeriya.

Shugaban kasar ya bayyana cewa an tanadi manhajar ne domin kowa ya san yadda sabuwar dokar haraji za ta shafe shi.

Ya kara da yin kira ga 'yan Najeriya da su gwada aiki da na'urar domin sanin kudin haraji da za su rika biya daga shekarar 2026.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng