Sauki Ya Zo: Tinubu Ya Sake Tausayawa Al'umma, Zai Fara Raba Kuɗi ga Yan Najeriya
- Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa kafin ƙarshen 2025 za a fara raba rancen ba tare da riba ba ga manoma da ‘yan kasuwa
- Shugaban shirin GEEP na ƙasa, Hamza Ibrahim Baba, ne ya bayyana hakan a jihar Kaduna da ke Arewacin Najeriya
- Hamza ya ce shirin GEEP zai baiwa masu sana’o’i da manoma damar samun N5,000 zuwa N100,000
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kaduna - Gwamnatin Tarayya ta sake shirya taimakawa manoma da kuma ƙananan yan kasuwa a fadin Najeriya.
An dauki wannan mataki ne domin farfaɗo da tattalin arziki duba da yadda al'umma ke kokawa a halin yanzu.

Source: UGC
Gwamnatin Tinubu ta shirya taimakawa manoma
Gwamnatin za ta fara raba rancen ba tare da riba ba ga manoma ƙanana da ‘yan kasuwa a fadin ƙasar nan kafin ƙarshen shekarar 2025, cewar The Guardian.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban shirin GEEP na ƙasa, Hamza Ibrahim Baba, ne ya bayyana hakan a Kaduna inda ya ce za a taallafa wa manoma da ke aikin noma da kiwo
Ya ce:
“Wannan matakin farko zai tallafa wa manoma a fadin ƙasa, da ‘yan kasuwa ƙanana, ciki har da jihar Kaduna."
Ya kara da cewa, za a baiwa masu cin gajiyar rancen wa’adin watanni shida kafin su fara biyan bashi, domin su samu damar yin aiki lafiya.
Baba ya bayyana cewa shirin na GEEP yana da rukuni uku; TraderMoni ga matasa ‘yan kasuwa, MarketMoni ga mata, da FarmerMoni ga manoma karkara.
Ya jaddada da cewa:
“Waɗannan ba tallafi ba ne, rance ne, amma ba tare da riba ba, domin tallafa wa ‘yan Najeriya su bunƙasa da ƙirƙirar ayyuka.”

Source: Facebook
Yadda gwamnatin Tinubu za ta raba rance
Baba ce rancen yana daga tsakanin N5,000 zuwa N100,000 dangane da shirin da mutum ya shiga, tare da tsarin duba nagartar masu cin gajiyar, Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Tinubu ta bude sabon shiri, za a hada matasa da masu daukar aiki a duniya
Ya yi kira ga ƙungiyoyin ‘yan kasuwa da kungiyoyin haɗin gwiwa su yi aiki da jami’an GEEP a fadin kananan hukumomi 774 na ƙasar nan.
Har ila yau, ya ce nasarar shirin na bukatar gaskiya da tsantseni wajen zaɓar wadanda suka cancanta, ba masu neman amfani da damar shirin ba bisa ka’ida ba.
Baba ya tabbatar da cewa gwamnatin Tinubu na da niyyar faɗaɗa shirin, inda wannan matakin zai zama tushe ga aiwatar da babban shiri a 2026.
Legit ta yi magana da wasu matasa
A tattaunawar, Hauwa Musa ta gode wa gwamnati bisa wannan tallafi, inda ta bayyana cewa ya taimaka mata sosai wajen fadada kasuwancinta.
Wani dan kasuwa, Umar Usman, ya ce bai samu rancen ba tukuna, amma yana da fatan shiga cikin shirin GEEP 3.0 da ke zuwa nan gaba.
Hauhawan farashin kaya ya sauka a Najeriya
Kun ji cewa Hukumar kididdiga ta NBS ta fitar sabuwar sabarwa kan hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya.
Hukumar ta ce farashin kayayyakin ya ragu zuwa kashi 21.88 a watan Yulin 2025, daga 22.22% a watan Yuni.
Rahoton ya nuna wannan shi ne karo na hudu a bana da aka samu raguwar hauhawar farashi, duk da ƙaruwa tsakanin wata da wata.
Asali: Legit.ng
