An Bukaci a Kashe Bello Turji kamar Shekau duk da Ya Nemi Ya Mika Wuya
- Bashir Ahmad ya gargadi gwamnati da kada ta karɓi tayin sulhu daga ɗan ta’adda, Bello Turji da ya ce zai ajiye makamai
- Matashin 'dan siyasar bayyana cewa wannan furuci na Turji ya nuna ƙarshensa ya kusa, don haka bai kamata a yarda da shi ba
- A wata hira da Sheikh Murtala Bello Asada ya yi da shi, Turji ya tabbatar da shirinsa na mika makamai idan za a kyale su
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Tsohon mai taimaka wa Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad, ya bayyana cewa bai kamata gwamnati ta amince da tayin sulhun da Bello Turji ya yi ba.
Bashir ya bayyana hakan ne bayan rahotannin da suka fito na cewa Turji ya nuna niyyar ajiye makamai tare da yaransa, idan za a ba su damar zaman lafiya.

Source: Facebook
Hadimin marigayi shugaba Muhammadu Buhari ya fadi haka ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X.
Wannan batu ya sake tayar da muhawara a tsakanin al’umma game da makomar shirin sulhu da ’yan bindiga.
A cewarsa, wannan furuci na Turji ba komai ba ne illa alamar cewa ya fara fahimtar ƙarshen ta’addancinsa ya kusa.
Kalaman Bello Turji kan zaman lafiya
'Dan ta'addan ya yi magana ne a wata hira da ya yi da Sheikh Murtala Bello Asada, inda ya tambaye shi kan maganganun da ake yadawa cewa yana neman sulhu.
Legit Hausa ta rahoto cewa Turji ya amsa cewa shi da yaransa a shirye suke su mika makamai idan za a bar su su zauna lafiya.
Sai dai Sheikh Asada ya gargade shi cewa maganar sulhu ba wasa ba ce, kuma wannan karon ya kamata ya tabbatar da gaskiyar niyyarsa.
A bidiyon da Zagazola Makama ya wallafa a X, malamin ya yi kira gare shi da ya miƙa dukkan makaman da ke hannunsa a fili domin jama’a su tabbatar.

Source: Twitter
Gargadin Bashir kan sulhu da Turji
Bashir Ahmad ya ce kada gwamnati ta yi kuskuren shiga tattaunawar da ba ta da tushe da ɗan ta’addan.
Ya bayyana cewa ya kamata Turji ya gamu da irin sakamakon da jagororin Boko Haram, Mohammed Yusuf da Abubakar Shekau, suka gamu da shi.
A cewarsa, waɗannan mutane sun kafa tarihi na ta’addanci da barna a Najeriya, don haka bai kamata a ba duk wani mai bin sawunsu dama ba.
Bashir ya yi nuni da cewa tattaunawa da masu aikata miyagun laifuffuka a baya ba ta kawo ci gaba ba, illa ƙara basu ƙarfin guiwa wajen cigaba da barna.
An kashe masallata a jihar Katsina
A wani rahoton, kun ji cewa ana cigaba da nuna damuwa kan kisan gillan da wasu 'yan ta'adda suka yi wa Musulmai a wani masallaci a jihar Katsina.
Sheikh Isa Ali Pantami ya nuna damuwa kan yadda maharan suka kashe mutane ba tare da an samu nasarar kamo su ba.
Malamin ya bukaci hukumomi da masu ruwa da tsaki su yi amfani da fasaha wajen gano 'yan ta'addan da suka kai harin.
Asali: Legit.ng

