Jirgin Ruwa Ya Kife da 'Yan Kasuwa a Sokoto, an Samu Asarar Rayuka
- An samu asarar rayuka bayan wani jirgin ruwa dauke da 'yan kasuwa ya gamu da hatsari a yankin jihar Sokoto
- Hatsarin jirgin ruwan ya jawo sanadiyyar rasuwar mutane akalla 30 wadanda ke kan hanyar zuwa kasuwar Goronyo
- Shugaban karamar hukumar Goronyo wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya bayyana cewa an samu nasarar ceto wasu mutane da ransu
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Sokoto - Aƙalla ‘yan kasuwa 30, ciki har da mata, ake zargin sun rasu sakamakon mummunan hatsarin jirgin ruwa da ya faru a jihar Sokoto.
Hatsarin jirgin ruwan dai ya auku ne a ranar Lahadi, 18 ga watan Agustan 2025 a kauyen Kojiyo, karamar hukumar Goronyo ta jihar Sokoto.

Source: Original
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa waɗanda abin ya rutsa da su na kan hanyarsu ce ta zuwa kasuwar mako-mako ta Goronyo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jirgin ruwa ya yi hatsari a Sokoto
Jirgin ruwan da ke ɗauke da 'yan kasuwan tare da kayayyakinsu ya kife ne da misalin karfe 1:30 na rana.
Shaidun gani da ido sun ce an dora kaya fiye da kima a jirgin, domin maimakon mutane da kaya kaɗai, har da babura aka ɗora a kansa, rahoton The Punch ya tabbatar.
Majiyoyi daga yankin sun ce ‘yan kasuwar sun fito ne daga ƙauyuka daban-daban na karamar hukumar Goronyo da maƙwabciyarta Gada.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, shugaban ƙaramar hukumar Goronyo, Hon. Zubairu Yari, ya bayyana cewa an ceto mutane huɗu da ransu.
Ya ce ba a tabbatar da adadin fasinjojin da ke cikin jirgin ba, amma babu shakka an cika shi fiye da abin da zai iya dauka.
'Yan kasuwa sun rasu a kauyen Sokoto
Ya bayyana cewa ‘yan kasuwan sun fito daga ƙauyuka da dama, ciki har da na karamar hukumar Gada, domin halartar kasuwar ta ranar Lahadi.

Source: Getty Images
Ya ƙara da cewa sun sanar da mazauna kauyuka makwabta domin taimakawa wajen nemo gawarwakin waɗanda abin ya rutsa da su, yana mai fatan za a iya gano wasu daga cikin su yau.
Shugaban ƙaramar hukumar ya danganta lamarin da daukar kaya fiye da kima, da kuma rashin ingantattun hanyoyin mota, wanda ke tilasta jama’a dogaro da hanyoyin ruwa.
Sai dai kuma ya bayyana cewa gwamnatin jiha na gudanar da aikin gina hanyoyi da gadoji domin saukaka zirga-zirga a yankin.
Karanta wasu labaran kan hatsarin jirgi
- Allah Sarki: Hankula sun tashi da yara 8 suka mutu a hadari bayan nutsewa a kogi
- Ruwa da iska mai ƙarfi sun kifar da jirgi bayan ya ɗauko fasinjoji a jihar Jigawa
- Jirgin ruwa ya yi mummunan hatsari a Taraba, an samu asarar rayuka
Jirgin ruwa ya yi hatsari a Jigawa
A wani labarin kuma, kun ji cewa wani jirgin ruwa na kwale-kwale ya gamu da hatsari a jihar Jigawa.
Hatsarin jirgin kwale-kwalen ya yi sanadiyyar rasuwar akalla mutane shida bayan ya kife lokacin da ake cikin tafiya.
Kwale-kwalen dai yana dauke da wasu yara ne wadanda suka dawo daga gonar jejin Gunka zuwa kauyensu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


