Lokaci Ya Yi: Jakadan Najeriya Ya Rasu, Ya Yi Mutuwar da ba a Yi Tsammani ba
- Karamin jakadan Najeriya a Jamhuriyar Kamaru, Taofik Obasanjo Coker ya rasu bayan fama da gajeruwar rashin lafiya
- Ma'aikatar harkokin kasashen waje ta Najeriya ce ta tabbatar da hakan a wata sanarwa da mai magana da yawunta, Kimiebi Imomotimi Ebienfa ya fitar
- Ya bayyana marigayin a matsayin dan kasa nagari, wanda ya yiwa kasarsa hidima a mukamai daban-daban da ya rike
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Karamin jakadan Najeriya a birnin Buea da ke jamhuriyar Kamaru, Ambasada Taofik Obasanjo Coker ya riga mu gidan gaskiya.
Ma’aikatar Harkokin Waje ta Najeriya ta tabbatar da rasuwar Taofik Obasanjo Coker bayan gajeruwar rashin lafiya, a wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba.

Source: UGC
Ta ce marigayi Coker ya rasu ba zato ba tsammani a ranar Asabar, 16 ga watan Agusta, lamarin da ya girgiza al’ummar diflomasiyya ta Najeriya, rahoton The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Karamin jakadan Najeriya a Kamaru ya rasu
A sanarwar, mai magana da yawun ma’aikatar, Kimiebi Imomotimi Ebienfa, ya bayyana marigayin a matsayin ɗan diflomasiyya wanda ya shafe tsawon shekaru yana yi wa ƙasarsa hidima da kwarewa, sadaukarwa da jajircewa.
Ebienfa ya ce:
“Rasuwarsa kwata'sam ba tare da an yi tsammani ba babban rashi ne ga iyalansa, abokansa, diflomasiyya da ƙasa baki ɗaya.
"Ambasada Coker mutum ne da ya sadaukar da rayuwarsa wajen kare martabar Najeriya a kasashen waje.”
Hidimar da ya yiwa Najeriya a rayuwarsa
Kafin nada shi a matsayin karamin jakadan Najeriya a Buea, Coker ya yi aiki a manyan ofisoshin jakadancin Najeriya da ke Conakry a Guinea da kuma Shanghai a kasar China.
Ya taka muhimmiyar rawa wajen karfafa dangantakar diflomasiyya da bunkasa hulɗar tattalin arziki tsakanin Najeriya da wadannan kasashe, rahoton Vanguard.
A cewar ma’aikatar, marigayi Coker ya kasance mai kishin kasa, kuma ya yi fice wajen kula da ’yan Najeriya mazauna kasashen da aka tura shi, musamman wajen kare muradunsu da tabbatar da kare ’yancinsu.
Ana ganin mutuwarsa a matsayin babban gibi da zai yi wuya a cike, musamman a wannan lokaci da Najeriya ke kara kokarin karfafa hulɗa da makwabtan kasashe da sauran kasashen duniya.
Ma'aikatar harkokin waje ta yi ta'aziyya
Ma’aikatar ta mika ta’aziyya ga iyalansa, abokan aikinsa da dukkan abokansa tare da addu’ar Allah ya jikansa, kuma Ya ba iyalansa hakuri da ƙarfin gwiwa don jure wannan babban rashi.
"Ma’aikatar Harkokin Waje tana mika ta’aziyyar ga iyalansa, abokan aiki da sauran abokan arziki a wannan lokaci mai wuya, tare da addu’ar samun hutu,” in ji sanarwar.
Hadimar gwamnan jihar Benuwai ta rasu
A wani labarin, kun ji cewa babbar mai ba gwamnan jihar Benuwai shawara ta musamman kan harkokin hulda da jama'a da siyasa, Mary Yisa ta mutu kwatsam.
Gwamnatin Jihar Benue ta yi ta’aziyya ga yan uwa da kuma dangin Mary Yisa, hadimar Gwamna Hyacinth Alia bisa wannan rashi da suka yi.
Ta bayyana Marigayiya Mary Yisa a matsayin jajirtacciyar ma’aikaciya, mai kishin ƙasa, kuma mace mai ƙarfin hali wadda ta yi wa jiharta hidima da zuciya daya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

