'Ta Gigita Ni': Tsohon Shugaban APC kan Mutuwar Buhari, Ya Tuna Haɗuwarsu Ta ƙarshe

'Ta Gigita Ni': Tsohon Shugaban APC kan Mutuwar Buhari, Ya Tuna Haɗuwarsu Ta ƙarshe

  • Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Bisi Akande, ya kai ziyara gidan marigayi Muhammadu Buhari
  • Cif Akande ya ziyarci gidan Buhari ne da ke Kaduna, inda ya bayyana mutuwarsa a matsayin babban rashi
  • Dattijon ya tuna haduwarsa ta karshe da Buhari a Daura, yana mai cewa tsohon shugaban ya kasance cikin koshin lafiya a lokacin

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kaduna - Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Cif Bisi Akande, ya bayyana Muhammadu Buhari a matsayin shugaba mai kishin kasa.

Tsohon gwamnan Osun ya ce mutuwar Buhari ta gigita shi inda ya tuna haduwarsu ta karshe a Daura.

Tsohon shugaban APC ya jajantawa iyalan marigayi Buhari
Cif Bisi Akande yayin ziyarar ta'aziyya a gidan marigayi Buhari da ke Kaduna. Hoto: Muhammadu Buhari.
Source: Facebook

Bisi Akande ya je ta'aziyya gidan Buhari

Akande ne ya jagoranci tawagar abokan siyasa zuwa Kaduna domin yin ta’aziyya ga iyalan Buhari, cewar Punch.

Kara karanta wannan

ADC ta cimma matsaya da Atiku, Peter Obi da Amaechi kan batun takara a zaben 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce labarin rasuwar tsohon shugaban ya girgiza shi sosai kuma bai taba tsammanin haka a wannan lokaci ba.

Tsohon ya tuna ganawarsa ta karshe da Muhammadu Buhari a Daura, inda ya bayyana cewa ya kasance cikin koshin lafiya, cikin kuzari, kuma ba ya nuna rashin lafiya.

Akande ya ce ganawar tasu ta kasance cikin annashuwa, inda suka yi barkwanci kan yadda kowannensu yake jin dadin rayuwa a kauyensa.

Ya kara da cewa, kafin rasuwar tasa, ya na shirin ziyartar sa a Kaduna, sai kawai ya ji cewa ya yi tafiya kafin daga baya ya rasu.

Bayan dawowarsa Najeriya, Akande ya ce wajibi ne abu na farko da zai yi shi ne ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigayi shugaban.

Akande ya bayyana cewa:

“Na samu labarin mutuwarsa a kasar waje, labari ne mai matukar radadi, abu mai matukar zafi da ba zato ba tsammani.
“Na dawo gida, kuma abin farko da ya kamata in yi shi ne in ziyarci iyalansa, in yi musu ta’aziyya, kuma in yi addu’a da su."

Kara karanta wannan

An yi babban rashi, mahaifiyar shugaban APC na kasa ta rasu bayan jinya

Bisi Akande ya ziyarci gidan marigayi Buhari a Kaduna
Marigayi Buhari yayin taro a fadar shugaban kasa a mulkinsa. Hoto: Muhammadu Buhari.
Source: Facebook

Bisi Akande ya kwarara yabo ga Buhari

Akande ya yi wa Buhari yabo mai yawa, inda ya bayyana shi a matsayin shugaba nagari da tasirinsa ba zai gogu ba a tarihin Najeriya, Daily Post ta ruwaito.

Akande ya ce Buhari ya bar darasi na gaskiya, biyayya da sadaukarwa, wanda zai ci gaba da zaburar da al’ummar Najeriya tsawon lokaci.

“Ya kasance dan Najeriya, mai kishin kasa,ya gama aikinsa, kuma ya tafi, ayyukansa nagari za su ci gaba da wanzuwa saboda irin gudunmawar da ya ba wa Najeriya."

- Cewar Akande

Tawagar Akande ta kunshi Sanata Abu Ibrahim, tsohon ministan matasa, Sunday Dare, Alhaji Mahmud Abdullahi, Silas Agara da Mohammed Alhaji Yakubu.

A gidan marigayin dake Kaduna, Aisha Buhari da Yusuf Buhari sun tarbi tawagar bisa karamci da girmamawa.

Tsohuwar hadimar Buhari ta rubuta masa wasika

Mun ba ku labarin cewa tsohuwar hadimar Muhammadu Buhari, Lauretta Onochie ta rubuta wasika ga marigayin bayan wata daya da rasuwarsa.

Kara karanta wannan

Fitaccen dan kasuwa a Arewa kuma na kusa da marigayi Shehu Shagari ya rasu

Lauretta Onochie ta yi kukan yadda APC ta rasa adalci, gaskiya da nagartar da marigayin ya tsaya kai lokacin yana kan mulki.

Duk da korafe-korafenta, Madam Onochie ta ce mabiyan shugaba Buhari ba za su bar koyarwarsa ta gaskiya da rikon amana ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.