Kano: Yan Sanda Sun Burma Matsala bayan Taimakon Ɗan Siyasa Yana Rabon Kuɗi

Kano: Yan Sanda Sun Burma Matsala bayan Taimakon Ɗan Siyasa Yana Rabon Kuɗi

  • Rundunar ’yan sandan Kano ta tabbatar da ɗaukar matakin ladabtarwa kan jami’anta guda biyar a jihar da ake zargi da saba doka
  • Rundunar ta ce jami'an su ne aka gani suna taimakawa ɗan siyasa wajen rabon kuɗi a wani bidiyo wanda mutane suka yi ta magana a kai
  • Rahoton ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar 10 ga Yuli 2025 a wani taro a gidan gwamnatin Kano, ba a lokacin zaɓe ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta yi karin haske kan bidiyon wasu jami'anta biyar da ake yadawa.

Rundunar ta tabbatar da cewa an ɗauki matakin ladabtarwa a kan jami’an da ke taimakawa dan siyasa wajen rabon kuɗi.

Yan sanda za su ladabtar da jami'ansu 5 a Kano
Kakakin yan sanda a Kano, ASP Abdullahi Haruna Kiyawa yana jawabi a hedkwatar rundunar. Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa.
Source: Facebook

Hakan na cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar ranar Talata 19 ga watan Agustan 2025 a shafin Facebook.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Ƴan sa kai sun yi wa ƴar bautar ƙasa tsirara, sun lakaɗa mata dukan tsiya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kano: Bidiyon 'yan sanda da ya jawo magana

Ganin bidiyon yan sanda ya tayar da kura inda aka yi ta kiran rundunar ta dauki mataki kan jami'anta biyar da aka gano.

Babban abin da ya fi daukar hankali game da bidiyon shi ne mutane sun yi zargin lamarin ya faru ne a lokacin zaben cike gurbi a Kano.

Hukumar zabe mai zaman kanta, INEC ta gudanar da zaɓen cike gurbin ne a jihohi 13 a ranar Asabar 16 ga watan Agustan 2025.

Karin bayani daga 'yan sanda a Kano

Rundunar yan sanda ta bakin Kiyawa ta ce bincike ya gano lamarin ya faru ne a ranar 10 ga watan Yuli 2025 a taron gidan gwamnatin Kano bayan wani biki.

Kiyawa ya tabbatar da cewa ba a lokacin zaɓen cike gurbi da aka gudanar a 16 ga watan Agusta abin ya faru ba kamar yadda ake yadawa.

Kara karanta wannan

Abubuwan 'tashin hankali' da aka gano a hannun mutane 333 da aka kama a zaben Kano

An gano yan sanda biyar a wani bidiyo suna taimakawa wani ɗan siyasa wajen raba kuɗi ga jama’a a bainar jama’a, abin da ya jawo surutu.

Yan sanda za su ladabtar da jami'anta a Kano
Taswirar jihar Kano da ke Arewa maso Yamma a Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Alkawarin yan sanda ga al'ummar Kano

Binciken ya gano cewa an tura jami’an ne domin tsaron wurin taron, amma abin takaici an gan su a cikin bidiyon suna aikata abin da bai dace ba a matsayin jami’an tsaro.

Sanarwar ta ce:

"Rundunar ’yan sandan ta ƙara tabbatar da cewa tana da cikakken niyyar tabbatar da ladabtarwa, bin ƙa’ida da tsarin aikin ’yan sanda.
"Ta ce za ta tabbatar da aminci a tsakanin al'umma game da rundunar da kare martabar hukumar a yayin ayyukansu."

Kisan DPO: 'Yan sanda sun kama wanda ake zargi

Kun ji cewa rundunar ‘yan sandan Kano ta tabbatar da kisan DPO na Rano, CSP Baba Ali, a yayin da yake bakin aikinsa a yankin.

Bayan binciken gaggawa, an cafke mutane 41 da ake zargi da hannu a kisan, ciki har da wanda ake zargi ya jagoranci aikata laifin.

Kwamishinan ‘yan sanda ya tabbatar da cewa za a tabbatar da hukunta wadanda suka aikata wannan danyen aikin a kan lokaci ba tare da bata lokaci ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.