Jami'an NDLEA Sun Cafke Dillalin Miyagun Kwayoyi da Aka Dade Ana Sa ido Kansa a Kano
- Dubun wani matashi da ake zargin mai safarar miyagun kwayoyi ne ta cika, bayan ya fada tarkon jami'an hukumar NDLEA a jihar Kano
- Jami'an na hukumar NDLEA sun cafke matashin ne mai shekaru 27 a duniya dauke da tabar wiwi mai yawa kan hanyarsa ta shiga Kano
- Kamun da aka yi masa na zuwa ne bayan an dade ana sanya ido kansa kan irin harkokin da yake gudanarwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA), reshen Kano, ta ce ta kama wani mai safarar kayan maye.
Hukumar NDLEA ta ce ta cafke mutumin mai suna Umar Adamu-Umar wanda yake da shekara 27 da haihuwa dauke da kayan laifi.

Source: Facebook
Hakan na cikin wata sanarwa ne da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar NDLEA a Kano, Sadiq Muhammad-Maigatari, ya fitar a ranar Asabar a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dilan kwaya ya shiga hannu a Kano
Ya bayyana cewa an kama dillalin ne dauke kilo 9 na tabar wiwi, wadda darajar kudin ta ya haura Naira miliyan 10.
Kakakin na NDLEA ya bayyana cewa an kama wanda ake zargin ne, mazaunin karamar hukumar Fagge ta jihar Kano, a ranar 6 ga watan Agusta.
Ya ce jami'an NDLEA da ke Kiru ne suka cafke shi a kan hanyar Zariya–Kano.
A cewarsa, an cafke shi ne a lokacin da yake ɗauke da kunshi 19 na tabar wiwin daga Legas zuwa Kano.
"Wanda ake zargin ya amsa cewa yana cikin harkar fataucin miyagun kwayoyi, kuma hukumar ta dade tana sa ido a kansa."
- Sadiq Muhammad-Maigatari.
NDLEA ta kawo cikas ga dilolin kwayoyi
Ya ƙara da cewa wannan kamen ya kawo babban koma baya ga masu safarar miyagun kwayoyi, domin an hana su samun kuɗaɗe masu yawa, an tarwatsa hanyoyin samar da kayayyakin su, tare da rage yawan kuɗaɗen da za a iya amfani da su wajen gudanar da sauran miyagun ayyuka.
"Haka kuma, kwace wannan miyagun kwayoyi daga hannun ’yan kasuwar ya taimaka wajen kare al’ummomi daga illolin da ke tattare da fataucin kwayoyi."
- Sadiq Muhammad Maigatari
Mai magana da yawun na NDLEA ya ce hukumar karkashin jagorancin Malam Abubakar Idris-Ahmad za ta kara tsaurara sintiri da kuma gudanar da ayyukan leken asiri domin magance safarar miyagun kwayoyi a jihar.

Source: Facebook
Karanta wasu labaran kan hukumar NDLEA
- Dilolin kwaya 2 sun gamu da hukumar NDLEA, kotu ta yanke masu shekaru 10 a kurkuku
- Jami'an NDLEA sun kai samame, an cafke masu safarar miyagun kwayoyi
- Kano: NDLEA ta yi babban kamu, fitaccen matashi mai safarar kwayoyi, ya shiga hannu
Jami'an NDLEA sun cafke mai safarar kwaya
A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA), sun cafke wani dillalin kwaya da aka dade ana nema ruwa a jallo.
Sunday Ibigide ya shiga hannu ne a jihar Delta, bayan jami'an hukumar NDLEA sun kwashe shekara uku suna farautarsa.
Dillalin miyagun kwayoyin dai ya fada komar NDLEa lokacin da yake rarraba tabar wiwi mai yawan gaske.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

