2027: Malamin Addini Ya 'Gano' Shirin Amurka domin Cire Tinubu da Ƙarfin Tsiya
- Limamin kirista, Elijah Ayodele ya gargadi Bola Tinubu kan zargin sauya mataimakinsa, Kashim Shettima
- Ayodele ya kuma yi magana kan tazarcensa, ya ce Amurka na “daura damara” domin ganin an cire shugaban daga mulki
- Malamin ya ja kunnen Tinubu ka da ya canza Shettima, ya ce hakan zai zama babbar illa da jawo masa makiya
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual Church, Primate Elijah Ayodele, ya sake gargadin Shugaba Bola Tinubu.
Fasto Ayodele ya yi gargadi kan sauya mataimakinsa, Kashim Shettima, da kuma burin tazarce a 2027.

Source: Twitter
Fasto ya gargadi Tinubu game da Shettima
Rahoton Tribune ya ruwaito cewa malamin ya ce Amurka na “daura damara” domin ganin ta cire shugaban daga mulki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Fasto Ayodele ya gargadi Tinubu ka da ya sauke Shettima, inda ya ce ko da mataimakin ya bata masa rai, ya dai sulhunta da shi domin alfaninsa.
Ya bayyana cewa yunkurin kawo wani a matsayin mataimaki zai zama “babban asara” kuma zai “lalata damar shugaban” tare da haifar masa da makiya marasa.
Ya ce:
“Sauke Shettima zai jefa ka cikin matsala; wadanda ke son a cire shi abokan gaba ne da ba sa son ka yi nasara. Duk abin da Shettima ya aikata, ka manta, mu tura kasa gaba.
“Idan ka cire Shettima, asara ce a gare ka; Ka da ka cire shi idan kana son kiyaye damar ka, ku yi sulhu ya zauna; idan ba haka ba, zai zama babban illa ga gwamnatinka.”

Source: Facebook
Ana zargin Amurka na yakar Tinubu
Malamin ya bayyana cewa Shettima ba barazana ba ne ga Tinubu, amma shugaban zai fuskanci kalubale daga Arewa, inda ya yi hasashen cewa Sarakunan gargajiya za su hada baki a kansa.
Fasto Ayodele ya kuma bayyana cewa Amurka ba za ta goyi bayan tazarcen Shugaba Tinubu ba, za ta yi duk abin da ya dace domin ganin an cire shi daga mulki.
Ya yi kira ga shugaban da ya guji matsalolin da ya jawo da kansa ta hanyar warware batun yunwa da tsaro.
Ya kara da cewa:
“Ka kuma tabbatar ka gyara batun hulda da kasashen duniya, kamar yadda na fada, Amurka ba abokiyarka ba ce. Amurka na daura damara domin ta cire ka; za ta yi duk abin da ya dace domin ganin ka sauka daga mulki.”
Ya bayyana cewa akwai mutanen da za su iya kayar da Tinubu, duk da cewa babu wanda ya fito fili yanzu, amma bisa halin da ake ciki, idan suka fito za su iya kayar da shi.
“Ba na goyon bayan kowa. Idan wani ya fito ya tsaya takara kuma zai iya kayar da kai, zan fada maka, amma ban gani ba tukuna.
“Shettima ba matsalarka ba ne, amma yunwar da ake ciki da sauran abubuwa. Idan ba ka magance su ba, cire wani ko kara wani a gwamnatinka ba zai amfani ka ba."
- Cewar Fasto Ayodele
Legit Hausa ta tattauna da dan APC
Daya daga cikin mambobin kungiyar Shettima Support Group, Nasir Musa Isa ya ce wannan abin da Fasto ya fada gaskiya ne.
Nasir ya ce har yanzu babu wanda zai iya ce maka ga abin da ya faru tsakanin Tinubu da Shettima.
Ya ce:
"Har yanzu fa jita-jita kawai ake yadawa amma babu wani abin da ya faru tsakaninsu, muna goyon bayan tafiya da Shettima 100%."
Fasto ya yi magana kan hadakar jam'iyyu
Kun ji cewa gabanin zaɓen 2027, Fasto Babatunde Elijah Ayodele ya bayyana cewa "sai da sihiri ne kawai za a rushe kawancen" ADC.
Ana kallon wannan sabon kawancen na ADC a matsayin babban sauyi a fagen siyasar Najeriya.
Fasto Ayodele ya faɗi haka ne yayin da yake jawabi ga manema labarai, game da zabukan da ke tafe.
Asali: Legit.ng


