Yadda 'Yan Bindiga Suka Kashe Masallata bayan Sun Bude Musu Wuta a Masallaci
- Bayanai na ta fitowa kan yadda 'yan bindiga suka farmaki masallata a wani kauyen da ke garin Malumfashi a jihar Katsina
- Mutanen da suka tsira daga harin sun bayyana cewa suna cikin sallar Asuba kawai 'yan bindiga suka bude musu wuta
- Majiyoyi sun nuna cewa adadin mutanen da suka rasa ransu yayin harin ya kusa mutum 30, sabanin mutane 13 da gwamnati ta ce sun rasu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Katsina - Mutanen da suka tsira daga harin da 'yan bindiga suka kai a wani masallaci a jihar Katsina sun bayyana yadda lamarin ya auku.
Mutanen sun bayyana cewa ’yan bindigan sun kai musu farmakin ne da safiyar ranar Talata yayin da suke yin sallar Asuba.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ce wasu mazauna ƙauyen Gidan Mantau, wanda yake kasa da kilomita 10 daga garin Malumfashi, sun yi mata bayani kan lamarin.

Kara karanta wannan
Sheikh Pantami ya nuna bacin rai kan an bindige Musulmai 27 suna salla a masallaci
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda mummunan lamarin ya auku
Mutanen sun ce kusan mutum 23 ne suka mutu a sakamakon lamarin duk da cewa gwamnatin jihar ta ce mutum 13 ne suka rasu.
Haka kuma an tattaro cewa mutane da dama sun ji raunuka daban-daban sakamakon harin.
Lamarin ya faru ne kwana guda bayan Gwamna Dikko Umaru Radda ya fara hutun jinya na makonni uku, inda ya mika mulki ga mataimakinsa, Malam Faruk Lawal.
Wannan hari ya kuma biyo bayan wani makamancinsa da aka kai watanni 18 da suka gabata a lokacin da aka kai wa masallata farmaki yayin sallar Isha’i a ƙauyen Yargoje, karamar hukumar Kankara, a cikin Katsina.
'Yan bindiga sun budewa masallata wuta
Majiyoyi sun ruwaito wadanda suka tsira daga sabon harin cewa lamarin ya faru kimanin ƙarfe 5:00 na safe, jim kaɗan bayan da suka fara sallar Asuba.
"Suna cikin Sallah sai suka ji karar harbi. Sai suka kashe wasu mutane, suka kuma raunata wasu."
- Wata majiya
Maharan sun zo ne da nufin ramuwar gayya, bayan da mutanen yankin suka yi musu kwanton bauna, suka kashe da yawa daga cikinsu tare da kwace musu makamai da baburan da suke amfani da su wajen kai hare-hare.

Source: Original
Adadin mutanen da suka rasu na iya karuwa
Wani mazaunin kauyen wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce adadin waɗanda suka mutu na iya ƙaruwa, domin da yawa daga cikin wadanda suka jikkata an kai su asibiti cikin mawuyacin hali.
"Yawan mutanen da suka mutu ya karu zuwa 27 daga abin da muka ji game da wadanda aka kai asibiti."
- Wata majiya
'Dan majalisa ya koka kan hare-haren 'yan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa dan majalisar dokokin jihar Katsina da ke wakiltar Matazu, ya koka kan halin da mutanen mazabarsa suke ciki.
Hon. Ibrahim Umar Dikko ya bayyana cewa 'yan bindiga su mamaye mafi yawa daga cikin gundumomin da ke cikin mazabarsa.
Ya koka kan cewa 'yan bindigan suna hana mutane zuwa gonakinsu, yayin da suke kashe wadanda ba su san hawa ba, ba su san sauka ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
