Bayan Dawowa daga London, Ganduje ya bi Sawun Shettima da Zulum wajen Ta'aziyya Kogi

Bayan Dawowa daga London, Ganduje ya bi Sawun Shettima da Zulum wajen Ta'aziyya Kogi

  • Tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya dawo daga London inda ya shafe kwanaki bayan saukarsa daga shugabanci
  • Da isowarsa Najeriya, ya kai ziyara ta musamman ga Gwamna Usman Ododo na Kogi domin yin ta’aziyya bisa rasuwar mahaifinsa
  • Haka kuma Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya jagoranci tawagar gwamnatin tarayya zuwa gidansu Ododo domin jajanta musu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kogi – Tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya kai ziyara ta’aziyya ga Gwamnan Jihar Kogi, Usman Ododo, bayan dawowarsa daga London.

Rahotanni sun nuna cewa ziyarar ta gudana ne a ranar Alhamis a gidan gwamnatin jihar da ke Lokoja.

Ganduje yana jawabi a jihar Kogi yayin ta'aziyya ga Ododo
Ganduje yana jawabi a jihar Kogi yayin ta'aziyya ga Ododo. Hoto: Abdullahi Umar Ganduje
Source: Facebook

Legit ta tattaro bayanai kan ziyarar da Abdullahi Ganduje ya kai ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Akwai kura: ASUU ta sake taso da batun rufe jami'o'in Najeriya, ta lissafo dalilanta

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Ododo ya rasa mahaifinsa, Alhaji Ahmed Momohsani Ododo, wanda ya rasu a makon da ya gabata, lamarin da ya jefa iyalinsa da jama’ar jihar cikin alhini.

Tun bayan rasuwar, manyan jami’an gwamnati, ‘yan siyasa, da shugabanni daga sassa daban-daban na ƙasar sun dinga kai ziyara domin jajantawa da nuna goyon baya ga iyalan marigayin.

Ganduje ya yi wa Ododo ta'aziyya a Kogi

A cikin jawabin da ya yi, Ganduje ya ce ya dawo daga London ranar Laraba kuma ya ziyarci Gwamnan Kogi ranar Alhamis domin yin ta’aziyyar rasuwar mahaifinsa.

Ya ce:

“Ina roƙon Allah Madaukakin Sarki Ya gafarta masa, Ya sanya shi cikin Aljanna Firdaus, Ya kuma bai wa iyalan da aka bari haƙuri da juriya.”

Ganduje ya yi addu’a ga iyalan marigayin tare da jaddada cewa marigayin ya bar tarihi na kishin al’umma da kyautatawa ga jama’arsa.

Tsohon shugaban APC ɗin ya shafe kwanaki a London bayan ya sauka daga kujerar jagorancin jam’iyyar, inda daga nan ya koma gida ya ci gaba da hulɗar siyasa da jama’a.

Kara karanta wannan

Gwamnan Kano, Abba ya rantsar da sabon shugaban hukumar yaƙi da cin hanci

Shettima ya jagoranci tawaga zuwa Kogi

A wani bangare, Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya jagoranci tawagar gwamnatin tarayya zuwa Okene a ranar Laraba, domin jajantawa ga Gwamna Ododo da iyalinsa.

Shettima ya wallafa a X cewa tawagar ta haɗa da Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, da Ministan Noma, Sanata Abubakar Kyari, da sauran manyan jami’an gwamnati.

A yayin ziyarar, Shettima ya yi addu’ar Allah Ya jiƙan marigayin tare da sanya shi cikin Aljanna Firdaus, ya kuma ba da ƙarfafa guiwa ga iyalan da al’ummar jihar gaba ɗaya.

Iyalan Ododo sun nuna godiyarsu ga Ganduje da sauran shugabanni da suka kawo ta’aziyya tun bayan rasuwar mahaifinsu, Alhaji Ahmed Momohsani Ododo.

Tawagar gwamnatin tarayya yayin ta'aziyya a Kogi
Tawagar gwamnatin tarayya yayin ta'aziyya a Kogi. Hoto: Kashim Shettima
Source: Facebook

An yi jana'izar mahaifin gwamna Ododo

A wani rahoton, kun ji cewa an yi sallar gawar mahaifin gwamnan Kogi, Alhaji Ahmed Momohsani Ododo.

Rahotanni sun bayyana cewa tarin jama'a ne daga sassa daban daban na jihar Kogi suka halarci jana'izar.

Binciken Legit Hausa ya gano cewa Alhaji Ahmed Momohsani Ododo ya rasu ne bayan ya shafe shekara 83 a duniya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng