An Yi Jana'izar Mahaifin Gwamma da Allah Ya Yiwa Rasuwa

An Yi Jana'izar Mahaifin Gwamma da Allah Ya Yiwa Rasuwa

  • A jiya Litinin ne Allah ya yi wa Alhaji Ahmed Momohsanni Ododo, mahaifin gwamnan jihar Kogi rasuwa
  • An gudanar sallar jana'izar marigayin bisa tsarin addinin musulunci a garinsu na Okene da ke jihar Kogi yau Talata
  • Manyan mutane ciki har da tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello, sarakuna da malamai sun halarci wurin jana'izar marigayin

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kogi - An gudanar da jana’izar marigayi Alhaji Ahmed Momohsanni Ododo, mahaifin Gwamnan Jihar Kogi, Alhaji Ahmed Ododo, a ranar Talata a garinsu na Okene.

Jana’izar ta tara jama’a da dama daga sassa daban-daban na Jihar Kogi da ma wajenta, abin da ya nuna irin mutunci da girmamawa da mahaifin gwamnan ke da shi a cikin al’umma.

Gwamna Ododo a wurin jana'izar mahaifinsa.
Hotunan yadda aka yi jana'izar mahaifin Gwamna Ododo da Allah ya karbi ransa a Okene Hoto: @GominaHabib
Source: Twitter

Tribune Nigeria ta ce an gudanar da jana’izar bisa tsarin Musulunci, inda jama’a da malamai da manyan baki suka taru domin yiwa mahaifin gwamnan addu'a.

Kara karanta wannan

Ajali ya yi: Hadimar gwamna ta rasu kwatsam, gwamnati ta tura sako ga iyalanta

An yiwa mahaifin gwamnan Kogi jana'iza

Babban Limamin Ebiraland, Sheikh Salihu Abere, ne ya jagoranci sallar janazar a garin Okene da ke jihar Kogi yau Talata, 19 ga watan Agusta, 2025.

A taƙaitaccen jawabin da ya yi bayan sallah, Babban Limami ya tunatar da jama’a game da ɗan gajeren lokacin da suke da shi a duniya, tare da yi wa Musulmi nasiha su rika rayuwa cikin tunawa da Allah a kodayaushe.

Sallar jana’izar ta samu halartar manyan malamai, daraktoci, dattawan al’umma da kuma manyan ’yan siyasa, abin da ya nuna irin zurfin dangantakar marigayin da addini da kuma zamantakewar al’umma.

Gwamna Ododo ya yi bakwana da mahaifinsa

Gwamnan Jihar Kogi, Alhaji Ahmed Ododo, ya halarci sallar tare da yin addu’a ga mahaifinsa, inda ya tsaya tare da malamai, ’yan uwa da dubban jama’a suna masa addu’a da ta’aziyya.

Mai Martaba Ohinoyin Ebiraland, Alhaji Dr. Ahmad Tijani Muhammed Anaje, ya halarci wurin jana'izar domin nuna girmamawarsa ga mahaifin Gwamna Ododo.

Kara karanta wannan

Isra'ila a Najeriya: Gumi ya ce a fara tsammanin kashe shugabanni Musulmai

Haka kuma malamai sun yi addu’ar Allah Madaukakin Sarki ya gafarta masa, ya ji ƙansa da rahama, ya yafe masa kura-kuransa, ya kuma saka shi da gidan Aljanna Firdausi, rahoton Daily Post.

Gwamna Ahmed Ododo.
Hoton Yahaya Bello, Ododo a wurin jana'izar mahaifin gwamnan Kogi Hoto: @GominaHabib
Source: Twitter

Manyan mutane sun halarci jana'izar

Daga cikin wadanda suka halarta akwai sarakuna, tsohon gwamna, Alhaji Yahaya Bello, da manyan jami’an gwamnati da dama, waɗanda suka je domin yi masa ban kwana na ƙarshe.

Marigayi Alhaji Ahmed Momohsanni Ododo ya kasance abin tunawa saboda gudummawar da ya bayar ga al’umma, kishinsa ga addinin Musulunci, da kuma kimarsa cikin al’ummarsa.

Dattijon Arewa, Alhaji Isiaku Ibrahim ya rasu

A wani labarin, kun ji cewa fitaccen ɗan kasuwa kuma dattijon Arewa, Alhaji Isiaku Ibrahim, ya rasu a asibiti a birnin tarayya Abuja.

Marigayin wanda ya kasance aboki kuma na kusa ga tsohon shugaban ƙasa, Shehu Usman Shagari ya rasu yana da shekara 88 a duniya.

An bayyana shi a matsayin ɗan siyasa gogagge wanda ya taka rawar gani wajen kafa jam’iyyar NPN a Jamhuriya ta biyu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262