Akwai Kura: ASUU Ta Sake Taso da Batun Rufe Jami'o'in Najeriya, Ta Lissafo Dalilanta
- Kungiyar malaman jami'o'i ta kasa (ASUU) ta nuna fushinta kan yadda gwamnatin tarayya ke jan kafa wajen cika mata alkawuran da ta dauka
- Shugaban ASUU na kasa, Farfesa Christopher Piwuna, ya nuna cewa akwai yiwuwar kungiyar za ta tsunduma yajin aiki
- Malamin jami'ar ya koka da cewa gwamnati ta yi kunnen uwar shegu kan bukatun da kungiyar take so a cika mata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Plateau - Ƙungiyar malaman jami’o’i ta kasa (ASUU) ta yi gargadin yiwuwar shiga yajin aikin gama-gari a fadin kasar nan.
Kungiyar ASUU ta yi zargin cewa gwamnatin tarayya da gaza cika yarjejeniyoyin da aka dade ana yi dangane da farfaɗo da jami’o’in gwamnati da kuma kudaden tafiyar da su.

Source: Getty Images
Shugaban kungiyar ASUU na kasa, Farfesa Christopher Piwuna, ya bayyana hakan yayin taron manema labarai a jami’ar Jos a ranar Alhamis, 21 ga watan Agustan 2025, cewar rahoton tashar Channels tv.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa ASUU za ta shiga yajin aiki?
Christopher Piwuna ya bayyana cewa malaman jami’a sun jure fiye da shekaru biyu, suna fuskantar karya alkawura da kuma dabarun jan lokaci daga gwamnati.
Ya lissafa batutuwan da ba a warware ba, waɗanda suka haɗa da, sabunta yarjejeniyar 2009 tsakanin ASUU da gwamnatin tarayya, biyan bashin albashi, kin karin girma da kuma walwalar malaman da suka yi ritaya.
"Ya kamata jama’a su sani cewa ASUU ta rubuta wasiku da dama zuwa ga gwamnatin tarayya tana jawo hankalinta kan bukatar a warware wannan rikici cikin lumana."
"Abin bakin ciki, gwamnatin tarayya tana ci gaba da yin kunnen uwar shegu ga bukatunmu.”
"Kamar kullum, gwamnatin tarayya ce ke tursasa kungiyarmu ta shiga yajin aiki. A bayyane yake cewa ASUU ba ta da wani zaɓi face ta ɗauki mataki domin tilasta gwamnati ta saurari bukatunmu ta kuma yi abin da ya dace.”
"Gwamnati ta yi alkawura kan waɗannan batutuwa. Abin takaici, muna nan yau muna sanar da jama’ar Najeriya cewa waɗannan batutuwan da za su iya jefa sashen ilimi cikin wani mummunan rikici, an yi kunnen uwar shegu da su."
- Farfesa Christopher Piwuna
Shugaban na ASUU ya yi watsi da shirin gwamnatin tarayya na bayar da bashi ga ma’aikatan jami'a, inda ya bayyana hakan a matsayin wani tarko, rahoton Vanguard ya tabbatar da batun.
"Ya’yanmu ba sa bukatar rance. Abin da muke bukata shi ne aiwatar da yarjejeniyoyin da za su amfane mu. Har yanzu muna bin gwamnati albashin watanni uku, amma yanzu suna ce mana mu nemi bashi.”
- Farfesa Christopher Piwuna

Source: Twitter
Kungiyar ASUU ta yi korafi kan fansho
A kan batun fansho, ƙungiyar ta yi korafi cewa farfesoshi da suka yi aiki fiye da shekaru 40 yanzu haka suna karɓar abin da bai wuce N150,000 ba, duk da tsadar rayuwa da hauhawar farashin kayayyaki.
Ƙungiyar ta bayyana cewa za ta jira sakamakon taron ta da gwamnati da aka tsara gudanarwa a ranar 28 ga watan Agusta, kafin ta yanke hukunci kan mataki na gaba.
Sai dai ta sanar da cewa mambobinta za su gudanar da zanga-zanga a manyan jami’o’i a mako mai zuwa domin nuna ɓacin ransu.

Kara karanta wannan
Bayan dawowa daga London, Ganduje ya bi sawun Shettima da Zulum wajen ta'aziyya Kogi
Ba mu fatan a shiga yajin aiki
Wami dalibin ajin karshen a jami'ar ABU, Faisal Sulaiman, ya shaidawa Legit Hausa cewa ko kadan ba ya fatan a shiga yajin aiki.
"Yajin aiki ba abin da yake yi sai batawa dalibai lokaci su dade ba su gama karatu ba. Muna fatan su sasanta ba sai lamarin ya kai ga rufe jami'o'i ba"
- Faisal Sulaiman
'Yan ASUU, SSANU sun shiga yajin aiki
A wani labarin kuma, kun ji cewa kungiyoyin ASUU da SSANU sun tsunduma yajin aikin sai baba ta gani a jami'ar jihar Legas (LASU).
Kungiyoyin sun tsunduma yajin aikin ne kan wasu matsaloli da aka gaza magancewa a jami'ar.
Sun bukaci mambobinsu da su yi gaggawar janye aikinsu nan take ba tare da bata wani lokaci ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

