Bayan Kashe Masallata, 'Yan Bindiga Sun Sake Kona Mutane a Katsina

Bayan Kashe Masallata, 'Yan Bindiga Sun Sake Kona Mutane a Katsina

  • Mutanen karamar hukumar Malumfashi na ci gaba da kokawa kan yadda 'yan bindiga suka addabi kauyukan yankin da kai hare-hare
  • Dan majalisar da ke wakiltar mazabar Malumfashi, Hon. Aminu Ibrahim, ya bayyana cewa an tafka barna a cikin hare-haren da aka kai na baya-bayan nan
  • Ya bayyana cewa a wani harin da 'yan bindigan suka kai, sun cinnawa mutane wuta da ransu saboda rashin imani

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Katsina - Dan majalisar da ke wakiltar mazabar Malumfashi a majalisar dokokin jihar Katsina, Hon. Aminu Ibrahim, ya bayyana adadin mutanen da 'yan bindiga suka kashe a mazabarsa.

Hon. Aminu Ibrahim ya bayyana cewa adadin mutanen da ’yan bindiga suka kashe a hare-haren da suka kai a mazabarsa ya karu zuwa mutum 50.

'Yan bindiga sun kashe mutane a Katsina
Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, yayin da yake jawabi a wajen wani taro Hoto: Ibrahima Kaulaha Mohammed
Source: Twitter

A cikin wani bidiyo da shafin Facebook na Katsina State House of Assembly Media Centre ya sanya, an nuna dan majalisar yana jawabi ga takwarorinsa.

Kara karanta wannan

Sheikh Pantami ya nuna bacin rai kan an bindige Musulmai 27 suna salla a masallaci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan bindiga sun kashe mutane a Katsina

Mutanen an kashe su ne a hare-hare daban-daban da ’yan bindiga suka kai a ƙaramar hukumar Malumfashi ta jihar Katsina.

Hon. Aminu Ibrahim ya ce ’yan bindigan da ke dauke da makamai sun kashe masallata 30, sannan suka kone wasu mutum 20 da ransu a cikin sabbin hare-haren da aka kai a yankin nasa.

'Dan majalisar ya ce hare-haren da aka kai a Gidan Adamu Mantau, Unguwar Yar Mai Dabo, da kauyen Makera a gundumar Karfi, da kuma kauyen Burdigau a gundumar Yaba, sun bar jama’a cikin tsananin fargaba da bakin ciki.

A cewar Aminu Ibrahim, mazauna kauyukan sun sanar da ganin motsin ’yan bindiga a kusa da Burdigau tsakanin ƙarfe 6:00 zuwa 7:00 na yamma a ranar Litinin, amma sai daga baya sojoji suka iso, sannan suka janye ba tare da tabbatar da tsaro ba.

A cewarsa, da safiyar ranar Talata, ’yan bindigan suka kai farmaki a Unguwar Mantau, inda suka bindige masallata 30 a yayin sallar Asuba.

Kara karanta wannan

Yadda 'yan bindiga suka kashe masallata bayan sun bude musu wuta a masallaci

"Lamarin ya kai makura. Mutanenmu ba za su iya ci gaba da zama a kauyukansu ba saboda waɗannan hare-haren marasa karewa."

- Hon. Aminu Ibrahim

Dan majalisa ya koka kan halin rashin tsaro a Katsina
Hon. Aminu Ibrahim yayin wani zama a majalisar dokokin jihar Katsina Hoto: Katsina State House of Assembly Media Centre
Source: Facebook

An yi muhimmin kira ga gwamnatoci

Dan majalisar ya roki gwamnati da ta kafa sansanin tsaro na dindindin a gundumomin Karfi da Yaba.

Bayanin nasa dai ya tayar da hankalin ’yan majalisa kan yadda jinin al’ummar Katsina ke ta zuba duk da ayyukan sojoji da ake ci gaba da yi.

Mazauna Malumfashi sun yi kira ga gwamnatocin jiha da ta tarayya da su ɗauki matakin gaggawar kafin a rasa karin rayuka.

'Yan bindiga sun farmaki masallata

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hari kan masallata a jihar Katsina.

'Yan bindigan sun kai harin ne a kauyen Gidan Mantau lokacin da mutane ke.cikin masallaci suna yin sallar Asuba.

Majiyoyi sun bayyana cewa 'yan bindigan sun kashe akalla mutane 27, yayin da suka raunata wasu da dama.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng