Gidaje Miliyan 2.2 za Su Samu Kudi a Sabon Shirin Tallafin Gwamnatin Tinubu

Gidaje Miliyan 2.2 za Su Samu Kudi a Sabon Shirin Tallafin Gwamnatin Tinubu

  • Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa za ta raba tallafin kuɗi na gaggawa ga gidaje miliyan 2.2 a ƙarshen watan Agusta
  • Tanko Sununu ya bayyana cewa an riga an fitar da sunayen talakawa a rijistar kasa ta jin kai domin shiga shirin
  • Ya kuma ce gwamnati na ci gaba da tallafawa manoma da iyalai da bala’o’i suka shafa ta hanyar lamuni da wasu tsare-tsare

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Karamin Ministan harkokin jin kai da rage talauci, Tanko Sununu, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya za ta fara rabawa gidaje miliyan 2.2 tallafin kuɗi kafin ƙarshen Agusta.

Ministan ya ce shirin zai gudana ne karkashin tsarin rijistar kasa ta tallafi, inda za a zaɓo talakawa da marasa galihu mafi rauni domin amfana da shirin.

Kara karanta wannan

Wuraren da suka halatta saurayi ya kalla a jikin macen da zai aura a Musulunci

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu yana jawabi a wani taro da ya je Katsina
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu yana jawabi a wani taro da ya je Katsina. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Vanguard ta wallafa cewa ya ƙara da cewa an riga an raba fiye da Naira biliyan 419 ga kusan mutane miliyan 5 a cikin shirin tallafin kuɗi, wanda ya fi yawa a Arewa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Za a raba tallafi ga gidaje miliyan 2.2

A cikin hirar da aka yi da shi, Sununu ya bayyana cewa za a fara isar da tallafin kuɗi nan da ‘yan kwanaki, kafin ƙarshen watan nan.

Ya ce:

“Shirin na gaba zai shafi gidaje miliyan 2.2, kuma tsarin NASSCO zai ɗebo sunayen talakawa daga rijistar kasa bisa matsayin da su ke a cikin marasa galihu.”

Ya ce shirin na nufin ba wa talakawa damar samun sauƙi a cikin mawuyacin halin tattalin arziki da ake ciki, domin kula da rayuwar su da ta ‘ya’yansu.

Matsalar karancin tallafi a Najeriya

Sununu ya nuna damuwa kan halin da ake ciki na rashin tallafi, inda ya ce mutane fiye da miliyan 3 sun rasa matsuguni sakamakon ambaliyar ruwa, rashin tsaro da bala’o’i da dama.

Kara karanta wannan

Alhaki ya kama su: 'Yan bindiga sun yi hadari bayan karbo makudan kudin fansa

This Day ta wallafa cewa ya ce:

“Tallafin agaji na duniya na ƙara raguwa, lamarin kuma zai shafi Najeriya.
"A ‘yan kwanakin nan, Hukumar Abinci ta Duniya ta dakatar da wasu ayyuka da suka tallafa wa fiye da mutane miliyan 1.2 a Arewa maso Gabas.
"Wannan ya bar fiye da yara 300,000 cikin hadarin rashin abinci mai gina jiki.”

Ministan ya yi gargadin cewa idan aka bar al’amura haka, miliyoyin ‘yan kasa na iya shiga cikin yunwa da talauci mai tsanani.

Karamin ministan jin kai, Tanko Sununu a wajen wani taro
Karamin ministan jin kai, Tanko Sununu a wajen wani taro. Hoto: Aso Rock Villa
Source: Twitter

Tallafin gwamnati ga manoma da gidaje

Ya ce gwamnati na amfani da shirin NSIP wajen ba da lamuni ga manoma domin farfado da rayuwarsu, inda kowannensu ke samun N300,000.

Haka kuma, ya tabbatar da cewa sama da gidaje miliyan 5.9 sun ci gajiyar tallafin kuɗin da aka rarraba.

Ya ce:

“Wannan wani bangare ne na alkawarin Shugaba Bola Tinubu na tabbatar da cewa ‘yan Najeriya na ci gaba da samun mutunci da rayuwa duk da kalubalen tattalin arziki.”

Kara karanta wannan

Gwamnatin Najeriya ta biya wa Kiristoci rabin kudin kujerar ziyara zuwa Isra'ila

Gwamnati za ta tallafawa iyayen dalibai

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta kawo shiri na musamman domin mayar da yara makaranta.

A karkashin shirin, gwamnati za ta rika ba iyaye mata tallafi domin karfafa musu gwiwa wajen tura 'ya'yansu makaranta.

Haka zalika, gwamnatin ta kara adadin kudin da dalibai za su rika samu a matsayin tallafin karatu a matakai daban daban.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng