Lokaci Ya Yi: Sarki Mai Martaba a Najeriya Ya Rasu Yana Mai Shekaru 89

Lokaci Ya Yi: Sarki Mai Martaba a Najeriya Ya Rasu Yana Mai Shekaru 89

  • An kara yin babban rashi a Najeriya da Sarkin Arigbajo, Mai Martaba Timothy Oluwole Sunday Mosaku ya rasu yana da shekara 89
  • Iyalansa sun tabbatar da rasuwar basaraken a wata sanarwa da suka rabawa manema labarai a yau Juma'a, 22 ga watan Agusta, 2025
  • Sanarwar ta bayyana tsare-tsaren jana'izar Marigayi Sarkin wanda za a yi a ranaku biyu a watan Satumba mai zuwa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ogun - Mai Martaba Sarkin Arigbajo na karamar hukumar Ifo a jihar Ogun, Oba Timothy Oluwole Sunday Mosaku, ya riga mu gidan gaskiya.

Marigayin Sarkin, wanda aka haifa a shekarar 1936, ya mutu yana da shekaru 89 a duniya.

Sarki a Ogun ya rasu.
Hoton marigayi Oba Timothy Oluwole Sunday Mosaku wanda ya rasu a Ogun Hoto: Oluwole Sunday
Source: UGC

Sarki mai martaba a Ogun ya mutu

Iyalan marigayi sarkin ne suka tabbatar da rasuwar cikin wata sanarwa da suka aika wa jaridar Punch a yau Juma’a, inda suka bayyana jadawalin jana’izarsa.

Kara karanta wannan

Al'umma sun samu sauƙi: Sojoji sun damƙe hatsabibin ɗan bindiga, yaransa 13

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce:

“Za a gudanar da taron tunawa da shi a ranar Alhamis, 25 ga Satumba, 2025, a fadarsa da ke Arigbajo da misalin karfe 5:00 na yamma.
"Sannan za a yi jana’iza a ranar Juma’a, 26 ga Satumba, a cocin St. John’s Anglican Church, Arigbajo, karamar hukumar Ifo, jihar Ogun, da misalin karfe 11:00 na safe.”

Takaitaccen tarihin rayuwar Sarki Mosaku

An haifi Oba Mosaku a shekarar 1936 a gidan Pa Samuel Olaonipekun Mosaku, ɗan Egunleti Mosaku (ɗan fari na Mamowolo).

Oba Mosaku ya taso tare da biyo duka matakai a cikin tsarin sarautar Arigbajo har zuwa lokacin da ya zama cikakken Sarki.

Ya rike sarautar Otun Baale na Arigbajo a shekarar 2001, daga bisani aka daukaka shi zuwa Baale a 2008, sannan a 2010 gwamnatin jihar Ogun ta amince da shi a hukumance a matsayin Sarkin Arigbajo.

Bikin nadin sarautarsa ya gudana ne karkashin jagorancin Mai Martaba Sarkin Egbaland, Oba Adedotun Aremu Gbadebo.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: An gano yadda ake amfani da siyasa wajen zafafa hare hare a Najeriya

Yadda aka kafa masarauta da garin Arigbajo

A wata tattaunawa da jaridar Vanguard ta yi da shi a watan Disamba 2023, marigayi Sarkin ya bayyana cewa kakansa ne ya kafa garin Arigbajo.

Ya ce:

"Ya zo wannan wurin ne domin ya yi farauta, bayan ya farauto namun daji, sai ya ci wani ɓangare, ya yi kyauta da wani, ya kuma kai sauran kasuwa a Itoku, Abeokuta. A haka ne ya kafa garin Arigbajo.”

Ya ce akwai dangantaka tsakanin Arigbajo da ƙasar Egba, inda ya nuna cewa zuriyarsa ta Owu tana da alaka kai tsaye da manyan sassan Egba guda hudu: Egba Ake, Oke-Ona, Gbagura, da Owu.

Taswirar jihar Ogun.
Hoton taswirar jihar Ogun da ke Kudu maso Yammacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Marigayi Oba Mosaku ya yi karatun firamare a Arigbajo, sannan ya halarci makarantar sakandire ta Modern School da ke Abeokuta.

Daga bisani ya shiga cibiyar Government Trade Centre, Ijebu-Ode, da kuma Institute of Management, inda ya samu digiri na biyu a fannin aikin jarida.

Jihar Ekiti ta rasa daya daga cikin sarakunanta

Kara karanta wannan

Mutuwa ta ratsa masana'antar fim, firaccen jarumi ya yi bankwana da duniya

A wani rahoton, kun ji cewa Sarkin Aramoko Ekiti, Oba Olu Adegoke Adeyemi, ya koma ga mahaliccinsa yana da shekara 82 a duniya.

Majiyoyi suka ce marigayin ya shahara saboda shugabanci mai nagarta, hikima, da jajircewa wajen inganta walwalar al’ummarsa.

A wata sanarwa da suka fitar, iyalansa sun bayyana mulkinsa a matsayin lokaci da ya kawo hadin kai, ci gaban al’adu, zaman lafiya da inganta rayuwar matasa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262