Kwana Ya Kare: Mahaifin Gwamna Ya Riga Mu Gidan Gaskiya Yana da Shekaru 83

Kwana Ya Kare: Mahaifin Gwamna Ya Riga Mu Gidan Gaskiya Yana da Shekaru 83

  • Mahaifin Gwamna Ahmed Usman Ododo na jihar Kogi, Ahmed Momohsani Ododo ya riga mu gidan gaskiya yau Litinin, 18 ga watan Agusta, 2023
  • Gwamnatin jihar Kogi ta tabbatar da rasuwar mahaifin gwamnan a wata sanarwa da ta fitar, ta ce ya rasu yana da shekaru 83 a duniya
  • Sanarwar ta bayyana cewa za a yi jana'izar marigayin kamar yadda addinin musulunci ya tanada, ta yi addu'ar Allah ya gafarta masa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kogi - Gwamnan jihar Kogi da ke Arewa ta Tsakiya a Najeriya, Alhaji Ahmed Usman Ododo ya rasa mahaifinsa.

Rahotanni daga gwamnatin jihar Kogi sun tabbatar da cewa mahaifin Mai girma gwamna, Alhaji Ahmed Momohsani Ododo ya riga mu gidan gaskiya.

Gwamna Ahmed Usman Ododo.
Hoton gwamnan jihar Kogi, Ahmed Usman Ododo a fadar gwamnatinsa Hoto: @horiiyomi
Asali: Twitter

Mahaifin gwamnan jihar Kogi ya rasu

Kara karanta wannan

Zuru: Fitaccen Sarki a Arewacin Najeriya ya rasu yana da shekaru 81 a duniya

Jaridar Tribune Nigeria ta tattaro cewa mahaifin gwamnan ya rasu yana da shekara 83 a duniya yau Litinin, 18 ga watan Agusta, 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamishinan yada labarai da sadarwa na jihar Kogi, Hon. Kingsley Femi Fanwo ne ya tabbatar da wannan rasuwa a wata sanarwa da ya fitar a yau Litinin.

A sanarwar, wacce ya raba wa manema labarai a Lokoja, babban birnin jihar Kogi, kwamishinan ya ce za a gudanar da jana'izar marigayin kamar yadda addinin musulunci ya tanata.

An shirya jana'izar marigayin a Kogi

Sanarwar ta ce:

“Gwamnatin Jihar Kogi na bakin cikin sanar da rasuwar mahaifin Gwamnan Jihar Kogi, marigayi Alhaji Ahmed Momohsani Ododo.
"Mahaifin mai girma gwamna ya koma ga Mahaliccinsa ne a ‘yan sa’o’in da suka gabata (a yau Litinin, 18 ga watan Agusta, 2025) yana da shekara 83 da haihuwa.
"Za a gudanar da jana’izarsa tare da birne shi a makwancinsa bisa tsarin addinin Musulunci.

Kara karanta wannan

Fitaccen dan kasuwa a Arewa kuma na kusa da marigayi Shehu Shagari ya rasu

Gwamnatin Kogi ta yi addu'ar Allah ji kansa

Kingsley Femi Fanwo ya bayyana jimaminsa tare da addu'ar Allah Ya gafarta wa marigayin kura-kuransa, Ya kuma sanya shi a gidan Aljannah Firdaus, rahoton Leadership.

Haka nan kuma ya roki Allah Ya bai wa Mai girma Gwamna Ahmed Ododo da iyalansa da duka yan uwa da abokan arziki karfin jure wannan rashi da suka yi.

“Muna roƙon Allah Madaukakin Sarki Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya karɓi ayyukansa na alheri, Ya kuma sanya shi a cikin Aljannah Firdaus.
"Haka kuma, muna roƙon Allah Ya ba wa Gwamna Ahmed Ododo, iyalansa da dukan dangin gidan Ododo ƙarfin zuciya wajen jure wannan babban rashi," in ji sanarwar.
Mahaifin gwamnan Ododo.
Hoton marigayi Alhaji Ahmed Momohsani Ododo, da dansa gwamnan Kogi na yanzu Hoto: @Dr_A_Muatapha
Asali: Twitter

Mai Martaba Sarkin Zuru ya kwanta dama

A wani labarin, kun ji cewa Sarkin Zuru, Mai Martaba Janar Muhammad Sani Sami Gomo II (rtd), ya rasu yana da shekara 81 a duniya bayan fama da jinya.

Kara karanta wannan

Lokaci ya yi: Tsohon sakataren jam'iyyar PDP na kasa ya riga mu gidan gaskiya

Rahotanni daga fadar sarkin da ke jihar Kebbi ta tabbatar da cewa mai martaba ya rasu ne a ranar Asabar da ta gabata a wani asibiti da ke birnin Landan a Birtaniya.

An haife shi a Zuru, inda ya shiga aiki a rundunar soji a ranar 10 ga Disamba 1962, ya samu horo a gida da waje, har ya kai ga zama gwamnan Bauchi na mulkin soji a 1983.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262