An Dauki Gwamna 1 a Najeriya, An ba Shi Lambar Yabo Ta 'Zabin Jama'a' a Kasar Faransa
- An bai wa Gwamna Bala Mohammed lambar yabo a kasar Faransa bisa yadda ya kawo sauyi a harkokin shugabancin jihar Bauchi
- Gwamnan ya shiga cikin jerin gwamnonin kasashen Afirka da suka samu lambar yabon People’s Choice Governors Excellence Award a birnin Faris
- Sanata Bala Mohammed ya ce wannan girmamawa za ta kara zaburar da shi wajen kawo manufofin da za su inganta rayuwar yan Bauchi
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Bauchi - Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya samu lambar yabo ta zabin jama'a, 'People’s Choice Governors Excellence Award' a birnin Faris na kasar Faransa.
An karrama Gwamna Bala ne tare da gwamnoni tara daga nahiyar Afirka domin yaba masu bisa kyakkyawan jagorancin da suka kafa a jihohinsu.

Source: Facebook
Mai magana da yawun gwamnan Bauchi, Mukhtar Gidado ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai jiya Alhamis, kamar yadda Leadership ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka ba Gwamna Bala lambar yabo
Ya bayyana cewa lambar yabon da aka bayar a rukunin nahiyar Afirka, ta zakulo shugabannin da suka kawo sauyi da jagoranci mai nagarta ga al'umarsu.
A cewarsa, wannan lambar yabo ta zo ne a matsayin girmamawa ga tsare-tsaren gwamnan da suka kunshi inganta rayuwar jama’a, samar da ayyukan raya kasa, da tabbatar da shugabanci nagari.
Shugaban ma'aikatar fadar gwamnatin Bauchi, Dr. Aminu Hassan Gamawa ne ya wakilci Gwamna Bala a wurin bikin mika wadannan kyaututtuka a birnin Faris.
Jawabin da gwamnan ya yi a Faransa
A jawabin da ya isar ta bakin wakilinsa, gwamnan ya bayyana wannan karramawa a matsayin kira na kara dagewa wajen yi wa Bauchi hidima.
Ya ce:
“Wannan kyauta tana tunatar da mu cewa, duk wani ci gaba da muka samu a yau shi ne kakkarfan ginshikin ci gaban gobe. Ba wai game da mukami ko siyasa ba ne, sai dai tasirin abin da za mu bari.”
Ya yi godiya ga masu shirya bikin saboda adalcinsu da jajircewarsu wajen haskaka shugabannin da ayyukansu ke kawo canji mai kyau a nahiyar Afirka.
An karrama gwamnoni 10 daga Afirka
Bikin na Paris ya samu halartar shugabanni, masana tsare-tsare, da masu fafutukar ci gaba, inda gwamnoni 10 daga kasashen Afrika, ciki har da Kenya, Masar, Morocco, Habasha, da Najeriya, suka samu lambar yabo.
Gwamna Bala ya jaddada manyan nasarorin da gwamnatinsa ta samu, ciki har da gina sabbin hanyoyi da gine-ginen zamani, gyaran makarantu da cibiyoyin kiwon lafiya a kananan hukumomi 20.

Source: Twitter
Haka kuma, ya bayyana cewa gwamnatinsa ta rungumi hadin kai da zaman lafiya a matsayin mabuɗin ci gaban Bauchi, rahoton The Sun.
Gwamnan ya kuma gayyaci kasashen duniya su halarci taron zuba jari na Bauchi mai zuwa, inda za a nuna damammaki a fannonin noma, gine-gine, ma’adinai, fasaha da yawon bude ido.
Gwamnan Bauchi ya ba dan China mukami
A wani rahoton, kun ji cewa Gwamnan Bala Mohammed ya nada ɗan ƙasar China, Li Zhensheng, a matsayin mai ba shi shawara kan tattalin arziki.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Kano ta bullo da shirin afuwa ga 'yan daba, ta fadi wadanda za su amfana
Gwamna Bala ya bayyana hakan ne a wurin taron rattaba hannu kan wata yarjejeniya tsakanin gwamnatin Bauchi da cibiyar CGPCRC.
Bala Mohammed ya ce wannan matakin da ya dauka zai sanya Bauchi ta zamo a gaba gaba wajen kulla alaka da kasashen duniya don samar da ci gaba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
