Akpabio Ya Bayyana ana Rade Radin Shugaban Majalisa Yana Kwance a Asibitin Landan

Akpabio Ya Bayyana ana Rade Radin Shugaban Majalisa Yana Kwance a Asibitin Landan

  • Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya dawo Najeriya daga hutu a Landan da ofishinsa ya bayyana a matsayin gajere
  • Isowarsa a filin jirgin saman Abuja ta kawo ƙarshen jita-jitar cewa yana kwance a asibitin Landan cikin rashin lafiya mai tsanani
  • Godswill Akpabio ya ce majalisar dattawa ta kasa za ta cigaba da ayyuka cikin ƙwazo tare da ƙarfafa dimokuraɗiyya a Najeriya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Godswill Akpabio, ya dawo ƙasar bayan hutun da ya yi a birnin Landan.

Rahotanni sun nuna cewa Akpabio ya sauka da sassafe a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe na birnin Abuja a safiyar Litinin.

Sanata Akpabio na magana da 'yan jarida bayan dawowa Najeriya daga London
Sanata Akpabio na magana da 'yan jarida bayan dawowa Najeriya daga London. Hoto: Anambra APC
Source: Facebook

Premium Times ta ce ofishinsa ya bayyana dawowarsa a matsayin ƙarshen jita-jitar da ta rika cewa shugaban majalisar ya kwanta a asibitin Landan sakamakon rashin lafiya mai tsanani.

Kara karanta wannan

Jerin manyan kujerun gwamnatin tarayya da Tinubu ya ba mutanen Kano a shekaru 2

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan lamari ya faru ne bayan gama taron shugabannin majalisun dokoki na duniya karo na shida da aka gudanar a Geneva daga 29 zuwa 31 ga watan Yuli.

Jita-jitar rashin lafiyar Godswill Akpabio

Rashin ganin shugaban majalisar dattawan a fili bayan kammala taron Geneva ne ya janyo jita-jita a kafafen sada zumunta cewa yana fama da rashin lafiya a Landan.

Sai dai isowarsa da safiyar Litinin ya zama hujja ta karyata rahotannin, lamarin da ya kawo sauƙi ga mambobin majalisar, magoya bayansa da kuma ’yan Najeriya da dama.

The Cable ta rahoto cewa ofishin yada labaran Akpabio ya ce:

“Dawowar shugaban majalisar ya karyata zancen cewa yana cikin mawuyacin hali a asibitin Landan.”

Yadda Akpabio ya isa Abuja da asuba

Akpabio ya iso da misalin ƙarfe 4:00 na asuba a filin jirgin saman Abuja, inda aka tarbe shi a ɓangaren shugabanni na filin jirgin saman.

’Yan majalisar dattawa, masu taimaka masa da magoya baya sun tarbe shi da farin ciki tare da nuna goyon baya a gare shi.

Kara karanta wannan

Tinubu ya sakawa kanwar Abdussamad BUA, ya ba ta mukami a gwamnatinsa

Bayan isowarsa, ya yi wa manema labarai jawabi inda ya jaddada aniyar majalisar dattawa na yin “ayyukan doka cikin ƙwazo” a lokacin da majalisar za ta koma aiki.

Sanata Akpabio yayin wani zaman majalisa a Abuja
Sanata Akpabio yayin wani zaman majalisa a Abuja. Hoto: Nigerian Senate
Source: Facebook

Martanin Akpabio kan rashin lafiya

Akpabio ya bayyana rahotannin da ke cewa yana cikin rashin lafiya a Landan a matsayin “ƙirƙirarrun labarai daga masu yayata jita-jita”.

Ya ce ba gaskiya ba ne cewa ya kwanta a asibiti, domin tafiyarsa ta kasance hutu ne na gajeren lokaci bayan taron kasa da kasa da ya halarta.

Ya kuma yaba wa mambobin tawagar Najeriya a taron Geneva, inda ya ce sun taka muhimmiyar rawa wajen ƙarfafa dimokuraɗiyya da haɓaka haɗin kai tsakanin rassan gwamnati.

Akpabio ya yi subutar baki a majalisa

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya yi subutar baki a zauren majalisa.

Akpabio ya yi magana ne yayin da ya ke zance a kan marigayi shugaba Muhammadu Buhari amma ya ambaci Bola Ahmed Tinubu.

Binciken Legit Hausa ya gano cewa lamarin ya janyo hankalin 'yan Najeriya da dama, musamman a kafafen sada zumunta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng