An Gama Shirye Shirye, Tsohon Gwamna Zai Zama Sabon Sarki Mai Martaba a Najeriya

An Gama Shirye Shirye, Tsohon Gwamna Zai Zama Sabon Sarki Mai Martaba a Najeriya

  • An shirya bikin nadin tsohon gwamnan jihar Oyo, Rashidi Ladoja a matsayin sabon Sarkin Ibadan watau Olubadan ranar 26 ga watan Satumba, 2025
  • Rahotanni daga jihar Oyo sun nuna cewa Gwamna Seyi Makinde ya amince da nadin Ladoja a matsayin Olubadan na 44
  • Wannan dai na zuwa ne bayan rasuwar tsohon Sarkin Ibadan, Oba Owolabi Olakulehin, a jihar da ke Kudu maso Yammacin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Oyo - Rahotanni daga jihar Oyo sun tabbatar da cewa kusan an kammala duk wasu shirye-shiryen nadin sabon Sarkin Ibadan mai cikakken tarihi.

Bayanai sun nuna cewa za a naɗa tsohon gwamna, Rashidi Ladoja a matsayin Olubadan na 44 na Ibadan, babban birnin jihar Oyo a ranar Juma'a 26 ga watan Satumba, 2025.

Oba Rashidi Ladoja.
Hoton tsohon gwamnan Oyo, Oba Rashidi Ladoja, wanda za a nada a matsayin Olubadan na 44 Hoto: Seyi Makinde
Source: Facebook

Gwamna Makinde ya amince da nadin Ladoja

Kara karanta wannan

IBB: Bayan cika shekara 84, Janar Babangida ya aika muhimmin sako ha 'yan Najeriya

Jaridar Tribune Online ta rawaito cewa gwamnan jihar Oyo, Injiniya Seyi Makinde, ya amince da nadin Oba Rashidi Ladoja a matsayin sabon Sarkin Ibadan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Za a yi wannan nadi ne a wani gagarumin biki da aka shirya yi ranar Juma'a, 26 ga watan Satumba, inda tsohon gwamnan zai hau karagar sarautar Olubadan na 44 a tarihi.

An tattaro cewa tuni tawagar gwamnatin jihar Oyo ta gana da Ladoja da sauran mambobin majalisar masarautar a gidansa da ke Bodija a ranar Laraba domin tattaunawa kan batun.

An sa ranar nada sabon Sarkin Ibadan

Yayin da aka tuntubi Mai taimaka wa Oba Ladoja kan harkokin yada labarai, Cif Adeola Oloko, ya tabbatar da hakan ga manema labarai.

Ya tabbatar da cewa Gwamna Makinde ya amince za a nada sabon Sarkin a watan Satumba mai zuwa.

“Za a naɗa Oba Ladoja a matsayin Olubadan na 44 na masarautar Ibadanland a ranar Jumma’a, 26 ga watan Satumba, 2025," in ji Cif Oloko.

An tsara gudanar da bikin nadin basaraken mai cike da tarihi a dakin taro na Mapo Hall da ke Ibadan.

Kara karanta wannan

2027: An hango wa Uba Sani matsala a Kaduna da jami'an gwamnati suka ajiye aiki

Sarki mai jiran gado ya gana da masu zabe

Rahoton jaridar Punch ya ƙara da cewa a ranar Talata, Ladoja ya gana da masu zaɓen sabon Sarki na masarautar Ibadan a gidansa da ke kan titin Ondo Street, Old Bodija, a karamar hukumar Ibadan ta Arewa.

Sarkin Ibadan mai jiran gado da Gwamna Makinde.
Hoton Olubadan na 44 mai jiran gado, Rashidi Ladoja, da Gwamna Seyi Makinde Hoto: Seyi Makinde
Source: Facebook

Wannan shi ne taron farko da aka yi tun bayan dawowar Ladoja, biyo bayan rasuwar tsohon Sarki, Owolabi Olakulehin, a Ibadan.

Taron ya gudana ne a sirrance kuma masu nadin Sarki sun shafe kusan sa'o'i biyu suna tattauna wa da Ladoja, amma ba a bayyana abin da suka maida hankali a kai ba.

Olubadan na 43 ya riga mu gidan gaskiya

A wani labarin, kun ji cewa Sarkin Ibadan, Oba Owolabi Olakulehin, ya rasu a ranar Litinin, 7 ga watan Yulin 2025, bayan sa'o'i 72 da cika shekaru 90 a duniya.

Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya nada marigayin a ranar 12 ga Yulin 2024, inda ya zama Sarkin Ibadan na 43 a wani gagarumin taro da aka shirya.

Mulkinsa ya kasance cike da zaman lafiya, hikima, da kuma kwazo ga ci gaban Ibadan, inda ya samu yabo daga shugabanni daban-daban ciki har da Bola Tinubu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262