Ana Wata ga Wata: Shugaban Boko Haram, Bakura Ya Karyata Labarin Kashe Shi

Ana Wata ga Wata: Shugaban Boko Haram, Bakura Ya Karyata Labarin Kashe Shi

  • Shugaban Boko Haram, Ibrahim Muhammad ya musanta rahoton gwamnatin Nijar da ta ce an kashe shi a hare-haren jiragen sama a Diffa
  • Sojojin Nijar sun sanar cewa an kawar da Bakura da wasu manyan kwamandoji yayin hare-haren da suka kai a Korongol, Kournawa da Shilawa
  • Bakoura ya ce ya ga labarin “mutuwarsa” a shafukan sada zumunta, amma ya jaddada cewa bai mutu ba duk da aukuwar hare-haren

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Niamey, Nijar – Ibrahim Muhammad Bakura, wanda aka fi sani da Abu Umaima, babban shugaban Boko Haram, ya fito ya musanta rahoton gwamnatin Nijar cewa an kashe shi.

Legit Hausa ta rahoto cewa kasar Nijar ta ce ta kashe Bakura ne a cikin hare-haren jiragen saman da aka kai a yankin Diffa.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta ragargaji Atiku, El Rufa'i kan wata nasarar da Tinubu ya samu

Shugaban Nijar, Abdurahamane Tchiani da shugaban Boko Haram, Abu Umaima
Shugaban Nijar, Abdurahamane Tchiani da shugaban Boko Haram, Abu Umaima. Hoto: Zagazola Makama|Getty Images
Source: Facebook

Legit ta tabbataro bayanan da shugaban 'yan ta'addan ya yi ne a wani sako da Zagazola Makama ya wallafa a X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da farko, sojojin Nijar sun bayyana cewa an hallaka Bakura da wasu kwamandojin ƙungiyar yayin farmakin da jiragen yaƙi suka kai a ranar 15 ga Agusta a Korongol, Kournawa da Shilawa.

Sai dai a cikin wata tattaunawa da aka ji daga bayan fage, Bakura ya bayyana cewa labarin mutuwarsa karya ne, inda ya nuna cewa shi da kansa ya ga rahoton a shafukan sada zumunta.

Sojojin Nijar sun ce sun hallaka Bakoura

A rahoton da rundunar sojin Nijar (FAN) ta fitar ya tabbatar da cewa an kai hare-haren da suka lalata sansanonin Boko Haram da ke a Diffa, tare da kashe mayaƙa da dama.

Sojojin sun bayyana cewa waɗanda aka hallaka sun haɗa da manyan kwamandoji, ciki har da Bakura wanda aka bayyana a matsayin babban ɗan ta'adda.

Kara karanta wannan

Nijar: An harbe shugaban Boko Haram da ya maye gurbin Shekau har lahira

Shugaban kasar Nijar, Abdurahamane Tchiani.
Shugaban kasar Nijar, Abdurahamane Tchiani. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Shugaban ƙasar Nijar, Janar Abdurahamane Tchiani, ya yi murna da wannan nasara, inda ya ce kisan Bakura ya zama babban ci gaba a yaki da ta’addanci a ƙasar.

Shugaban Boko Haram ya ce yana raye

Rahoton Tribune ya nuna cewa an samu saƙon sadarwa da aka tsinkaya daga Bakura a ranar Juma'a, inda ya nuna rashin gaskiyar rahoton.

A cikin saƙon, Bakura ya shaida wa kwamandojinsa cewa ya ga labarin a shafukan sada zumunta cewa an kashe shi, amma ya tabbatar musu da cewa yana nan da rai.

Ya kuma amince cewa hare-haren da sojojin Nijar suka kai gaskiya ne, amma ya ƙara da cewa ba shi da alaƙa da jerin mutanen da aka kashe a lokacin farmakin.

Janar Musa ya yi magana kan ta'addanci

A wani rahoton, kun ji cewa hafsun tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya bayyana cewa akwai 'yan siyasa masu taimakawa 'yan ta'adda.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: An gano yadda ake amfani da siyasa wajen zafafa hare hare a Najeriya

Janar Musa ya ce ya ce mutanen sun siyasantar da lamarin tsaron Najeriya domin son cimma manufar su a 2027.

Baya ga haka, shugaban tsaron ya ce 'yan ta'addan Najeriya suna samun goyon baya daga kasashen waje, musamman a bangaren kudi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng