Yadda Gwamna Ke Biyan Hadimansa Albashi kusan na Tinubu a Wata, Ya Ja Kunnensu
- Gwamnan Akwa Ibom, Umo Eno, ya bayyana makudan kudi da yake biyan masu taimaka masa duk wata a jihar
- Mai girma Gwamna Eno ya ce ba wani daga cikin hadimansa da ke karɓar ƙasa da miliyan ɗaya a wata
- Eno ya gargadi masu rike da mukaman siyasa ka da su yaudari al’umma, yana mai cewa za a wallafa sunayensu a jaridu
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Uyo, Akwa Ibom - Gwamna Umo Eno ya fusata game da halayen wasu hadimansa kan albashin da ake biyansu.
Gwamna Eno ya soki wasu daga cikin mataimakansa saboda maganganu da ƙanƙantar da albashinsu a bainar jama’a.

Source: Facebook
Gwamna ya bugi kirji kan albashin hadimansa
Rahoton Vanguard ya ruwaito gwamnan na cewa babu wani hadiminsa da ke karbar kasa da N1m a wata.

Kara karanta wannan
'Na sha tsangwama sosai': Gwamna ya tuna yadda ake masa ba'a ba za a zaɓi zabiya ba
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana haka ne a taron jama’a na Ikono da Ini a Ibiaku Ntok Okpo, inda ya ɗaga matsayin hadiminsa, Blessed Essien daga 'PA' zuwa 'SA'.
Gwamnan ya ce,
“Da isowa ta, na ga littafi daga wani hadimi na wanda daga ƙaramin albashi ya gina rijiyar ruwa ya rabawa yankinsa."

Source: Facebook
Gwamna ya yabawa hadiminsa kan babban aiki
Gwamnan ya ce hadimi ne ya yi haka, amma wasu masu mukaman siyasa har yanzu suna yaudarar jama’a cewa gwamnati ba ta yi komai ba.
Ya yabawa hadimin kan kokarin da ya yi tare da nuna cewa hadimai ma za su iya gudanar da irin wannan aiki ga al'umma.
Ya kara da cewa:
"Wasu na kiran shi kawai PA, amma PA ga gwamnan jiha ba zai taɓa zama na banza ba.”
“Ku saurare ni da kyau, babu wani hadimi da ke karɓar ƙasa da miliyan ɗaya, sannan idan suna magana, suna kiran shi alawus.

Kara karanta wannan
Bayan dawowa daga London, Ganduje ya bi sawun Shettima da Zulum wajen ta'aziyya Kogi
"Kuna kiran N1m alawus, a wurina, N1m ba alawus ba ne, kuɗi ne sosai wanda ba kowa ke samu ba.
"Don haka na umarci Sakataren Gwamnati ya tara sunayen dukkan masu mukaman siyasa bisa ga kananan hukumomi, za mu wallafa a jarida.”
- Cewar Gwamna Eno
Gwamna ya karawa hadiminsa girma
Gwamnan ya umarci jama’a da su tambayi wakilansu, yana cewa, “Ku kira PA ɗinku, ku kira SA, SSA, da Kwamishina, ku tambaye su, me kuka yi?”
Daga bisani ya sanar da Essien, “daga yau ka zama babban hadiminsa na musanman a kan Ayyukan Jama’a, Punch ta ruwaito.
Essien ya yi godiya ta musamman ga Gwamna Eno tare da ba shi tabbacin ci gaba da ayyukan alheri domin kawo sauyi a jihar.
Gwamnan Eno ya tuna tsangwamar da ya sha
A wani labarin, mun ba labarin cewa Gwamnan Akwa Ibom, Umo Eno, ya bayyana yadda aka yi masa ba’a yayin da yake kamfe na neman takarar gwamna.
Mai girma Gwamnan ya ce an nuna masa wariya sosai saboda shi zabiya ne a yakin neman zaben 2023 a jihar Akwa Ibom.
Eno ya ce ya sha wahala tun yana yaro saboda halittasa, amma yau yana karrama masu irin wannan yanayi saboda nuna darajarsu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng