Duk da Yin Sulhu, 'Yan Bindiga Sun Kashe Manoma a Kaduna
- 'Yan bindiga sun kai harin ramuwar gayya bayan 'yan sa-kai sun kashe dan uwansu a karamar hukumar Birnin Gwari
- Miyagun sun huce fushinsu kan manoman da ke dawowa daga gonakinsu, wadanda ba su san hawa ba, ba su san sauka ba
- Harin da 'yan bindigan suka kai na zuwa ne duk da sulhun da aka yi da su a yankin na Birnin Gwari a kwanakin baya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kaduna - 'Yan bindiga sun kashe manoma biyar a wani hari da suka kai a kauyen Kakangi da ke yammacin karamar hukumar Birnin Gwari a jihar Kaduna.
Rahotanni sun bayyana cewa daga cikin waɗanda aka kashe, mutum hudu ’yan gida ɗaya ne.

Source: Twitter
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa harin ya auku ne da yammacin ranar Talata, 19 ga watan Agustan 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan bindiga sun kashe manoma a Kaduna
'Yan bindigan sun farmake su ne yayin da suke dawowa daga gonakinsu, inda kuma wasu mutane uku, suka jikkata.
Wannan harin ya faru ne duk da yarjejeniyar zaman lafiya da ake da ita a yankin.
Majiyoyi daga yankin sun ce maharan sun fito ne da nufin ramuwar gayya bayan wasu 'yan sa-kai daga al’ummomin jihar Neja, sun kashe wani da ake zargin ɗan bindiga ne a ranar Litinin.
Rahotanni sun nuna cewa 'yan sa-kai a Neja kan dora alhakin hare-haren da ake kai wa al’ummominsu a kan ’yan bindigan da ke ɓoye a dajin Birnin Gwari, waɗanda kan ketara su kai hari a kauyukan da ke kan iyaka.
Bayan kisan da aka yi a ranar Litinin, ’yan bindigan da aka kashe ɗan uwansu sun yi alwashin ɗaukar fansa, inda suka kai hari kan manoma daga Kakangi da ke dawowa daga gona a ranar Talata.
An bukaci gwamnati ta dauki mataki
Shugaban ƙungiyar Birnin Gwari–Niger Inter-Border Communities for Peace and Development (BG-NI CUPD), Ishaq Usman Kasai, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Source: Original
Ishaq Usman Kasai, wanda kuma tsohon shugaban kungiyar Birnin Gwari Emirate Progressive Union (BEPU) ne, ya bayyana cewa manoma uku da suka jikkata yanzu haka suna karɓar magani a babban asibitin Jibril Mai Gwari.
“Muna Allah wadai da wannan kisan gilla na manoma marasa laifi a Kakangi, tare da mika ta’aziyyarmu ga majalisar Sarkin Kakangi da dukkan al’ummar yankin.”
"Muna kira cikin gaggawa ga hukumomin ƙaramar hukuma, gwamnatin jihar Kaduna, gwamnatin tarayyar Najeriya, da sauran masu ruwa da tsaki a yarjejeniyar zaman lafiya da sulhu."
"Da su ɗauki matakai cikin gaggawa domin hana rushewar zaman lafiyar da al’ummar Birnin Gwari suka daɗe suna ƙoƙarin farfaɗowa da shi.
- Ishaq Usman Kasai
'Yan bindiga sun kona mutane a Katsina
A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga dauke da makamao sun kai kazamin hari a jihar Katsina.
'Yan bindigan sun kona mitame 20 bayan sun farmaki wani kauye da ke karamar hukumar Malumfashi.
'Dan majalisar dokokin jihar Katsina mai wakiltar Malumfashi, Hon. Aminu Ibrahim, ya koka kan yadda 'yan bindiga ke cin karensu babu babbaka a mazabarsa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


