Shettima, Sarkin Musulmi, Sanusi II, Manyan Kasa Sun Halarci Jana'izar Sarkin Zuru
- Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya jagoranci tawagar gwamnatin tarayya wajen halartar jana’izar marigayi Sarkin Zuru
- Marigayi Sarkin ya rasu a birnin Landan yana da shekaru 81, inda aka birne shi bayan sallar Juma’a a garin Zuru, jihar Kebbi
- Rahoto ya nuna cewa shugabanni da sarakunan gargajiya daga sassa daban-daban na ƙasar sun halarci jana’izar tare da yin ta’aziyya ga jama'a
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kebbi – An gudanar da jana’izar marigayi Sarkin Zuru, Mai Martaba Janar Muhammadu Sani Sami, wanda ya rasu a asibiti a birnin Landan yana da shekaru 81, bayan rashin lafiya.
An yi jana’izar ne a babban masallacin Juma’a na Zuru bayan Juma’a, inda babban limamin masallacin, Alhaji Suleiman Muhammad Tanko, ya jagoranci sallar.

Source: Facebook
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya wallafa a X cewa shi ya jagoranci tawagar gwamnatin tarayya zuwa jana'izar.
Daga nan aka kai gawar marigayin zuwa gidansa da ke Zuru, inda aka birne shi a wani waje na musamman.
Manya sun halarci jana'izar Sarkin Zuru
Mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya jagoranci tawagar gwamnatin tarayya zuwa jana’izar, inda ya mika sakon ta’aziyyar shugaba, Bola Ahmed Tinubu.
Shettima ya bayyana marigayi Sarkin a matsayin shugaba nagari da ya bar manyan ayyuka na zaman lafiya da haɗin kai a ƙasar nan.
Ya ce:
“Ayyukansa za su ci gaba da kasancewa abin tunawa.”
Haka kuma, gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, da tsohon ministan tsaro, Laftanar Janar Abdulrahman Dambazau, sun samu halarta.
Mai alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar II, da Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, sun halarci sallar jana’izar.
Daga cikin sauran manyan da suka halarci jana’izar har da Sarkin Yauri, Sarkin Anka, Sarkin Gummi, da kuma Estu Nupe, Alhaji Yahaya Abubakar.
Karin mutanen da aka gani a jana'izar

Kara karanta wannan
Fadar shugaban kasa ta ragargaji Atiku, El Rufa'i kan wata nasarar da Tinubu ya samu
Ministan harkokin jinƙai, Dr Yusuf Tanko Sununu, da tsohon gwamnan Kebbi, Sa’idu Dakingari, suma sun halarci taron jana’izar.
Haka nan, dattawan Arewa da sarakunan gargajiya daga jihohi daban-daban sun yi tattaki zuwa Zuru domin girmama marigayin.
Daily Trust ta wallafa cewa a yayin jana’izar, duk kasuwanni da shaguna a fadin masarautar Zuru aka rufe domin nuna alhini da mutunta marigayin.

Source: Facebook
Haka kuma, manyan hanyoyi da tituna na gari sun cika da daruruwan jama’a da suka fito domin yi masa bankwana na ƙarshe.
Marigayi Janar Muhammadu Sani Sami, wanda aka fi sani da Sami Gomo II, ya kasance Sarkin Zuru mai tasiri da gagarumar rawar da ya taka wajen ci gaban masarautarsa.
Gwamna Buni ya gana da 'yan Darika
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya gana da shugabannin Darikar Tijjaniya a fadar gwamnatinsa.
Mai Mala Buni ya bukaci shugabannin da su rika yi wa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu addu'a da sauran shugabanni.
Sheikh Ibrahim Dahiru Usman Bauchi ya bayyana cewa sun ziyarci jihar Yobe ne domin taron Mauludi Darikar Tijjaniyya.
Asali: Legit.ng
