Ajali Ya Yi: Hadimar Gwamna Ta Rasu Kwatsam, Gwamnati Tura Sako ga Iyalanta

Ajali Ya Yi: Hadimar Gwamna Ta Rasu Kwatsam, Gwamnati Tura Sako ga Iyalanta

  • Gwamnatin Benuwai ta gabbatar da rasuwar babbar mai ba gwamna shawara kan harkokin hulda da jama'a da siyasa, Mary Yisa
  • Sakataren gwamnatin jihar, Serumun Aber ya ce mutuwar hadimar gwamnan kwatsam ya jefa abokan aikinta da dangi cikin bakin ciki
  • a mika sakon ta'aziyya ga iyalan marigayiya Mary Yisa da yan uwanta, tare da addu'ar Allah sa ta huta har abada

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Benue - Babbar mai ba gwamnan jihar Benuwai shawara ta musamman kan harkokin hulda da jama'a da siyasa, Mary Yisa ta riga mu gidan gaskiya.

Gwamnatin Jihar Benue ta yi ta’aziyya ga yan uwa da kuma dangin Mary Yisa, hadimar Gwamna Hyacinth Alia bisa wannan rashi da suka yi ba zato ba tsammani.

Gwamna Alia na jihar Benue.
Hoton gwamnan jihar Benuwai yana jawabi ga manema labarai a fadar gwamnati Hoto: Fr. Hyacinth Lormem Alia
Source: Facebook

Leadership ta tattaro cewa hakan na kunshe ne a wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar Benue (SSG), Serumun Aber, ya fitar a Makurdi.

Kara karanta wannan

'Gwamnan CBN na iya fin shugaban kasa albashi,' Gwamnati za ta kara wa jami'ai kudi

Ya bayyana Marigayiya Mary Yisa a matsayin jajirtacciyar ma’aikaciya, mai kishin ƙasa, kuma mace mai ƙarfin hali wadda ta yi wa jiharta hidima da gaskiya, tawali’u da zuciya ɗaya.

Hadimar gwamnan Benuwai ta rasu

A rahoton AIT, Mista Aber ya ce:

“A madadin gwamnati da mutanen Jihar Benue, muna miƙa ta’aziyyarmu ga dangin Mary, mai bai wa gwamna shawara ta musamman kan harkokin siyasa da hulda da jama'a, wadda rasuwarta ta jefa mu cikin baƙin ciki.
"Mary Yisa jajirtacciyar ma’aikaciyar gwamnati ce, mai kishin ƙasa, kuma mace mai ƙarfin hali wadda ta yi wa jiharmu hidima da gaskiya, tawali’u da zuciyar jin ƙai.
"Za a ci gaba da tunawa da gudummawar da ta bayar a harkokin mulki da ci gaban Jihar Benuwai tare da yiwa Allah godiya bisa rayuwar da ta yi."

Gwamnatin Benue ta yiwa mamaciyar adddu'a

Serumun Aber ya bayyana cewa rasuwar hadimar gwamnan kwatsam ta girgiza gwamnatin jihar Benuwai da mutanen da ta taimaka a rayuwa.

Kara karanta wannan

Ambaliyar ruwa ta lalata gidaje da gonaki a Kebbi, gwamnati ta ba da tallafi

"Mutuwar Yisa kwatsam babban rashi ne, ba ga iyalinta kaɗai ba, har ma ga gwamnatin Jihar Benue da mutanen da ta yi wa taimaka ta hanyoyi daban-daban.
"Yayin da muke jimamin wannan babban rashi, muna kuma alfahari gaskiyar cewa ta rayu rayuwa mai tasiri, cike da hidima da sadaukarwa ta alheri ga kowa.
"Muna addu’a, Allah cikin rahamarsa mara iyaka Ya ba iyalinta da abokan aiki da masoya juriya, Ya kuma jikan ta da rahama Ya sa ta huta har abada.”

- Serumun Aber.

Mahaifin gwamnan jihar Kogi ya rasu

A baya, mun kawo maku labarin cewa mahaifin Gwamna Ahmed Usman Ododo na jihar Kogi, Ahmed Momohsani Ododo ya riga mu gidan gaskiya ranar Litinin, 18 ga watan Agusta, 2025.

Kwamishinan yada labarai da sadarwa na jihar Kogi, Hon. Kingsley Femi Fanwo ne ya tabbatar da wannan rasuwa a wata sanarwa, ya ce an shirya masa jana'iza bisa tsarin musulunci.

Fanwo ya bayyana jimaminsa tare da addu'ar Allah Ya gafarta wa marigayin kura-kuransa, Ya kuma sanya shi a gidan Aljannah Firdaus.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262