An Yi Rashi: Shugaban Jam'iyyar PDP Na Farko Ya Yi Bankwana da Duniya a Edo

An Yi Rashi: Shugaban Jam'iyyar PDP Na Farko Ya Yi Bankwana da Duniya a Edo

  • Jam'iyyar PDP a jihar Edo ta rasa daya daga cikin mutanen da suka taba jagorantarta, bayan ya koma ga Mahaliccinsa
  • Mukaddashin PDP na Edo, Anthony Aziegbemi, ya sanar da rasuwar wanda ya fara shugabantar jama'iyyar a jihar, Solomon Aguele
  • Ya bayyana marigayin mutum wanda za a rika tunawa da shi saboda irn gudunmawar da ya ba da wajen ci gaban PDP da jihar Edo

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Edo - Tsohon shugaban jam’iyyar PDP na farko a jihar Edo, Solomon Aguele, ya koma ga mahaliccinsa.

Marigayi Solomom Aguele ya shugabanci jam’iyyar PDP a jihar Edo daga shekarar 1999 har zuwa 2007.

Tsohon shugaban PDP a Edo ya rasu
Hoton tsohon shugaban PDP a Edo, Solomon Aguele a gidansa Hoto: @Aighodalo
Source: Twitter

Shugaban PDP na farko a Edo ya rasu

Mukaddashin shugaban jam'iyyar PDP na jihar Edo, Anthony Aziegbemi, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar, cewar rahoton jaridar The Punch.

Kara karanta wannan

An yi babban rashi, mahaifiyar shugaban APC na kasa ta rasu bayan jinya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban na PDP ya bayyana marigayi Solomon Aguele, a matsayin mutum wanda ya yi wa jam’iyyar hidima cike da nagarta da kuma jajircewa.

Anthony Aziegbemi ya mika ta’aziyyar jam’iyyar ga iyalansa, abokansa, abokan siyasa da duk masu alhinin rashin nasa, rahoton jaridar The Nation ya tabbatar.

Ya ce za a ci gaba da tunawa da marigayi Solomom Aguele, saboda kankan da kai, amana, da kuma gudummawar da ya bayar ga jam’iyyar PDP da cigaban jihar Edo.

Jam'iyyar PDP ta aika sakon ta'aziyya

"Jam’iyyar PDP, reshen Edo, cikin alhini mai zurfi na sanar da rasuwar shugaban jam’iyyar na farko a jihar, Cif Solomon Aguele, wanda ya yi shugabanci da jajircewa daga 1999 zuwa 2007."
"Cif Solomon Aguele jagora ne mai jajircewa wanda amincinsa, hikimarsa, da jajircewarsa wajen tabbatar da manufofin dimokuraɗiyya suka kafa tubalin da jam’iyyarmu ke tsaye a kai har yau."
"Shugabancinsa a shekarun farko na gina jam’iyyarmu a jihar Edo ya taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa ta da samun nasarorin da ta samu."

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta lallasa PDP a zaben cike gurbi na dan majalisar Jigawa da ya rasu

"Muna mika ta’aziyyarmu ga iyalansa, abokansa, abokan siyasa da duk masu alhinin rashin nasa."
"Za a rika tunawa da Cif Solomon Aguele, saboda kankan da kai, amana, da kuma gudummawar da ba za a manta da ita ba ga PDP da ci gaban jihar Edo."

- Anthony Aziegbemi

Shugaban PDP na farko a Edo ya rasu
Dan takarar gwamnan PDP na Edo, Asue Ighodalo yayin wata ziyara da ya kai gidan Solomon Aguele Hoto: @Aighodalo
Source: Twitter

Karanta karin wasu labaran kan rashe-rashe

Ali Nuhu ya musanta labarin mutuwarsa

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban hukumar fina-finai ta Najeriya (NFC), Ali Nuhu, ya yi martani kan rahotannin da ke cewa ya yi bankwana da duniya.

Ali Nuhu wanda ya ke jarumi, furodusa kuma mai ba da umarni a masana'antar Kannywood, ya musanta cewa lokacinsa ya yi.

Shugaban na hukumar NFC ya bayyana cewa ba abin mamaki ba ne don an yada jita-jita kan rasuwarsa, saboda an saba yin hakan duk shekara.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng