Wata Sabuwa: An Fadi Sojojin da Suka Fi Yan Bindiga Hatsari, an Nemo Mafita
- Hafsan tsaro, Janar Christopher Musa ya ce rundunar soji tana daukar tsauraran matakai wajen daukar ma’aikata da horaswa
- Ya bayyana cewa gwamnati ta fara karfafa sojoji da sababbin makamai, jiragen sama da kayan aikin yaki domin yaki da ta’addanc
- Musa ya ce rundunar soji tana kiyaye dokoki, tana kauce wa barnar fararen hula, kuma tana hukunta duk sojan da ya aikata laifi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Hafsan tsaron kasa, Janar Christopher Musa, ya yi magana kan kwarewar dakarun sojoji.
Janar Musa ya bayyana cewa rundunar soji tana daukar matakai na tsanaki wajen daukar ma’aikata da kuma horaswa kafin a tura su aiki.

Source: Twitter
Musa ya fadi yadda suke ba sojoji horaswa
Janar Musa ya bayyana hakan ne yayin hira da gidan talabijin na Channels, inda ya ce rashin horo na iya zama barazana fiye da barayin daji ko ‘yan ta’adda.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Musa ya ce babu wani abin da ake kira “harbi da gangan” a rundunar soji, saboda duk matakin harbi yana bukatar tsari da shiri.
A cewarsa, kowane soja ana horas da shi ya dauki bindigarsa tamkar ransa, inda ake koyar da su cewa rasa bindiga babban laifi ne.
Ya kara da cewa gwamnati karkashin shugaba Bola Tinubu tana cika alkawarin karfafa rundunar soji ta hanyar karin dakarun aiki da sababbin jiragen yaki da kayayyaki.

Source: Facebook
Makaman da rundunar sojoji ta karba
Janar Musa ya tabbatar da cewa an karbi sababbin jiragen sama, jiragen yaki masu saukar ungulu, tare da jiragen 'Super Tucano' da aka cika musu makaman yaki.
Ya ce dogaro da makaman kasashen waje babban kalubale ne, inda ya jaddada bukatar Najeriya ta samar da nata kayan aikin yaki domin cin gashin kanta.
Hafsan tsaron ya koka kan rahoton da ya nuna yawan mace-mace a 2025 ya ninka na bara, saboda ‘yan ta’adda na boyewa cikin al’umma.
Ya bayyana cewa sojoji suna kauce wa kai hare-hare idan za su jawo mutuwar fararen hula, duk da haka hakan na baiwa ‘yan ta’adda damar tserewa.
Sai dai ya gargadi cewa duk wani farar hula da ya taimaka wa ‘yan ta’adda zai zama abin kai hari da doka za ta dauki mataki a kansa.
Janar Musa ya magantu kan gurbatattun jami'ai
Musa ya amince akwai wasu mugayen jami’ai da ke shiga cikin aikin tsaro, musamman daga sauran hukumomi, kamar yan sanda amma ya ce a bangarensu, kotun soja na hukunta su.
Ya bayyana cewa akwai tsofaffin sojoji da dama da ke zaman gidan yari saboda laifuffukan taimakawa ‘yan bindiga ko rashin da’a a bakin aiki.
Hafsan tsaron ya jaddada cewa rundunar soji za ta ci gaba da kare Najeriya, tabbatar da ladabi da gaskiya a cikin aikin sojoji da kare fararen hula.
Sojoji sun kama makamai a Kaduna
A baya, kun ji cewa dakarun Operation Hadin Kai sun gano tarin harsashi da aka ɓoye a cikin wata mota a hanyar Maiduguri zuwa Kaduna.
Ana zargin cewa kayan na da alaka da wani soja da ke aiki a Damaturu, wanda yanzu ake nema domin a cafke shi.
Hukumar ta ce wannan babban ci gaba ne wajen rage yaduwar makamai da ke haddasa rashin tsaro a jihohin Arewa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

