Sojoji Sun Kama Makamai ana Shirin Tafiya da Su Jihar Kaduna daga Borno

Sojoji Sun Kama Makamai ana Shirin Tafiya da Su Jihar Kaduna daga Borno

  • Dakarun Operation Hadin Kai sun gano tarin harsashi da aka ɓoye a cikin wata mota a hanyar Maiduguri–Kaduna
  • Ana zargin cewa kayan na da alaka da wani soja da ke aiki a Damaturu, wanda yanzu ake nema domin a cafke shi
  • Hukuma ta ce wannan babban ci gaba ne wajen rage yaduwar makamai da ke haddasa rashin tsaro a jihohin Arewa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Dakarun sojin Najeriya da ke aiki a ƙarƙashin Operation Hadin Kai sun kama wata babbar jaka cike da harsasai da aka ɓoye a cikin wata mota a hanyar Maiduguri–Kaduna.

Lamarin ya faru ne a wurin binciken sojoji da ke Nafada, hanyar zuwa Gombe, bayan direban motar ya nuna shakku kan wata jakar da aka ba shi ya kai Kaduna.

Kara karanta wannan

Rundunar 'yan sanda ta dakume manyan barayi da jagoran 'yan ta'adda a Abuja

Wajen da sojoji suka kama tarin harsahi a iyakar Gombe da Yobe
Wajen da sojoji suka kama tarin harsahi a iyakar Gombe da Yobe. Hoto: Zagazola Makama
Source: Facebook

Zagazola Makama ya wallafa a X cewa bayan an buɗe jakar, sai aka gano cike take da harsasai masu yawa, abin da ya janyo bincike mai zurfi kan waɗanda ke da hannu a harkar.

Yadda aka gano tarin harsashi a mota

Rahotanni sun nuna cewa direban motar ya karɓi jakar a Maiduguri tare da adireshin wanda zai mika wa a Kaduna.

Duk da haka, direban ya bayyana damuwarsa ga sojoji, yana mai cewa bai san abin da ke cikin jakar ba.

Sojojin da ke bakin aiki a wurin suka umarci direban ya buɗe jakar, inda nan take aka gano makamai da yawa da aka lullube cikin dabara.

Wannan lamari ya nuna irin dabarun da masu safarar makamai ke amfani da su wajen ɓoye haramtattun kayayyaki.

An zargi wani soja da safarar makaman

Binciken farko ya nuna cewa an danganta kayan makaman da wani soja da ke aiki a Damaturu, jihar Yobe.

Kara karanta wannan

Kotu ta rufe asusun banki 4 da ake zargin na da alaka da tsohon shugaban NNPCL, Kyari

Rahotanni sun bayyana cewa an riga an sanar da rundunar da ya ke aiki da ita domin a gano shi tare da hukunta shi.

Tasirin kama makaman da aka yi

Masu sharhi kan tsaro sun bayyana wannan mataki a matsayin babbar nasara wajen dakile yaduwar makamai a ƙasar.

Sun ce hanyar Maiduguri–Kaduna na da muhimmanci ga ‘yan kasuwa da fasinjoji, amma kuma ana ta amfani da ita wajen safarar makamai da miyagun kaya.

Hukuma ta gargadi cewa masu safarar makamai na iya ci gaba da amfani da direbobi da ba su san komai ba domin jefa su a hadari.

Hafsun tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa
Hafsun tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa. Hoto: Defence Headquaters
Source: Facebook

Don haka, an ce dole ne a ƙara tsaurara tsaro da bincike sosai a dukkan wuraren binciken da sojoji ke tsayuwa a kan hanyoyin Najeriya.

An bukaci hallaka Turji maimakon sulhu

A wani rahoton, kun ji cewa hadimin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad ya bukaci jami'an tsaro su yi watsi da maganar sulhu da BelloTurji.

Rahotanni sun bayyana cewa Bashir ya yi magana ne bayan da aka fara wata tattaunawa da wasu malaman addini da dan ta'addan.

Maimakon sulhu, matashin 'dan siyasar ya bukaci da a yi wa Bello Turji hukunci kamar yadda aka yi wa wasu daga cikin shugabannin Boko Haram.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng