Masu Sayen Baburan Sata a Kano Sun Fada Tarkon 'Yan Sanda, an Kama Mutum 10

Masu Sayen Baburan Sata a Kano Sun Fada Tarkon 'Yan Sanda, an Kama Mutum 10

  • Rundunar ’yan sandan Kano ta cafke mutum 10 da ake zargi da sayen babura da aka sata bayan kama sanannen barawo, Dahiru Jibrin
  • ’Yan sanda sun samu nasarar kwato babura guda bakwai tare da mika su ga sahihan mutanen da suka mallake su a jihar Kano
  • Kwamishinan ’yan sanda, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yaba da kokarin jami’ansa tare da kiran jama’a da su ba da bayanai kan masu laifi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano – Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta tabbatar da kama mutum 10 da ake zargi da sayen babura da aka sata daga hannun barayi.

Rahotanni sun tabbatar da cewa 'yan sanda sun kuma kwato babura guda bakwai da aka riga aka mika ga masu su.

Babura 7 da 'yan sanda suka kwato a jihar Kano
Babura 7 da 'yan sanda suka kwato a jihar Kano. Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Source: Facebook

An yi ram da barawon babura a Kano

Kara karanta wannan

Nijar: An harbe shugaban Boko Haram da ya maye gurbin Shekau har lahira

Kakakin 'yan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya wallafa labarin a wani sako da ya fitar a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne mako biyu bayan cafke sanannen barawo, Dahiru Jibrin, wanda ake zargi da hannu a satar babura a sassa daban-daban na jihar.

Kwamishinan ’yan sanda na jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya bayyana cewa wannan nasara ta biyo bayan zurfaffen bincike da sashen CID ya gudanar.

Binciken ya bai wa jami’an tsaro damar gano sauran wadanda ke da hannu a cinikin babura da aka sata a jihar.

An mika baburan sata ga masu su

Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce bincike ya sanya an kama masu sayen kayan sata da suka hada da babura a jihar Kano.

Ya ce hakan ne ya sanya 'yan sanda kama su domin karya tsarin ta’addancin sata da safarar babura a jihar.

An bayyana cewa kwace babura bakwai, aka mika su ga sahihan masu su ya kara tabbatar da jajircewar rundunar wajen kare dukiyoyin jama’a da kuma tabbatar da adalci.

Kwamishinan 'yan sandan Kano, CP Bakori na jawabi
Kwamishinan 'yan sandan Kano, CP Bakori na jawabi. Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Source: Facebook

Karin haske daga kwamishinan 'Yan sanda

Kara karanta wannan

Zaben 2027: An gano yadda ake amfani da siyasa wajen zafafa hare hare a Najeriya

Kwamishinan ’yan sanda ya jinjinawa jami’an da suka gudanar da binciken bisa jajircewa, kwazo da kuma bin ka’idojin aikin ’yan sanda.

Ya ce wannan mataki ba rage damuwar jama’a ya yi ba kawai, har ma ya nuna cewa rundunar ta himmatu wajen murkushe duk wata hanyar aikata laifi a Kano.

Babban jami'in ya kuma bukaci jama’a da su ci gaba da bayar da bayanai da rahotanni na gaggawa domin taimaka wa ’yan sanda wajen dakile laifi, musamman satar babura.

Kiran hadin kai daga jama’an Kano

Rundunar ta jaddada cewa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen fatattakar masu laifi da kuma kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

An shawarci al’umma da su yi amfani da lambobin gaggawa da aka wallafa domin bayar da bayanai kan duk wani abin da ya shafi tsaro.

A baya, jami'an tsaro sun saba cewa sai jama'a sun bada gudumuwa wajen samun zaman lafiya.

Janar Musa ya magantu kan ta'addanci

A wani rahoton, kun ji cewa Hafsun tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya ce 'yan siyasa na kara dagula matsalar tsaro.

Kara karanta wannan

Adamawa: An kama matar da ke sace yara daga Arewa zuwa Kudu ta sayar da su

Janar Musa ya bayyana cewa wasu daga cikin 'yan siyasa na amfani da matsalar tsaro domin nuna gazawar gwamnati.

Ya ce sannu a hankali hukumomin tsaro na bincike tare da bin diddigi domin gano masu daukar nauyin ta'addanci a Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng