Abu Ya Girma: Malaman Musulunci Sun Yi Zanga Zanga kan Alaƙar Najeriya da Isra'ila
- Manyan malamai Musulmi a Ibadan sun gudanar da zanga-zangar lumana, suna adawa da duk wata hulɗar soja tsakanin Najeriya da Isra’ila kan Gaza
- Malaman sun bayyana Isra’ila a matsayin ƙasar da take nuna wariyar launin fata da laifin kisan gilla, suna kira ga gwamnati ta katse dangantaka baki ɗaya
- MURIC ta bayyana cewa Isra’ila na kashe yara da yunwa, da harin asibitoci, makarantu, wuraren ibada da mafaka, tana kira Najeriya ta fasa yarjejeniya
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ibadan, Oyo - Shugabannin Musulmi a Kudu maso Yamma sun gudanar da zanga-zangar lumana a Ibadan, Jihar Oyo da ke yankin a Najeriya.
Malaman Musulunci sun suna adawa da hulɗar soja tsakanin Najeriya da kasar Isra’ila da suke ganin akwai matsala duba da kisan kiyashi da kasar ke yi.

Source: Original
Isra'ila: Malaman Musulunci sun yi zanga-zanga
Kungiyar 'Aqsah Nigeria' reshen Ibadan ce ta shirya wannan zanga-zanga, don jan hankali kan rikicin Gaza da kuma kiran kawo ƙarshen abin da suka kira kisan gilla, cewar Daily Trust.
Malamai fitattu sun halarta ciki har da Dr. Dawud Amoo-Alaga, Sheikh Abdulwaheed Abdul Hamid, Sheikh Abdul Fatah Sanni da Sheikh Dhikrullah Shafii.
Zanga-zangar ta biyo bayan bayanan ma’aikatar tsaro ta Najeriya da suka tabbatar da shirye-shiryen ƙarfafa hulɗar soja da Isra’ila a fannoni daban-daban.

Source: Twitter
MURIC ta zargi Isra'ila da kisan kiyashi
Wannan ya haɗa da ziyartar ma’aikatar ta tsaro da jakadan kasar Isra’ila, Michael Freeman ya yi inda aka tattauna aikin haɗin gwiwa da yarjejeniyar soja.
Yayin jawabi, Daraktan MURIC, Farfesa Ishaq Akintola, ya la’anci Isra’ila kan hare-haren da ake yi a Gaza wanda ya ce sun sabawa dokokin ɗan Adam.
Ya zargi Isra’ila da ragargazar makarantu, majami’u, masallatai, gidajen jarida, da sansanonin ‘yan gudun hijira, inda dubban mutane da ‘yan jarida suka hallaka.

Kara karanta wannan
Fadar shugaban kasa ta ragargaji Atiku, El Rufa'i kan wata nasarar da Tinubu ya samu
Ya ce:
“A ranar Talata, yara 266 sun mutu da yunwa saboda kulle. Isra’ila ta mayar da asibitoci wuraren mutuwa yayin tattaunawar tsagaita wuta."
Kungiyar MURIC ta kalubalanci kasar Isra'ila
Akintola ya ce wannan keta hakkin ɗan Adam ne yana jaddada cewa Isra’ila ƙasar wariyar launin fata ce mai laifin kisan gilla a Gaza, The Nation ta tattaro.
Ya tambayi dalilin da yasa Najeriya za ta nemi hulɗar soja da Isra’ila, yana kira gwamnati ta katse yarjejeniyar tsaro da kuma huldar tattalin arziki.
Sheikh Gumi ya koka kan alaƙar Najeriya, Isra'ila
Mun ba ku labarin cewa Sheikh Ahmad Mahmud Gumi ya nuna rashin jin daɗi kan zuwan mataimakiyar ministar harkokin wajen Isra’ila, Sharren Haskel-Harpaz Najeriya.
Malamin ya yi zargin cewa Isra’ila na iya amfani da wannan ziyara wajen cutar da shugabannin Musulmi a kasar duba da zargin sharrinsu da ake yi.
Haskel ta gana da manyan shugabannin Kiristoci a Abuja tare da tattaunawa kan haɗin kai da alaƙar diflomasiyya a tsakanin kasashen biyu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
