Gwamnatin Najeriya Ta Biya wa Kiristoci Rabin Kudin Kujerarar Ziyara zuwa Isra'ila

Gwamnatin Najeriya Ta Biya wa Kiristoci Rabin Kudin Kujerarar Ziyara zuwa Isra'ila

  • Hukumar NCPC ta ce za a dawo ziyarar Kiristoci zuwa Isra’ila da Jordan daga watan Satumba bayan ɗage takunkumin da aka saka
  • Shugaban hukumar ya ce gwamnatin tarayya ta bayar da rangwamen kashi 50 cikin 100, inda masu ziyara za su biya rabin kuɗin tafiya kacal
  • NCPC ta tabbatar da cewa duk shirin kariya da tsaron lafiya ya riga ya kammala don tabbatar da zuwa da dawowar su lami lafiya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja Hukumar kula da ziyarar ibadar Kiristoci ta kasa (NCPC) ta bayyana cewa daga watan Satumba za a koma gudanar da aikin ziyara zuwa ƙasashen Isra’ila da Jordan.

Wannan ya biyo bayan ɗagewar dakatarwar da aka yi a baya saboda tashin hankali tsakanin Isra’ila da Iran.

Kara karanta wannan

ADC ta cimma matsaya da Atiku, Peter Obi da Amaechi kan batun takara a zaben 2027

Shugaban hukumar alhazan Kiristocin Najeriya, Stephen Adegbite
Shugaban hukumar alhazan Kiristocin Najeriya, Stephen Adegbite. Hoto: Nigerian Christian Pilgrims Commission
Source: Facebook

Punch ta wallafa cewa shugaban NCPC, Stephen Adegbite, ne ya sanar da hakan, inda ya ce gwamnatin tarayya ta amince da bayar da tallafin 50% don rage kuɗin tafiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar NCPC ta ɗage takunkumi

A baya, hukumar ta sanar da cewa ba za a ci gaba da ibadar ziyara Isra’ila ba har sai an samu zaman lafiya da Iran, musamman bayan rikicin da ya tashi ranar 13 ga Yuni, 2025.

Sararin samaniya a lokacin da ake harba makamai a yakin Iran da Isra'ila
Sararin samaniya a lokacin da ake harba makamai a yakin Iran da Isra'ila. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Wannan mataki ya biyo bayan ƙarin rikici da ya tada hankalin duniya gaba ɗaya yayin da aka gwabza fada a Gabas ta Tsakiya.

Sai dai a wani sabon jawabi, Adegbite ya tabbatar da cewa yakin ya lafa, kuma Isra’ila ta koma cikin yanayin kwanciyar hankali.

Ya bayyana cewa shi da wasu ‘yan majalisar wakilai sun je Isra’ila kwanan nan kuma babu wata matsala ta tsaro.

An sa wa Kiristoci tallafin 50%

Fasto Adegbite ya bayyana cewa za a gudanar da tafiyar har tsawon kwanaki 10, kuma duk da tsadar kuɗin tafiya, gwamnati ta riga ta rage rabin kuɗin.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu za ta fara ba iyaye tallafin kudi domin tura 'ya'yansu makaranta

A cewarsa, maniyyata za su biya Naira miliyan 4.5 kacal, yayin da gwamnatin tarayya za ta biya sauran rabin kuɗin.

Ya jaddada cewa wannan tallafi daga gwamnati wani muhimmin mataki ne na sauƙaƙa wa Kiristoci damar gudanar da wannan muhimmin tafiya mai alaka da addini da al’ada.

Shirin tafiyar ziyarar Kiristocin Najeriya

Shugaban hukumar ya ce akwai shirye-shirye na musamman da aka yi don tabbatar da tsaro idan har wani sabon rikici ya tashi a lokacin ibadar ziyarar.

Ya ƙara da cewa tun daga shekarar 1999 babu wani lokaci da aka je Isra’ila ba tare da wani yanayi na tashin hankali ba, amma kullum ana shawo kan lamura lafiya.

Ya kuma bayyana cewa an tsara fara aikin ibadan na bana daga ranar 14 ga Satumba, inda jirgin farko zai tashi daga jihar Imo.

Rahoton Muslim News ya nuna cewa ya ce shi da wasu ‘yan majalisar wakilai kusan 100 za su fara tafiya a kafin a fara babban aikin bautar.

Mahajjatan Musulmi za su biya N8.5m

Kara karanta wannan

Zaben 2027: INEC ta fara rajistar masu kada kuri'a a jihohi 36 da Abuja

A wani rahoton, kun ji cewa hukumar alhazai ta NAHCON ta fara shirye shiryen gudanar da aikin hajji na 2026.

Hakan na zuwa ne bayan shugaban hukumar, Farfesa Sale Usman ya tabbatar da cewa sun samu nasarar kammala hajjin 2025 lafiya.

Rahotannin da Legit Hausa ta samu sun nuna cewa NAHCON ta bukaci mahajjata Musulmi su tanadi kudin ajiya har N8.5m.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng