IBB: Bayan Cika Shekara 84, Janar Babangida Ya Aika Muhimmin Sako ga 'Yan Najeriya

IBB: Bayan Cika Shekara 84, Janar Babangida Ya Aika Muhimmin Sako ga 'Yan Najeriya

  • Kwanan nan tsohon shugaban kasa a lokacin mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya cika shekara 84 a duniya
  • Janar Babangida (mai ritaya) ya bayyana cewa addu'o'in da Musulmai da Kiristoci suke yi, suna da tasiri sosai wajen hadin kan kasar nan
  • Tsohon sojan ya bukaci 'yan Najeriya da ka da su gajiya wajen ci gaba da sanya kasar nan cikin addu'a domin samun ci gaban ta

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Neja - Tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, ya ce addu’o’in Kiristoci da Musulmi ne suka haɗa kan kasar nan a wuri guda.

Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya roƙi mabiyan addinan biyu da kada su gaji da yi wa kasar nan addu’a.

Janar IBB ya shawarci 'yan Najeriya
Janar Ibrahim Badamasi Babangida a wajen taron kaddamar da littafinsa a Abuja Hoto: @DOlusegun
Source: Twitter

Janar Babangida ya faɗi haka ne a gidansa da ke Minna, babban birnin Jihar Neja, a ranar Talata, 19 ga watan Agustan 2025, cewar rahoton jaridar The Nation.

Kara karanta wannan

Isra'ila a Najeriya: Gumi ya ce a fara tsammanin kashe shugabanni Musulmai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon shugaban kasan ya karɓi tawagar kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) reshen jiha Neja, karkashin jagorancin shugaban ta, Archbishop Bulus Dauwa Yohanna.

IBB ya godewa shugabannin CAN

Janar Babangida ya nuna godiyarsa ga shugabannin addinin bisa ziyarar da suka kai masa da addu’o’in da suka yi musamman a zagayowar ranar haihuwarsa ta cika shekara 84.

"Ina matukar godiya ga CAN saboda addu’o’i. Dole na faɗa muku cewa addu’o’in mabiya addinai biyu, Kiristoci da Musulmai sun yi tasiri ƙwarai, kuma su ne suke rike da kasar nan."
"Ina rokonku ku ci gaba da wannan dangantaka don amfanin kasa da al’ummar ta gaba ɗaya.”

- Janar Ibrahim Badamasi Babangida

Wace shawara Janar Babangida ya ba da?

Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya kuma yi kira ga mabiyan addinan biyu da su ci gaba da rike kyakkyawar alaka da fahimtar juna, rahoton jaridar Independent ya tabbatar.

Ya jaddada cewa wannan shi ne mabuɗin zaman lafiya da ci gaban ƙasa.

Kara karanta wannan

Ansaru: Barnar da jagogorin yan ta'adda suka yi da ba ku sani ba kafin cafke su

"Ina so ku ci gaba da wannan alaka mai ɗorewa domin tana da matukar muhimmanci wajen inganta ci gabanmu a matsayin kasa. Haɗin kai da wanzuwar kasar nan suna hannun Kiristoci da Musulmai.”

- Janar Ibrahim Badamasi Babangida

Janar IBB ya ba da shawara ga 'yan Najeriya
Hoton Janar Ibrahim Badamasi Babangida a cikin gidansa Hoto: @ChucsEric
Source: Twitter

Janar IBB ya samu yabon CAN

A nasa jawabin, Bulus Dauwa Yohanna ya yaba wa irin hangen nesa da kishin zaman lafiya na Babangida, yana mai cewa rayuwarsa tana ci gaba da samun karin albarka ta soyayya da girmamawar ’yan ƙasa.

Shugaban na CAN, wanda mataimakinsa, Fasto Joshua Markus, ya wakilta, ya yaba da gudunmawowin da Babangida ya ba kasar nan, waɗanda har yanzu suna ci gaba da tasiri a fannoni daban-daban.

Ya yi addu’ar Allah ya ba tsohon shugaban kasan ƙoshin lafiya da farin ciki a shekaru masu zuwa, inda ya kara da cewa Najeriya da jihar Neja suna alfahari da shi.

Shugaba Tinubu ya ba dan IBB mukami

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya nada dan Janar Ibrahim Badamasi Babangida, mukami.

Shugaba Tinubu ya nada Muhammad Babangida a matsayin shugaban hukumar bankin noma (BoA).

Nadin na Muhammad Babangida na daga cikin nade-naden da Shugaba Tinubu ya yi na shugabannin hukumomin gwamnatin tarayya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng