Tsakanin Assadus Sunnah, Asada Waye Mai Gaskiya? Dan Sadiya Ya Magantu kan Sulhu
- Sheikh Musa Yusuf Assadus Sunnah ya jagoranci zaman sulhu da Bello Turji, inda aka saki mutane sama da 30 bayan tattaunawa
- Malam Murtala Bello Asada ya soki sulhun, yana zargin akwai boye-boye da karɓar kuɗi daga wasu da ke kiran kansu malamai
- 'Dan Sadiya ya tabbatar da sulhu ba tare da fansa ba, ya ce suna son zaman lafiya tare da mutunta alkawarin da aka yi
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kaduna - An yi ta maganganu kan zama da aka yi da Bello Turji a jihar Zamfara karkashin jagorancin malamin addinin Musulunci.
Sheikh Musa Yusuf Assadus Sunnah shi ya jagoranci tawagar inda ya ce sun yi zama kuma an saki wasu mutane dalilin haka.

Source: Facebook
Yayin wata hira da jaridar DCL Hausa da aka wallafa a Facebook dan bindiga, Dan Sadiya ya yi magana kan abin da ya faru lokacin sulhun.

Kara karanta wannan
Tsohon ministan Buhari ya yi magana game da mulki, 'yan adawa da halin da APC take ciki
Assadus Sunnah ya jaddada sulhu da yan bindiga
Wannan magana ta Dan Sadiya ya jefa shakku game da maganganun malamai da ke sukar juna.
Assadus Sunnah ya tabbatar da cewa sulhu ita ce mafita domin kawo karshen kashe-kashen da ake yi a yankin Arewa ta Yamma.
Malamin ya ce dalilin zaman da suka yi da Turji ya saki wadansu mutane fiye da 30 bayan wa'azi da suka yi masa.
Sai dai wasu malamai sun soki maganar sulhu inda suke cewa bai kamata bayan kisan al'umma kuma a yi sulhu da su ba.

Source: Facebook
Asada bai tare da Assadus Sunnah
Daga cikin wadanda suke sukar lamarin akwai Sheikh Murtala Bello Asada wanda ya ce tabbas an yaudari malamai kan maganar tattaunawa da ake yi da su.
Asada ya ce akwai zargin cewa wasu na karbar kudi da nufin sulhu yayin da suke karyar ba a biya kudin fansa ba sabanin abin da yan uwan wadanda aka saken suke fada.
Dan Sadiya ya magantu game da sulhu
A yayin hirar, Dan Sadiya ya tabbatar da cewa suna bukatar sulhu amma dole a bi wasu tsare-tsare domin samun zaman lafiya.
Dan Sadiya ya tabbatar da cewa babu ko sisin kwabo da aka biya su amma kuma suka saki wadanda suka kama saboda suna son zaman lafiya.
Ya ce:
"Muna so mu zauna lafiya mun saki mutane kuma babu ko sisin kwabo da aka bamu mun dauka mun ba da su.
"Mun saurari kiran malamai, mun fahimce su kuma mun ba su rana tare da cika musu alkawari, mun yi maganganu da su tare da cika ka'ida."
Har ila yau, Dan Sadiya ya karyata cewa akwai wadanda aka yi wa yankan rago inda ya ce bai san da labarin ba kuma bai yadda da maganar ba.
Abin da yan Zamfara ke fada kan sulhu
Kun ji cewa mazauna Sabon Birni, Isa da Shinkafi a jihar Zamfara da Sokoto sun bayyana matsayarsu kan sulhu.
Mutanen sun yi watsi da kiran tattaunawa da hatsabibin dan bindiga, Bello Turji, suna cewa sulhun bai da amfani.
Al'ummomin yankunan sun zargi Turji da kashe-kashe, garkuwa da mutane, cin zarafin mata da kona kauyuka da-dama.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

