Babbar Magana: Gwamnan Neja Ya Ce za Su Daina Tura Shanu Kudancin Najeriya

Babbar Magana: Gwamnan Neja Ya Ce za Su Daina Tura Shanu Kudancin Najeriya

  • Gwamnan Lagos, Babajide Sanwo-Olu ya ce Najeriya na asara mai yawa saboda fitar da amfanin gona ba tare da sarrafa su ba
  • Gwamnan Neja, Umar Bago ya ce za su daina tura shanu jihohin Kudu sai dai a sarrafa nama a kai musu domin amfani da shi
  • Sun bayyana haka a wani taro da ya tattauna dabarun bunkasa fitar da kayayyakin noma don rage dogaro da man fetur a Najeriya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Legas – Gwamnan Jihar Lagos, Babajide Sanwo-Olu, ya yi gargadi cewa Najeriya na ci gaba da asarar dimbin arziki saboda dogaro da fitar da kayayyakin noma ba tare da sarrafa su ba.

A yayin taron, gwamnan jihar Neja ya ce za su daina tura shanu da ransu zuwa wasu jihohin Kudu a nan gaba.

Kara karanta wannan

Mamakon ruwan ya lalata gidaje, ya raba mutane sama da 600 da muhallansu a Yobe

Ana kokarin loda shanu a mota domin tafiya da su wani gari
Ana kokarin loda shanu a mota domin tafiya da su wani gari. Hoto: Balogi Ibrahim|Getty Images
Source: Facebook

A sakon da ya wallafa a X, gwamna Sanwo-Olu ya ce matsalar na hana manoma samun karin riba da kuma hana kasar samun martaba a kasuwannin duniya.

Ya ce kasashen Afirka da dama na kara zage damtse wajen sarrafa kayayyakin noman su, yayin da Najeriya ke cigaba da fitar da kayayyakin, abin da ke rage alfanu da damar samar da ayyuka.

Jihar Neja za ta daina tura shanu Kudu

Gwamnan Jihar Nijar, Umar Bago, ya yi tsokaci a wajen taron inda ya ce kasashe da ke fitar da kayayyakin da ba a sarrafa ba su kan yi asarar tattalin arziki mai yawa.

PM News ta rahoto cewa Bago ya sanar da cewa jiharsa za ta daina kai shanu kai tsaye zuwa kasuwannin Lagos da Ogun da wasu jihohin Kudu.

Maimakon haka, ya ce za su sarrafa nama a cikin jihar sannan a kai daskararre zuwa Kudu maso Yamma.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta bude sabon shiri, za a hada matasa da masu daukar aiki a duniya

A cewar gwamna Umaru Bago, hakan zai ba manoma da makiyaya damar cin moriyar amfanin da suka yi.

Gwamna Umaru Bago da Sanwo Olu yayin taron da aka yi a Legas
Gwamna Umaru Bago da Sanwo Olu yayin taron da aka yi a Legas. Hoto: Lagos State Government
Source: Facebook

Bago ya kara da cewa Neja za ta kara yawan filayen gona da ta ware wa Lagos daga kadada 20,000 zuwa 100,000 domin kara inganta hadin kai wajen samar da abinci.

Kalubale a harkar fitar da amfanin gona

Gwamna Sanwo-Olu na jihar Legas ya ce duk da cewa Najeriya na kara fitar da amfanin gona a kowace shekara, har yanzu ana asara mai yawa ta tattali saboda rashin sarrafa kayayyakin.

Sanwo-Olu ya ce:

“Duniya ba za ta jira Najeriya ba, sauran kasashe suna daukar matakai wajen kare kasuwannin su da jawo masu zuba jari,"

Gwamnan ya ce gwamnatinsa ta zuba jari a bangaren hanyoyin sufuri, sauya tsarin tashoshin jiragen ruwa da kafa hanyoyin cinikayyar zamani ta intanet.

Sai dai duka da haka, ya ce babban kalubale shi ne rashin isasshen kudin lamuni ga manoma da masu fitar da kaya.

An hana motar Dangote wucewa a Edo

A wani rahoton, kun ji cewa wasu matasa a jihar Edo sun hana motocin Dangote wucewa a hanyar Auchi zuwa Benin.

Kara karanta wannan

Abba Gida Gida ya yi wa matasa albishir, ya faɗi tanadin da gwamnatinsa ta yi masu

Legit ta rahoto cewa mai fafutukar kare hakkin dan Adam da aka fi sani da VDM ne ya jagoranci tare hanyar.

Matasan sun bayyana cewa sun dauki matakin ne domin rage yawan haduran da suke zargin motocin Dangote da jawowa a hanyar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng