Najeriya Ta Gaza Hakuri, Za Ta Buga da Kasar Amurka kan Sabuwar Dokar Biza

Najeriya Ta Gaza Hakuri, Za Ta Buga da Kasar Amurka kan Sabuwar Dokar Biza

  • Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa za ta ɗauki irin matakin da Amurka ta ɗauka kan tsarin neman biza
  • Amurka ta sanar da cewa duk mai neman biza daga Najeriya dole ya bayyana bayanan kafofin sada zumunta na tsawon shekara biyar
  • Ma’aikatar Harkokin Waje ta Najeriya ta ce za ta yi taro da hukumomi domin tsara yadda za a aiwatar da matakin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Sabon tsarin neman bizar Amurka ya jawo ce-ce-ku-ce a Najeriya bayan da hukumomi suka kawo sababbin dokoki.

Amurka ta ce dole ne masu neman biza daga Najeriya su bayyana dukkan bayanan kafofin sada zumunta da suka yi amfani da su a tsawon shekara biyar da suka gabata.

Ministan harkokin wajen Najeriya, Yusuf Tuggar da shugaba Donald Trump
Ministan harkokin wajen Najeriya, Yusuf Tuggar da shugaba Donald Trump. Hoto: Federal Ministry of Foreign Affairs|Getty Images
Source: Twitter

A sakon da ta wallafa a X, Amurka ta ce matakin na cikin tsarin tantance mutane da sahihancin bayanan masu neman bizar.

Kara karanta wannan

An jero wuraren da aka samu matsala a zaben cike gurbin da aka yi a Kano da waau jihohi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa ba za ta yi shiru game da wannan doka ba, domin za ta ɗauki irin matakin ga duk wani ɗan ƙasar Amurka da ke neman biza a Najeriya.

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Waje, Kimiebi Ebienfa, ne ya bayyana wannan a ranar Litinin, inda ya ce gwamnati ta riga ta samu sanarwa daga Amurka kafin aiwatar da matakin.

Sabon tsarin neman bizar Amurka

Amurka ta ce daga yanzu duk wanda ke neman bizar ƙasar dole ne ya cike fom na DS-160 tare da lissafa dukkan asusun kafofin sada zumunta da ya taɓa amfani da su a tsawon shekara biyar.

An ce duk wanda ya boye bayanan zai iya fuskantar ƙin amincewa da neman bizarsa, tare da rasa damar sake neman biza nan gaba.

Hukumomin Amurka sun yi gargadin cewa yana da muhimmanci masu neman biza su fadi bayanai na gaskiya.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Najeriya ta biya wa Kiristoci rabin kudin kujerar ziyara zuwa Isra'ila

Wannan ya sa suka jaddada cewa duk wani ɓoye bayani ko karya na iya zama babban ƙalubale ga mai neman biza.

Martanin gwamnatin Najeriya ga Amurka

Punch ta ce gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa za ta ɗauki matakin daidai da abin da Amurka ta yi.

Ebienfa ya bayyana cewa duk ɗan ƙasar Amurka da ke neman biza a Najeriya zai fuskanci irin dokar.

Vanguard ta wallafa cewa ya ce zai zama wajibi a bayyana dukkan bayanan kafofin sada zumunta na shekara biyar.

Ya ce gwamnati za ta gudanar da taro tsakanin hukumomin da abin ya shafa, ciki har da Ma’aikatar Harkokin Waje, Ma’aikatar Cikin Gida da kuma Hukumar Tsaro ta NIA.

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu yayin wani taro a kasar waje
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu yayin wani taro a kasar waje. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Tsarin hadin gwiwa tsakanin hukumomi

Ebienfa ya bayyana cewa tattaunawar za ta kasance ne domin tabbatar da cewa matakin da Najeriya za ta ɗauka ya yi daidai da bukatun tsaro da tsarin diflomasiyya.

Ya ce taron zai tabbatar da cewa dukkan hukumomin da abin ya shafa sun amince da tsarin aiki guda ɗaya.

Amurka da Birtaniya sun yaba wa Najeriya

Kara karanta wannan

Abba Gida Gida ya yi wa matasa albishir, ya faɗi tanadin da gwamnatinsa ta yi masu

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatocin Amurka da Birtaniya sun yaba wa Najeriya kan kama shugabannin 'yan ta'adda.

A makon da ya wuce mai ba shugaban Najeriya shawara kan tsaro, Malam Nuhu Ribadu ya sanar da cafke shugabannin 'yan ta'addan Ansaru.

Amurka ta ce kama shugabannin mataki ne babba wajen samun nasara a yaki da ta'addanci da masu tayar da kayar baya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng