Matan da Aurensu Ya Mutu Za Su Caba, Gwamna Ya Fara Biyan Zawarawa N15,000 duk Wata

Matan da Aurensu Ya Mutu Za Su Caba, Gwamna Ya Fara Biyan Zawarawa N15,000 duk Wata

  • Gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori ya kaddamar da shirin tallafawa zawara, inda mata 10,000 za au amfana da tallafa duk wata
  • Sheriff Oborevwori ya za a fara biyan kowace bazawara da aka dauka karkashin shirin N15,000 duk wata tare da inshorar lafiya
  • Ya ce matan da suka rasa mazajensu ta hanyar mutuwa ko rabuwar aure su na fama da matsin rayuwa da tsangwama daga al'umma

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Delta - Gwamnan Jihar Delta, Hon. Sheriff Oborevwori, ya ƙaddamar da shirin tallafin zawarawa 'Widows’ Welfare Scheme' domin tallafa wa matan da suka rasa mazajensu 10,000.

An gudanar da bikin ƙaddamarwar a wani dakin taro da ke Asaba, babban birnin jihar Delta, wani bangaren matakin aiwatar da Ajendar MORE da gwamnan ya bullo da ita.

Gwamna Oborevwori na jihar Delta.
Hoton Gwamna Sheriff Oborevwori na jihar Delta yana aiki a ofishinsa da ke fadar gwamnati Hoto: Sheriff Oborevwori
Source: Facebook

Gwamnan Oborevwori ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Litinin, 18 ga watan Agusta, 2025.

Kara karanta wannan

Gidaje miliyan 2.2 za su samu kudi a sabon shirin tallafin gwamnatin Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan matakin wani bangare ne na alkawuran da ya yi a lokacin yaƙin neman zaɓe na kafa gwamnatin da za ta jawo kowa a jikinta.

Za a rika ba zawarawa tallafin N15,000

A wajen taron, Gwamna Oborevwori ya bayyana cewa, a karkashin shirin, kowace bazawara za ta rika karɓar tallafin kuɗi na ₦15,000 a duk wata, wanda za a riƙa biya kai tsaye cikin asusun bankinsu.

Ya ce za fara ba da tallafin nan take, inda kowace mai cin gajiyar shirin za ta karɓi ₦45,000 na watanni uku a matsayin biyan bashi.

Baya ga tallafin kuɗi, zawarawa 10,000 na rukunin farko, za a saka su cikin Shirin Inshorar Lafiya na Jihar Delta domin ba su damar samun kulawa kyauta a asibitoci da cibiyoyin lafiya na gwamnati.

Sheriff Oborevwori ya tuna yadda ya dade yana kula da zawarawa tun kafin zama gwamna da kuma a lokacin da ya hau kujerara shugabanci.

Kara karanta wannan

Wuraren da suka halatta saurayi ya kalla a jikin macen da zai aura a Musulunci

Gwamna ya tausayawa matan da ke zawarci

Ya bayyana rayuwar zawarci a matsayin halin baƙin ciki da jarabawa, yana mai jaddada cewa mafi yawan zawarawa kan shiga cikin ƙuncin rayuwa bayan mutuwar aurensu.

Oborevwori ya ce:

“Zama bazawara ba zaɓi ba ne, kuma ba zai taɓa zama zaɓin kowa ba. Bayan ciwon rasa masoyi, zawarawa kan fuskanci nauyin dogaro da kai. Shi ya sa wannan gwamnati ta kuduri aniyar inganta rayuwarsu.”
Gwamnan Delta da zawarawa.
Hoton zawara suna murna da sabon shirin da zai taimaka masu a taron da Gwamna Sheriff ya kaddamar a Delta Hoto: Rt. Hon. Sherrif Oborevwori
Source: Facebook

Zawarawa za su samu inshorar lafiya a Delta

Ya ƙara da cewa wannan shiri na daga cikin ginshiƙan ajendarsa ta MORE, wato Slsamar da dama ga kowa, kamar yadda Leadership ta kawo.

“Inshorar lafiya da muke ba ku ta fi muhimmanci fiye da tallafin kuɗin, saboda tana tabbatar da cewa ba a hana kowace bazawara magani saboda ƙarancin kuɗi ba,” in ji shi.

Gwamnan ya yi bayani cewa babu siyasa a cikin wannan shiri, kuma ya shafi dukkan addinai da kabilu a Jihar Delta.

Gwamnan Delta ya yi barazanar korar kwamishinoni

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta bude sabon shiri, za a hada matasa da masu daukar aiki a duniya

A wani rahoton, kun.ji cewa Gwamna Oborevwori Dgargaɗi kwamishinonin Delta cewa ba zai iya ci gaba da aiki da waɗanda ba sa nuna ƙwazo a bakin aiki ba.

Gwamnan ya musanta rade-radin da ake yadawa cewa yana shirin sallamar duka kwamishinoninsa amma ya jaddada cewa ba zai lamurci lalaci ba.

Ya buƙaci kwamishinoni su zama masu ƙirƙirar sababbin hanyoyin ci gaba, su samar da dabarun inganta harkokin gwamnati domin taiamakawa talakawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262