Kotu Ta Taka wa Gwamnatin Kogi Burki daga Hana Tsohon Mataimakin Gwamna Hakkinsa
- Kotun daukaka kara ta Abuja ta tabbatar da hukuncinta da ya umarci gwamnatin Kogi ta biya tsohon mataimakin gwamna Simon Achuba hakkokinsa
- Ta ce kudin da su ka hada da alawus, albashinsa da gwamnati ta rike da sauransu da ta umarci a biya Achuba ya kai N1.07bn, kuma dole a bi doka
- Alkalan kotu sun ce ba za a iya daukaka kara zuwa kotun koli ba, domin ita ce matakin karshe a shari’o’in da su ka danganci sha'anin kwadago
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kogi – Kotun daukaka kara da ke Abuja ta tabbatar da hukuncinta na baya da ya umarci gwamnatin Kogi ta biya tsohon mataimakin gwamnan jihar, Simon Achuba hakkokinsa, N1.07bn.
A hukuncin da aka yanke a ranar Talata, kotun ta tabbatar da matsayin ta a matsayin kotu ta ƙarshe da ke da hurumin sauraro da yanke hukunci a kan dukkannin batutuwan kwadago.

Source: UGC
The Cable ta ruwaito kotun ta kuma bayyana cewa gwamnatin jihar Kogi ba za ta iya daukaka kara zuwa kotun koli ba a kan wannan hukunci.
Kotu ta takawa gwamnatin jihar Kogi burki
Premium Times ta ruwaito cewa kwamitin alkalai uku karkashin Okon Abang ya yi watsi da bukatar Gwamna Usman Ododo da kuma babban mai shari’a na jihar, inda suka nemi kotun ta dakatar da aiwatar da hukuncin.
Kotun ta ce:
“Hukuncin wannan kotu shi ne na ƙarshe. Idan doka ta ce hukuncin wannan kotu shi ne na ƙarshe, babu abin da masu kare kansu za su iya yi."
Achuba, wanda aka tsige daga kujerarsa a 2019, ya kai kara zuwa kotun masana’antu ta kasa (NICN) inda ya nemi a biya shi albashi da kudin sallama da sauran hakkokinsa

Source: Original
A ranar 4 ga Nuwamba, 2020, kotun ta yanke hukuncin da ya tabbatar da cewa dole gwamnati ta biya shi kudinsa.
Gwamnatin jihar ta daukaka kara, amma a ranar 29 ga Afrilu, 2024, kotun daukaka kara ta tabbatar da hukuncin, inda ta tabbatar da hakkin Achuba na karbar albashi da alawus.
Tsohon mataimakin gwamnan Kogi ya je kotu
Bayan gwamnatin ta ki bin umarnin kotu, Achuba ya sake komawa kotu. A ranar 25 ga Afrilu, 2025, kotun daukaka kara ta kayyade hakkokinsa zuwa N1,070,860,138.
A hukuncin nasa, Alkalin Abang ya jaddada cewa a karkashin Sashe na 243(4) na Kundin Tsarin Mulki na 1999 da aka yi wa kwaskwarima, ta jaddada huruminta kan shari'ar.
Ya bayyana bukatar gwamnatin jihar na kan shari'ar a matsayin marar tushe kuma sakaci ne tare da nuna raini ga kotu.
Tsohon gwamnan Kogi ya kara aure
A wani labarin, mun wallafa cewa rahotanni sun tabbatar cewa tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya ƙara aure yayin wani biki na sirri da aka gudanar a birnin Abuja.
A cikin bidiyon da aka yada a kafafen sada zumunta, an ga yadda aka gudanar da bikin cikin natsuwa, inda ‘yan uwa da abokai suka halarta ba tare da an yi babban taro ba.
Matarsa ta uku, Hafiza Yahaya Bello, ta tabbatar da auren ne ta kafar sada zumunta, ta yi maraba da sabuwar amarya tare da addu’ar albarka da zaman lafiya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

