Gwamnatin Kano Ta Bullo da Shirin Afuwa ga 'Yan Daba, Ta Fadi Wadanda Za Su Amfana
- Gwamnatin jihar Kano ta shirya gyara matasan da suka tsinci kansu a cikin harkar dabanci wadanda suka ajiye makamansu
- Kwamishinan yada labarai na jihar Kano, ya bayyana cewa an gama tantance matasa 718 wadanda gwamnati za ta yi wa afuwa
- Ibrahim Abdullahi Waiya ya kara da cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya damu matuka kan matsalar harkar daba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ta bayyana shirinta na yin afuwa ga matasan ’yan daba da suka tuba karkashin shirin ta na ‘safe corridor’.
An kirkiro shirin ne domin kawo karshen ɗabanci na siyasa da tashin hankali tsakanin matasa a jihar.

Source: Facebook
Kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida, Ibrahim Abdullahi-Waiya, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba a hedkwatar rundunar ’yan sandan jihar yayin kaddamar da shirin, cewar rahoton jaridar The Punch.
Ya ce an riga an yi wa matasa 718 rajista, yayin da wasu 960 ke jiran tabbatarwar ’yan sanda kafin a saka su cikin shirin.
Gwamna Abba ya damu da matsalar daba
Kwamishinan ya bayyana cewa Gwamna Abba Kabir ya damu matuka kan matsalar dabanci.
"Mai girma Gwamna Abba Yusuf ya damu kwarai da wannan matsala ta dabanci saboda ci gaban da take haifarwa abu ne mummuna, wanda yake bata sunan jihar."
"Saboda haka mai girma gwamna ya yanke shawarar fara wannan shiri don magance matsalar.”
- Ibrahim Abdullahi Waiya
Ibrahim Abdullahi Waiya ya bayyana cewa matasan za a yi musu gwajin miyagun kwayoyi, a yi musu gyaran tarbiyya, sannan a sake dawo da su cikin al’umma, rahoton Vanguard ya tabbatar.
'Yan daba za su samu afuwa a Kano
Ya kara da cewa gwamnan zai bayar da afuwa bayan tabbatarwar ’yan sanda.
"Mun sani sosai cewa wasu daga cikin matasan da suka tsinci kansu a ciki, ba da gangan suka shiga ba, ba sha’awar su ba ce, amma wasu ’yan siyasa masu mugun nufi ne suka jawo su cikin hakan."
"Wannan gwamnati ba za ta yarda da hakan ba, kuma ba za ta bari hakan ya ci gaba a jihar ba."
"Da zarar an basu afuwa, za su zama ’yantattu daga duk wani zargi ko laifi, kuma za a ɗauke su kamar sauran mutanen kirki na al’umma."
- Ibrahim Abdullahi Waiya

Source: Facebook
Shi ma kwamishinan ’yan sanda, Ibrahim Adamu Bakori, ya yi kira ga waɗanda har yanzu ke riƙe da makamai da su mika su ga hukumomi.
Ya bayyana cewa wannan shiri dama ce a garesu domin su fara sabuwar rayuwa,su kuma zama ’yan kasa masu amfani a cikin al’umma.
Gwamna Abba ya rantsar da shugaban PCACC
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya rantsar da shugaban hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci (PCACC).
Gwamna Abba ya rantsar da Sa'idu Yahya a matsayin sabon shugaban hukumar PCACC, bayan wa'adin Muhuyi Magaji Rimin-Gado ya cika.
Babban lauya kuma kwamishinan shari'a na jihar Kano, Haruna Isa Dederi, ya jagoranci rantsarwar a fadar gwamnatin Kano.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

