Bidiyo: Ƴan Sa Kai Sun Yi wa Ƴar Bautar Ƙasa Tsirara, Sun Lakaɗa Mata Dukan Tsiya
- 'Yan sa kai na Agunechemba sun kai samame gidan ƴan NYSC inda suka lakadawa wata Jennifer Elohor duka tare da yi mata tsirara
- Bidiyon da ya yadu a soshiyal midiya ya nuna lokacin da ƴan sa-kan suka farmaki gidan, suna zargi 'yan bautar kasar da laifin damfara
- Lamari ya haifar da ce-ce-ku-ce, inda daga baya gwamnatin jihar Anambra ta tabbatar da cewa kama jami’an da suka aikata cin zarafin
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Anambra - Wasu jami'an tsaron Agunechemba (ƴan sa kai) sun yi wa wata ƴar bautar ƙasa mai suna Jennifer Edema Elohor tsirara a Anambra.
Wani bidiyo da ya bazu a shafukan sada zumunta ya nuna lokacin da ƴan sa kan suka rika dukan Jenniffer Elohor, har ta kai sun yi mata tsirara.

Source: Getty Images
Ƴan sa-kai sun farmaki gidan 'yan NYSC
Jaridar Punch ta rahoto cewa (ƴan sa kan da ake kyautata zaton jami’an Operation Udo Ga-Achi, ne sun kai samame dakin kwanan 'yan bautar kasa na jihar, inda abin ya faru.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bidiyon, wanda Gidauniyar Haven 360 ta wallafa a Facebook ranar Litinin, ya nuna yadda aka lakada wa Jennifer Elohor duka tare da cire mata kaya, yayin da jami'an ke ɗauke da bindigogi.
Gidauniyar ta bayyana cewa an yi wa masu bautar kasar duka, an jefa su a cikin wani yanayi na tsantsar wulakanci, har ma da barazanar lalata.
An ce ƴan sa kai sun zargi masu bautar kasar a karkashin NYSC da ayyukan damfara (Yahoo-Yahoo), kuma sun ci zarafinsu duk da cewa sun nuna katin shaidar aikin NYSC ɗin su.
Bidiyon ƴan sa-kai na dukan ƴan NYSC
Gidauniyar ta ce:
“Mun daga murya tare da la’antar wannan mummunan cin zarafi da tauye hakkin ƴan NYSC da jami’an Operation Udo Ga-Achi (Agunechemba) suka yi a Anambra.
“Ranar 23 ga Yuli, 2025, waɗannan ƴan sa kan suka kai hari dakin zaman ƴan bautar kasar, inda suka zarge su da zama ƴan Yahoo, duk da cewa nan take suka nuna katin shaidarsu da kayansu na NYSC.
“An fi gallaza wa Jennifer Edema Elohor, inda aka doke ta, aka cire mata kaya, suka yi mata tsirara, kuma suka yi mata jina-jina.
Kalli bidiyon a nan kasa:

Source: Facebook
An kama waɗanda suka kai harin
Wannan hari ya jawo fushi a kafafen sada zumunta, inda ƴan Najeriya da dama suka la’anci abin da ƴan sa kan suka yi tare da neman a samar da adalci ga waɗanda abin ya shafa.
A hira da Channels Television ranar Talata, mai ba gwamnan Anambra, Chukwuma Soludo, shawara kan tsaron al’umma, Ken Emeakayi, ya bayyana wannan lamari a matsayin abin takaici kuma abin ƙi.
Ya tabbatar da cewa an kama jami’an da suka yi wannan aika-aikar kuma ana gudanar da bincike a kansu.
Malamai sun zane 'yar bautar kasa a Kwara
A wani labarin, mun ruwaito cewa, wasu malaman makaranta sun doki matashiya mai bautar ƙasa saboda ta gagara gaishe su yadda ya kamata.
Matashiyar da ba a bayyana sunanta ba ta gamu da tsautsayin ne a makarantar sakandare da ke Kulende a Ilorin da ke jihar Kwara.
Hukumar da ke kula da matasa masu yiwa kasa hidima (NYSC) ta tabbatar da faruwar lamarin inda ta sha alwashin daukar mataki kan cin zarafin.
Asali: Legit.ng


