Bayan Korafe Korafe, Tinubu Ya Ɗauki Alƙawari bayan Kisan Masallata a Katsina
- Gwamnatin tarayya ta yi magana bayan kisan Musulmai suna tsaka da sallah a jihar Katsina a makon nan
- Gwamnatin ta yi alkawarin cafke wadanda suka kai mummunan hari kan masu ibada a garin Malumfashi
- Ministan yada labarai, Mohammed Idris ya ce jami’an tsaro sun bi sawun ‘yan ta’addan kuma za a cimma su
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta yi Allah wadai da harin yan bindiga kan masallata a Malumfashi da ke jihar Katsina.
Gwamnatin ta yi rantsuwa za ta cafke tare da gurfanar da wadanda suka kashe masu ibada a masallaci cikin karamar hukumar Malumfashi.

Source: Twitter
Alkawarin gwamnatin Tinubu kan yan bindiga
Hakan na cikin wata sanarwa da ma'aikatar yada labarai da wayar da kan jama'a ta wallafa a shafin Facebook.

Kara karanta wannan
'Mun sha azaba,' Adadin bayin Allah da 'yan ta'adda su ka hallaka a Katsina ya haura 55
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar da ministan yada labarai, Mohammed Idris ya sanyawa hannu, ta ce gwamnatin ta ɗauki hakan a matsayin keta doka da mugunta kan al’umma masu zaman lafiya.
Idris ya ce jami’an tsaro sun fara bin sawun masu laifin, kuma ba za a bari lamarin ya wuce haka ba tare da daukar matakin bincike da daukar mataki ba.

Source: Facebook
Kokarin gwamnatin Tinubu a yaki da ta'addanci
Idris ya tabbatar wa ‘yan kasa cewa adalci zai kasance cikin gaggawa da tsauri, yana mai jaddada cewa ba za a bari ayyukan ta’addanci su samu tushe a kasar nan ba.
Sanarwar ta ce:
“Gwamnatin tarayya na Allah wadai da wannan mummunan hari, wannan ba kawai hari ne kan Malumfashi ba, har ma kan darajar mu ta kasa.
“Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana mika ta’aziyya ga iyalan mamatan, al’ummar Malumfashi da gwamnatin Katsina.
"Allah ya ji kan wadanda suka rasu, ya ba iyalansu hakuri. Gwamnati na tare da su a wannan mawuyacin hali mai ciwo.
“’Yan kwanakin baya, cibiyar yaki da ta’addanci ta kasa (NCTC) ta sanar da kama shugabannin manyan kungiyoyin ta’addanci ciki har da Mahmud al-Nigeri da mataimakinsa.”
Yadda aka kama shugabannin yan ta'adda
An kuma kama Mahmud Muhammad Usman (Abu Baraa) na kungiyar Ansaru.
Kamar yadda rahotanni suka gabata kafin yanzu, wadannan shugabanni suna cikin jerin sunayen da ake nema a kasashen duniya.
Kama wadannan shugabanni alama ce ta nasarorin da ake samu a yakin da gwamnati ke yi da ta’addanci, bisa umarnin Shugaba Tinubu.
Ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya tabbatar da cewa ayyukan ta’addanci kan kasar nan da ‘yan kasa za su zama tarihi nan ba da jimawa ba.
Gwamnatin Bola Tinubu ta jaddada cewa duk wanda ya zubar da jinin marasa laifi ba zai samu mafaka ko wurin boyewa a cikin Najeriya ba.
Adadin wadanda aka kashe a masallaci ya karu
Mun ba ku labarin cewa al'ummar Gidan Mantau a Malumfashi, jihar Katsina, sun bayyana irin halin ƙunci da suka shiga bayan mummunan harin ‘yan ta’adda a yankin.
Rahotanni sun tabbatar da cewa sama da gawarwaki 50 aka gano, yayin da ake ci gaba da binciken wasu a cikin dazuka.
Mazauna yankin sun roƙi gwamnatin tarayya da ta jihar Katsina da su ɗauki mataki don kare su daga ƙarin hare-hare.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

